Capítulo: Suratul Fatiha

Verso : 6

ٱهۡدِنَا ٱلصِّرَٰطَ ٱلۡمُسۡتَقِيمَ

Ka shiryar da mu tafarkin nan madaidaici



Capítulo: Suratul Fatiha

Verso : 7

صِرَٰطَ ٱلَّذِينَ أَنۡعَمۡتَ عَلَيۡهِمۡ غَيۡرِ ٱلۡمَغۡضُوبِ عَلَيۡهِمۡ وَلَا ٱلضَّآلِّينَ

Tafarkin waxanda Ka yi wa ni’ima[1], ba waxanda aka yi fushi da su ba[2], ba kuma vatattu ba[3]


1- Su ne waxanda aka ambata a aya ta 69 a Suratun Nisa’i.


2- Watau waxanda suka san gaskiya suka take, kamar Yahudawa.


3- Watau waxanda suke bautar Allah da jahilci, kamar Nasara.


Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 112

بَلَىٰۚ مَنۡ أَسۡلَمَ وَجۡهَهُۥ لِلَّهِ وَهُوَ مُحۡسِنٞ فَلَهُۥٓ أَجۡرُهُۥ عِندَ رَبِّهِۦ وَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ

E! Wanda ya miqa fuskarsa ga Allah alhali yana mai kyautata aikinsa, to yana da ladansa a wajen Ubangijinsa, kuma babu tsoro a tare da su kuma ba za su yi baqin ciki ba



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 131

إِذۡ قَالَ لَهُۥ رَبُّهُۥٓ أَسۡلِمۡۖ قَالَ أَسۡلَمۡتُ لِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Ka tuna lokacin da Ubangijijinsa Ya ce masa: “Ka miqa wuya”, sai ya ce: “Na miqa wuya ga Ubangijin talikai.”



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 132

وَوَصَّىٰ بِهَآ إِبۡرَٰهِـۧمُ بَنِيهِ وَيَعۡقُوبُ يَٰبَنِيَّ إِنَّ ٱللَّهَ ٱصۡطَفَىٰ لَكُمُ ٱلدِّينَ فَلَا تَمُوتُنَّ إِلَّا وَأَنتُم مُّسۡلِمُونَ

Kuma Ibrahimu da Ya’aqubu suka yi wasiyya da wannan ga ‘ya’yansu cewa: “Ya ‘ya’yana, lalle Allah Ya zava muku addini, don haka kada ku mutu face kuna Musulmi.”



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 135

وَقَالُواْ كُونُواْ هُودًا أَوۡ نَصَٰرَىٰ تَهۡتَدُواْۗ قُلۡ بَلۡ مِلَّةَ إِبۡرَٰهِـۧمَ حَنِيفٗاۖ وَمَا كَانَ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ

Kuma suka ce: “Ku zama Yahudawa ko Nasara za ku shiriya”. Ka ce: “A’a! (Za mu bi) addinin Ibrahimu ne wanda yake miqe totar, kuma bai zamo daga cikin masu shirka ba.”



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 146

ٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ يَعۡرِفُونَهُۥ كَمَا يَعۡرِفُونَ أَبۡنَآءَهُمۡۖ وَإِنَّ فَرِيقٗا مِّنۡهُمۡ لَيَكۡتُمُونَ ٱلۡحَقَّ وَهُمۡ يَعۡلَمُونَ

Waxanda Muka ba su Littafi suna sane da shi (Manzon Allah) kamar yadda suke sane da ‘ya’yansu; kuma lalle wani vangare daga cikinsu tabbas suna voye gaskiya alhalin suna sane



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 208

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱدۡخُلُواْ فِي ٱلسِّلۡمِ كَآفَّةٗ وَلَا تَتَّبِعُواْ خُطُوَٰتِ ٱلشَّيۡطَٰنِۚ إِنَّهُۥ لَكُمۡ عَدُوّٞ مُّبِينٞ

