Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 37

فَتَلَقَّىٰٓ ءَادَمُ مِن رَّبِّهِۦ كَلِمَٰتٖ فَتَابَ عَلَيۡهِۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلتَّوَّابُ ٱلرَّحِيمُ

Sai Adamu ya karvi wasu kalmomi daga Ubangijinsa (na neman gafara), sai Ya yafe masa; lalle Shi ne Mai yawan karvar tuba kuma Mai yawan jin qai



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 52

ثُمَّ عَفَوۡنَا عَنكُم مِّنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَ لَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ

Sannan sai Muka yi muku afuwa bayan haka, don ku yi godiya



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 54

وَإِذۡ قَالَ مُوسَىٰ لِقَوۡمِهِۦ يَٰقَوۡمِ إِنَّكُمۡ ظَلَمۡتُمۡ أَنفُسَكُم بِٱتِّخَاذِكُمُ ٱلۡعِجۡلَ فَتُوبُوٓاْ إِلَىٰ بَارِئِكُمۡ فَٱقۡتُلُوٓاْ أَنفُسَكُمۡ ذَٰلِكُمۡ خَيۡرٞ لَّكُمۡ عِندَ بَارِئِكُمۡ فَتَابَ عَلَيۡكُمۡۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلتَّوَّابُ ٱلرَّحِيمُ

Kuma ku tuna lokacin da Musa ya cewa mutanensa: “Ya ku mutanena, lalle ku kun zalunci kawunanku ta hanyar mayar da xan maraqi abin bauta, don haka ku tuba zuwa ga Mahaliccinku, kuma ku kashe kawunanku; wannan shi ne ya fi alheri a gare ku a wajen Mahaliccinku. Lalle shi Mai yawan karvar tuba ne, Mai yawan jin qai.”



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 160

إِلَّا ٱلَّذِينَ تَابُواْ وَأَصۡلَحُواْ وَبَيَّنُواْ فَأُوْلَـٰٓئِكَ أَتُوبُ عَلَيۡهِمۡ وَأَنَا ٱلتَّوَّابُ ٱلرَّحِيمُ

Sai dai waxanda suka tuba kuma suka gyara kuma suka bayyana, to waxannan zan karvi tubansu, kuma lalle Ni Mai karvar tuba ne, Mai jin qai



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 173

إِنَّمَا حَرَّمَ عَلَيۡكُمُ ٱلۡمَيۡتَةَ وَٱلدَّمَ وَلَحۡمَ ٱلۡخِنزِيرِ وَمَآ أُهِلَّ بِهِۦ لِغَيۡرِ ٱللَّهِۖ فَمَنِ ٱضۡطُرَّ غَيۡرَ بَاغٖ وَلَا عَادٖ فَلَآ إِثۡمَ عَلَيۡهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٌ

(Allah) Ya haramta muku mushe ne kawai da jini da naman alade da abin da aka kira sunan wani ba Allah ba (lokacin yanka shi). Don haka duk wanda ya matsu, ba mai zalunci ba, kuma ba mai qetare iyaka ba, to babu laifi a kansa ya ci. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 225

لَّا يُؤَاخِذُكُمُ ٱللَّهُ بِٱللَّغۡوِ فِيٓ أَيۡمَٰنِكُمۡ وَلَٰكِن يُؤَاخِذُكُم بِمَا كَسَبَتۡ قُلُوبُكُمۡۗ وَٱللَّهُ غَفُورٌ حَلِيمٞ

Allah ba zai kama ku da yasasshen zance a cikin rantse-rantsenku ba, sai dai zai kama ku da abin da zukatanku suka qudurce. Kuma Allah Mai yawan gafara ne, Mai yawan haquri