Ya ku waxanda suka yi imani, ku shiga cikin addinin Musulunci gaba xaya, kuma kar ku bi hanyoyin Shaixan. Lalle shi maqiyi ne a gare ku, mai bayyana (qiyayya)



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 19

إِنَّ ٱلدِّينَ عِندَ ٱللَّهِ ٱلۡإِسۡلَٰمُۗ وَمَا ٱخۡتَلَفَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ إِلَّا مِنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَهُمُ ٱلۡعِلۡمُ بَغۡيَۢا بَيۡنَهُمۡۗ وَمَن يَكۡفُرۡ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ فَإِنَّ ٱللَّهَ سَرِيعُ ٱلۡحِسَابِ

Lalle addini a wurin Allah shi ne Musulunci. Kuma waxanda aka ba wa Littafi ba su yi savani ba sai bayan da ilimi ya zo musu saboda zalunci a tsakaninsu. Wanda kuwa duk ya kafirce wa ayoyin Allah, to lalle Allah Mai gaggawar hisabi ne



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 20

فَإِنۡ حَآجُّوكَ فَقُلۡ أَسۡلَمۡتُ وَجۡهِيَ لِلَّهِ وَمَنِ ٱتَّبَعَنِۗ وَقُل لِّلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡأُمِّيِّـۧنَ ءَأَسۡلَمۡتُمۡۚ فَإِنۡ أَسۡلَمُواْ فَقَدِ ٱهۡتَدَواْۖ وَّإِن تَوَلَّوۡاْ فَإِنَّمَا عَلَيۡكَ ٱلۡبَلَٰغُۗ وَٱللَّهُ بَصِيرُۢ بِٱلۡعِبَادِ

To idan sun yi jayayya da kai, sai ka ce: “Ni na miqa wuyana ne ga Allah, haka ma wanda ya bi ni.” Kuma ka faxa wa waxanda aka bai wa Littafi da Ummiyyai (Larabawa): “Shin kun miqa wuya?” To idan sun miqa wuya, haqiqa sun shiryu; idan kuwa suka juya baya, to babu abin da yake a kanka sai isar da saqo. Kuma Allah Mai ganin bayinsa ne



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 51

إِنَّ ٱللَّهَ رَبِّي وَرَبُّكُمۡ فَٱعۡبُدُوهُۚ هَٰذَا صِرَٰطٞ مُّسۡتَقِيمٞ

“Lalle Allah Shi ne Ubangijina kuma Ubangijinku, don haka ku bautata masa Shi kaxai. Wannan shi ne tafarki madaidaici.”



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 67

مَا كَانَ إِبۡرَٰهِيمُ يَهُودِيّٗا وَلَا نَصۡرَانِيّٗا وَلَٰكِن كَانَ حَنِيفٗا مُّسۡلِمٗا وَمَا كَانَ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ

Ibrahimu bai tava zama Bayahude ba, sannan bai tava zama Banasare ba, sai dai ya kasance mai barin varna ne, Musulmi, kuma bai kasance xaya daga cikin mushirikai ba



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 85

وَمَن يَبۡتَغِ غَيۡرَ ٱلۡإِسۡلَٰمِ دِينٗا فَلَن يُقۡبَلَ مِنۡهُ وَهُوَ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ

Duk kuma wanda ya nemi (bin) wani addini ba Musulunci ba, to har abada ba za a karva daga gare shi ba, kuma shi a lahira yana cikin hasararru



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 101

وَكَيۡفَ تَكۡفُرُونَ وَأَنتُمۡ تُتۡلَىٰ عَلَيۡكُمۡ ءَايَٰتُ ٱللَّهِ وَفِيكُمۡ رَسُولُهُۥۗ وَمَن يَعۡتَصِم بِٱللَّهِ فَقَدۡ هُدِيَ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