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 235

وَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ فِيمَا عَرَّضۡتُم بِهِۦ مِنۡ خِطۡبَةِ ٱلنِّسَآءِ أَوۡ أَكۡنَنتُمۡ فِيٓ أَنفُسِكُمۡۚ عَلِمَ ٱللَّهُ أَنَّكُمۡ سَتَذۡكُرُونَهُنَّ وَلَٰكِن لَّا تُوَاعِدُوهُنَّ سِرًّا إِلَّآ أَن تَقُولُواْ قَوۡلٗا مَّعۡرُوفٗاۚ وَلَا تَعۡزِمُواْ عُقۡدَةَ ٱلنِّكَاحِ حَتَّىٰ يَبۡلُغَ ٱلۡكِتَٰبُ أَجَلَهُۥۚ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا فِيٓ أَنفُسِكُمۡ فَٱحۡذَرُوهُۚ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ حَلِيمٞ

Kuma babu laifi a kanku game da abin da kuka yi wa mata jirwaye da shi na neman aurensu ko kuma kuka voye a cikin zukatanku, Allah Ya san cewa ku za ku riqa maganarsu, sai dai kar ku yi alqawari da su (na aure) a asirce, sai dai in za ku faxi zance wanda yake sananne a (shari’a). Kuma kada ku qulla igiyar aure (da mata masu takaba) har sai faralin idda ya cika wa’adinsa. Kuma ku sani lalle Allah Ya san abin da yake cikin zukatanku, don haka ku kiyaye Shi. Kuma ku sani lalle Allah Mai yawan gafara ne, Mai haquri



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 284

لِّلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ وَإِن تُبۡدُواْ مَا فِيٓ أَنفُسِكُمۡ أَوۡ تُخۡفُوهُ يُحَاسِبۡكُم بِهِ ٱللَّهُۖ فَيَغۡفِرُ لِمَن يَشَآءُ وَيُعَذِّبُ مَن يَشَآءُۗ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ

Duk abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qasa na Allah ne. Kuma in har kuka bayyana abin da yake cikin zukatanku ko kuka voye shi, Allah zai yi muku hisabi a kansa, sai Ya yi gafara ga wanda Ya ga dama, Ya kuma yi azaba ga wanda Ya ga dama. Kuma Allah Mai iko ne a kan komai



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 31

قُلۡ إِن كُنتُمۡ تُحِبُّونَ ٱللَّهَ فَٱتَّبِعُونِي يُحۡبِبۡكُمُ ٱللَّهُ وَيَغۡفِرۡ لَكُمۡ ذُنُوبَكُمۡۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Ka ce: “In kun kasance kuna son Allah, to ku yi mini biyayya, sai Allah Ya so ku, kuma Ya gafarta muku zunubanku. Kuma Allah Mai gafara ne, Mai jin qai.”



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 129

وَلِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۚ يَغۡفِرُ لِمَن يَشَآءُ وَيُعَذِّبُ مَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Kuma abin da yake cikin sammai da kuma abin da yake cikin qasa na Allah ne. Yana yin gafara ga wanda Ya ga dama, Yana kuma yin azaba ga wanda Ya ga dama. Kuma Allah Mai gafara ne, Mai jin qai



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 135

وَٱلَّذِينَ إِذَا فَعَلُواْ فَٰحِشَةً أَوۡ ظَلَمُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ ذَكَرُواْ ٱللَّهَ فَٱسۡتَغۡفَرُواْ لِذُنُوبِهِمۡ وَمَن يَغۡفِرُ ٱلذُّنُوبَ إِلَّا ٱللَّهُ وَلَمۡ يُصِرُّواْ عَلَىٰ مَا فَعَلُواْ وَهُمۡ يَعۡلَمُونَ

(Su ne) kuma waxanda idan sun aikata mummunan aiki, ko suka zalunci kansu, nan take sai su tuna da Allah, sai su nemi gafarar zunubansu. Wane ne kuwa mai gafarta zunubbai in ba Allah ba? Kuma ba sa zarcewa a kan abin da suka yi, alhali suna sane