Ta yaya kuma za ku kafirce, ga shi kuwa ana karanta muku ayoyin Allah, kuma Manzonsa yana tare da ku? Duk kuwa wanda ya riqi Allah, to haqiqa an shiryar da shi tafarki madaidaici



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 125

وَمَنۡ أَحۡسَنُ دِينٗا مِّمَّنۡ أَسۡلَمَ وَجۡهَهُۥ لِلَّهِ وَهُوَ مُحۡسِنٞ وَٱتَّبَعَ مِلَّةَ إِبۡرَٰهِيمَ حَنِيفٗاۗ وَٱتَّخَذَ ٱللَّهُ إِبۡرَٰهِيمَ خَلِيلٗا

Kuma wane ne mafi kyawun addini fiye da wanda ya miqa fuskarsa ga Allah, yana kuma mai kaxaita Allah, sannan ya bi addinin Ibrahimu yana mai karkacewa duk wata varna? Allah kuwa Ya riqi Ibrahimu a matsayin badaxayi



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 16

يَهۡدِي بِهِ ٱللَّهُ مَنِ ٱتَّبَعَ رِضۡوَٰنَهُۥ سُبُلَ ٱلسَّلَٰمِ وَيُخۡرِجُهُم مِّنَ ٱلظُّلُمَٰتِ إِلَى ٱلنُّورِ بِإِذۡنِهِۦ وَيَهۡدِيهِمۡ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

Da shi ne Allah Yake shiryar da wanda ya bi yardarsa hanyoyi na aminci, kuma Yake fitar da su daga duffai zuwa ga haske da izininsa, kuma Yana shiryar da su zuwa ga tafarki madaidaici



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 136

وَجَعَلُواْ لِلَّهِ مِمَّا ذَرَأَ مِنَ ٱلۡحَرۡثِ وَٱلۡأَنۡعَٰمِ نَصِيبٗا فَقَالُواْ هَٰذَا لِلَّهِ بِزَعۡمِهِمۡ وَهَٰذَا لِشُرَكَآئِنَاۖ فَمَا كَانَ لِشُرَكَآئِهِمۡ فَلَا يَصِلُ إِلَى ٱللَّهِۖ وَمَا كَانَ لِلَّهِ فَهُوَ يَصِلُ إِلَىٰ شُرَكَآئِهِمۡۗ سَآءَ مَا يَحۡكُمُونَ

Kuma sun sanya wa Allah wani kaso cikin abin da Ya halitta na amfanin gona da dabbobin gida, sai suka riqa cewa: “Wannan kaso na Allah ne”, a riyawarsu, “Wannan kuma na gumakanmu ne;” sannan abin da ya kasance na gumakansu ba zai isa ga Allah ba; abin da kuwa ya kasance na Allah, to shi zai isa ga gumakansu. Abin da suke hukuntawa ya munana[1]


1- Mushirikan Larabawa sukan kasa amfanin gonarsu da dabbobinsu kaso biyu, kaso xaya su ce na Allah ne, kaso na biyun kuma su ce na gumakansu ne. To idan kason gumakansu ya shiga cikin kason Allah sai su dawo da shi wurinsu, amma idan kason da suka ware wa Allah ya shiga na gumakansu ba za su dawo da shi ba.


Capítulo: Suratul An’am

Verso : 153

وَأَنَّ هَٰذَا صِرَٰطِي مُسۡتَقِيمٗا فَٱتَّبِعُوهُۖ وَلَا تَتَّبِعُواْ ٱلسُّبُلَ فَتَفَرَّقَ بِكُمۡ عَن سَبِيلِهِۦۚ ذَٰلِكُمۡ وَصَّىٰكُم بِهِۦ لَعَلَّكُمۡ تَتَّقُونَ

“Kuma lalle wannan shi ne tafarkina miqaqqe, don haka ku bi shi; kada ku bi waxansu hanyoyi daban, sai su raba ku da hanyarsa. Wannan shi ne abin da (Allah) Yake yi muku wasicci da shi don ku samu taqawa.”