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 155

إِنَّ ٱلَّذِينَ تَوَلَّوۡاْ مِنكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡتَقَى ٱلۡجَمۡعَانِ إِنَّمَا ٱسۡتَزَلَّهُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ بِبَعۡضِ مَا كَسَبُواْۖ وَلَقَدۡ عَفَا ٱللَّهُ عَنۡهُمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ حَلِيمٞ

Lalle waxanda suka gudu daga cikinku yayin da runduna biyu suka haxu, Shaixan ne ya nemi ya zamar da su saboda wani laifi da suka yi; kuma tabbas haqiqa Allah Ya yi musu afuwa. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai haquri



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 17

إِنَّمَا ٱلتَّوۡبَةُ عَلَى ٱللَّهِ لِلَّذِينَ يَعۡمَلُونَ ٱلسُّوٓءَ بِجَهَٰلَةٖ ثُمَّ يَتُوبُونَ مِن قَرِيبٖ فَأُوْلَـٰٓئِكَ يَتُوبُ ٱللَّهُ عَلَيۡهِمۡۗ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمٗا

Tuban da Allah Yake karva kawai (ita ce) na waxanda suke aikata mummunan aiki da jahilci, sannan su gaggauta tuba, to waxannan Allah zai karvi tubansu. Allah kuma Ya kasance Mai yawan sani ne, Mai hikima



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 26

يُرِيدُ ٱللَّهُ لِيُبَيِّنَ لَكُمۡ وَيَهۡدِيَكُمۡ سُنَنَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكُمۡ وَيَتُوبَ عَلَيۡكُمۡۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٞ

Allah Yana nufin yi muku bayani ne, kuma Ya shiryar da ku hanyoyin waxanda suka gabace ku, kuma Ya karvi tubanku. Kuma Allah Mai yawan sani ne, Mai hikima



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 27

وَٱللَّهُ يُرِيدُ أَن يَتُوبَ عَلَيۡكُمۡ وَيُرِيدُ ٱلَّذِينَ يَتَّبِعُونَ ٱلشَّهَوَٰتِ أَن تَمِيلُواْ مَيۡلًا عَظِيمٗا

Kuma Allah Yana nufin Ya karvi tubanku ne, amma waxanda suke bin sha’awace-sha’awace, su kuma suna nufin ku karkace karkacewa mai girma



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 48

إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَغۡفِرُ أَن يُشۡرَكَ بِهِۦ وَيَغۡفِرُ مَا دُونَ ذَٰلِكَ لِمَن يَشَآءُۚ وَمَن يُشۡرِكۡ بِٱللَّهِ فَقَدِ ٱفۡتَرَىٰٓ إِثۡمًا عَظِيمًا

Lalle Allah ba Ya gafarta a yi shirka da Shi, amma Yana gafarta abin da bai kai shirka ba ga wanda Ya ga dama. Kuma duk wanda ya yi shirka da Allah, to haqiqa ya qirqiri wani gagarumin laifi



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 96

دَرَجَٰتٖ مِّنۡهُ وَمَغۡفِرَةٗ وَرَحۡمَةٗۚ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمًا

Wasu darajoji masu yawa daga gare Shi da gafara da kuma jin qai. Kuma Allah Ya kasance Mai yawan gafara ne, Mai yawan jin qai



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 99

فَأُوْلَـٰٓئِكَ عَسَى ٱللَّهُ أَن يَعۡفُوَ عَنۡهُمۡۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَفُوًّا غَفُورٗا

To waxannan mai yiwuwa ne Allah Ya yi musu afuwa, Allah kuma Ya kasance Mai afuwa ne, Mai yawan gafara



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 110

وَمَن يَعۡمَلۡ سُوٓءًا أَوۡ يَظۡلِمۡ نَفۡسَهُۥ ثُمَّ يَسۡتَغۡفِرِ ٱللَّهَ يَجِدِ ٱللَّهَ غَفُورٗا رَّحِيمٗا