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 161

قُلۡ إِنَّنِي هَدَىٰنِي رَبِّيٓ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ دِينٗا قِيَمٗا مِّلَّةَ إِبۡرَٰهِيمَ حَنِيفٗاۚ وَمَا كَانَ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ

Ka ce: “Lalle ni, Ubangijina Ya shiryar da ni zuwa ga tafarki madaidaici, shi ne addini miqaqqe, addinin Ibrahimu wanda ya karkace wa varna, kuma bai zama daga masu shirka ba.”



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 29

قُلۡ أَمَرَ رَبِّي بِٱلۡقِسۡطِۖ وَأَقِيمُواْ وُجُوهَكُمۡ عِندَ كُلِّ مَسۡجِدٖ وَٱدۡعُوهُ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَۚ كَمَا بَدَأَكُمۡ تَعُودُونَ

Ka ce: “Ubangijina Ya yi umarni da adalci; kuma ku tsai da fuskokinku (don Allah) a kowace salla, ku kuma roqe Shi kuna masu tsantsanta addini gare Shi. Kamar yadda Ya fari halittarku, haka za ku koma (wurinsa)



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 33

هُوَ ٱلَّذِيٓ أَرۡسَلَ رَسُولَهُۥ بِٱلۡهُدَىٰ وَدِينِ ٱلۡحَقِّ لِيُظۡهِرَهُۥ عَلَى ٱلدِّينِ كُلِّهِۦ وَلَوۡ كَرِهَ ٱلۡمُشۡرِكُونَ

Shi ne wanda Ya aiko Manzonsa da shiriya da kuma addini na gaskiya don Ya xora shi a kan dukkanin addinai, ko da kuwa mushrikai sun qi



Capítulo: Suratu Yunus

Verso : 25

وَٱللَّهُ يَدۡعُوٓاْ إِلَىٰ دَارِ ٱلسَّلَٰمِ وَيَهۡدِي مَن يَشَآءُ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

Allah kuwa Yana kira ne zuwa gidan aminci (wato Aljanna), Yana kuma shiryar da wanda Ya ga dama zuwa tafarki madaidaici



Capítulo: Suratu Hud

Verso : 56

إِنِّي تَوَكَّلۡتُ عَلَى ٱللَّهِ رَبِّي وَرَبِّكُمۚ مَّا مِن دَآبَّةٍ إِلَّا هُوَ ءَاخِذُۢ بِنَاصِيَتِهَآۚ إِنَّ رَبِّي عَلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

“Lalle ni na dogara ga Allah, Ubangijina kuma Ubangijinku. Babu wata dabba face Shi ne Yake riqe da makwarkwaxarta. Lalle Ubangijina a kan tafarki madaidaici Yake



Capítulo: Suratu Ibrahim

Verso : 40

رَبِّ ٱجۡعَلۡنِي مُقِيمَ ٱلصَّلَوٰةِ وَمِن ذُرِّيَّتِيۚ رَبَّنَا وَتَقَبَّلۡ دُعَآءِ

“Ya Ubangijina, Ka sanya ni in zama mai tsayar da salla da kuma zuriyata. Ya Ubangijinmu, Ka karvi addu’ata



Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 76

وَضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلٗا رَّجُلَيۡنِ أَحَدُهُمَآ أَبۡكَمُ لَا يَقۡدِرُ عَلَىٰ شَيۡءٖ وَهُوَ كَلٌّ عَلَىٰ مَوۡلَىٰهُ أَيۡنَمَا يُوَجِّههُّ لَا يَأۡتِ بِخَيۡرٍ هَلۡ يَسۡتَوِي هُوَ وَمَن يَأۡمُرُ بِٱلۡعَدۡلِ وَهُوَ عَلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

Allah kuma Ya ba da wani misali da mutum biyu, xayansu bebe ne ba ya iya yin komai, kuma ya zama nauyi a kan mai gidansa, duk inda ya fuskantar da shi ba zai zo da wani alheri ba. Yanzu shi zai yi daidai da wanda yake umarni da adalci kuma yana bisa tafarki madaidaici?