Kuma duk wanda ya aikata mummunan aiki ko ya zalunci kansa, sannan ya nemi gafarar Allah, to zai sami Allah Mai yawan gafara ne, Mai yawan jin qai



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 116

إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَغۡفِرُ أَن يُشۡرَكَ بِهِۦ وَيَغۡفِرُ مَا دُونَ ذَٰلِكَ لِمَن يَشَآءُۚ وَمَن يُشۡرِكۡ بِٱللَّهِ فَقَدۡ ضَلَّ ضَلَٰلَۢا بَعِيدًا

Lalle Allah ba Ya gafartawa a yi masa shirka, Yana kuwa gafarta abin da bai kai shirka ba ga wanda Ya ga dama. Duk wanda ya yi wa Allah shirka, to haqiqa ya vata manisanciyar vata



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 129

وَلَن تَسۡتَطِيعُوٓاْ أَن تَعۡدِلُواْ بَيۡنَ ٱلنِّسَآءِ وَلَوۡ حَرَصۡتُمۡۖ فَلَا تَمِيلُواْ كُلَّ ٱلۡمَيۡلِ فَتَذَرُوهَا كَٱلۡمُعَلَّقَةِۚ وَإِن تُصۡلِحُواْ وَتَتَّقُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ كَانَ غَفُورٗا رَّحِيمٗا

Kuma ba za ku iya yin adalci (na soyayya) a tsakankanin mata ba, ko da kuna matuqar son yin hakan. To kada ku karkata, karkata ta gaba xaya, ta yadda za ku qyale xayar kamar ratayayya[1]. Amma idan za ku kyautata kuma ku yi taqawa, to lalle Allah Ya kasance Mai yawan gafara ne, Mai yawan jin qai


1- Watau su karkata ga xaya su qyale xayar a rataye, ita ba a sake ta ba ita kuma ba mai jin daxin aure ba.


Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 9

وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ لَهُم مَّغۡفِرَةٞ وَأَجۡرٌ عَظِيمٞ

Allah Ya yi alqawari ga waxanda suka yi imani, kuma suka yi aiki nagari, suna da gafara da kuma lada mai girma



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 18

وَقَالَتِ ٱلۡيَهُودُ وَٱلنَّصَٰرَىٰ نَحۡنُ أَبۡنَـٰٓؤُاْ ٱللَّهِ وَأَحِبَّـٰٓؤُهُۥۚ قُلۡ فَلِمَ يُعَذِّبُكُم بِذُنُوبِكُمۖ بَلۡ أَنتُم بَشَرٞ مِّمَّنۡ خَلَقَۚ يَغۡفِرُ لِمَن يَشَآءُ وَيُعَذِّبُ مَن يَشَآءُۚ وَلِلَّهِ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَاۖ وَإِلَيۡهِ ٱلۡمَصِيرُ

Kuma Yahudawa da Nasara suka ce: “Mu ‘ya’yan Allah ne, kuma masoyansa.” Ka ce: “To don me Yake muku azaba a sanadiyyar zunubanku? Ba haka ne ba, ku mutane ne daga cikin waxanda Ya halitta. Yana yin gafara ga wanda Ya ga dama, kuma Yana yin azaba ga wanda Ya ga dama. Kuma mulkin sammai da qasa da abin da yake tsakaninsu na Allah ne, kuma zuwa gare Shi ne makoma take.”