Capítulo: Suratu Maryam

Verso : 36

وَإِنَّ ٱللَّهَ رَبِّي وَرَبُّكُمۡ فَٱعۡبُدُوهُۚ هَٰذَا صِرَٰطٞ مُّسۡتَقِيمٞ

“Lalle kuma Allah shi ne Ubangijina kuma Ubangijinku, sai ku bauta masa. Wannan ita ce hanya madaidaiciya.”



Capítulo: Suratul Anbiya

Verso : 22

لَوۡ كَانَ فِيهِمَآ ءَالِهَةٌ إِلَّا ٱللَّهُ لَفَسَدَتَاۚ فَسُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ رَبِّ ٱلۡعَرۡشِ عَمَّا يَصِفُونَ

Da ya zamana akwai wasu ababen bauta ba Allah ba a cikinsu (wato sammai da qasa), to da sun lalace. Sai dai tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin Al’arshi game da abin da suke siffata (Shi da shi)



Capítulo: Suratul Anbiya

Verso : 92

إِنَّ هَٰذِهِۦٓ أُمَّتُكُمۡ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ وَأَنَا۠ رَبُّكُمۡ فَٱعۡبُدُونِ

Lallai wannan addini naku guda xaya ne (wato Musulunci), kuma Ni ne Ubangijinku, to ku bauta min



Capítulo: Suratul Hajji

Verso : 54

وَلِيَعۡلَمَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ أَنَّهُ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّكَ فَيُؤۡمِنُواْ بِهِۦ فَتُخۡبِتَ لَهُۥ قُلُوبُهُمۡۗ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَهَادِ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

Don kuma waxanda aka bai wa ilimi su san cewa shi (Alqur’ani) gaskiya ne daga Ubangijinka yake, sai su yi imani da shi sai zukatansu su nutsu da shi. Kuma lalle Allah tabbas Mai shiryar da waxanda suka yi imani ne zuwa ga tafarki madaidaici



Capítulo: Suratul Hajji

Verso : 78

وَجَٰهِدُواْ فِي ٱللَّهِ حَقَّ جِهَادِهِۦۚ هُوَ ٱجۡتَبَىٰكُمۡ وَمَا جَعَلَ عَلَيۡكُمۡ فِي ٱلدِّينِ مِنۡ حَرَجٖۚ مِّلَّةَ أَبِيكُمۡ إِبۡرَٰهِيمَۚ هُوَ سَمَّىٰكُمُ ٱلۡمُسۡلِمِينَ مِن قَبۡلُ وَفِي هَٰذَا لِيَكُونَ ٱلرَّسُولُ شَهِيدًا عَلَيۡكُمۡ وَتَكُونُواْ شُهَدَآءَ عَلَى ٱلنَّاسِۚ فَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ وَٱعۡتَصِمُواْ بِٱللَّهِ هُوَ مَوۡلَىٰكُمۡۖ فَنِعۡمَ ٱلۡمَوۡلَىٰ وَنِعۡمَ ٱلنَّصِيرُ

Kuma ku yi jihadi wajen (xaukaka addinin) Allah iyakar iyawarku. Shi ne Ya zave ku, bai kuma sanya muku wani qunci ba cikin addini. Addinin Babanku ne Ibrahimu. (Allah) Shi ne Ya kira ku Musulmi tuntuni, da kuma cikin wannan (Alqur’ani) don Manzo ya zama shaida a gare ku, ku kuma ku zama shaida ga (sauran) mutane. To sai ku tsai da salla kuma ku ba da zakka, ku kuma yi riqo da (addinin) Allah, Shi ne Majivincin al’amarinku; to madalla da Majivinci, kuma madalla da Mataimaki