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 34

إِلَّا ٱلَّذِينَ تَابُواْ مِن قَبۡلِ أَن تَقۡدِرُواْ عَلَيۡهِمۡۖ فَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Sai dai waxanda suka tuba tun kafin ku sami damar kama su; to ku sani cewa, lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 39

فَمَن تَابَ مِنۢ بَعۡدِ ظُلۡمِهِۦ وَأَصۡلَحَ فَإِنَّ ٱللَّهَ يَتُوبُ عَلَيۡهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٌ

To (amma) wanda ya tuba bayan zaluncinsa, kuma ya gyara aikinsa, to lalle Allah zai karvi tubansa. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 40

أَلَمۡ تَعۡلَمۡ أَنَّ ٱللَّهَ لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ يُعَذِّبُ مَن يَشَآءُ وَيَغۡفِرُ لِمَن يَشَآءُۗ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Shin ba ka da masaniyar cewa, lalle Allah Shi ne Yake mallakar abin da yake cikin sammai da kuma qasa, Yana yin azaba ga wanda Ya ga dama, kuma Yana gafarta wa wanda Ya ga dama. Kuma Allah Mai iko ne a kan komai?



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 74

أَفَلَا يَتُوبُونَ إِلَى ٱللَّهِ وَيَسۡتَغۡفِرُونَهُۥۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Shin yanzu ba za su tuba zuwa ga Allah ba, kuma su nemi gafararsa? Allah kuwa Mai gafara ne, Mai jin qai



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 95

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَقۡتُلُواْ ٱلصَّيۡدَ وَأَنتُمۡ حُرُمٞۚ وَمَن قَتَلَهُۥ مِنكُم مُّتَعَمِّدٗا فَجَزَآءٞ مِّثۡلُ مَا قَتَلَ مِنَ ٱلنَّعَمِ يَحۡكُمُ بِهِۦ ذَوَا عَدۡلٖ مِّنكُمۡ هَدۡيَۢا بَٰلِغَ ٱلۡكَعۡبَةِ أَوۡ كَفَّـٰرَةٞ طَعَامُ مَسَٰكِينَ أَوۡ عَدۡلُ ذَٰلِكَ صِيَامٗا لِّيَذُوقَ وَبَالَ أَمۡرِهِۦۗ عَفَا ٱللَّهُ عَمَّا سَلَفَۚ وَمَنۡ عَادَ فَيَنتَقِمُ ٱللَّهُ مِنۡهُۚ وَٱللَّهُ عَزِيزٞ ذُو ٱنتِقَامٍ

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku kashe abin farauta alhali kuna cikin Harami[1]. Duk kuwa wanda ya kashe shi daga cikinku da gangan, to sakamakonsa shi ne (ya bayar) da kwatankwacin abin da ya kashe cikin dabbobin gida; waxanda za su yi hukunci da wannan su ne mutum biyu adalai a cikinku, a matsayin hadaya wadda za ta isa Ka’aba, ko kuma ya yi kaffarar ciyar da miskinai, ko kuma ya yi azumi na kwatankwacin haka, don ya xanxani kuxar lamarinsa. Allah Ya yi afuwa dangane da abin da ya wuce. Duk kuwa wanda ya sake komawa, to Allah zai yi masa uquba. Kuma Allah Mabuwayi ne, Ma’abocin uquba


1- Watau kuna sanye da haramin hajji ko na umara.


Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 98

ٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ وَأَنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Ku sani lalle Allah Mai tsananin uquba ne, kuma lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 101

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَسۡـَٔلُواْ عَنۡ أَشۡيَآءَ إِن تُبۡدَ لَكُمۡ تَسُؤۡكُمۡ وَإِن تَسۡـَٔلُواْ عَنۡهَا حِينَ يُنَزَّلُ ٱلۡقُرۡءَانُ تُبۡدَ لَكُمۡ عَفَا ٱللَّهُ عَنۡهَاۗ وَٱللَّهُ غَفُورٌ حَلِيمٞ

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku yi tambaya game da waxansu al’amurra, waxanda idan aka bayyana muku su za su dame ku, idan kuwa kuka riqa tambaya game da su yayin da Alqur’ani yake sauka, za a bayyana muku su; Allah Ya yi rangwame game da su. Kuma Allah Mai gafara ne, Mai haquri