Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 61

وَإِذۡ قُلۡتُمۡ يَٰمُوسَىٰ لَن نَّصۡبِرَ عَلَىٰ طَعَامٖ وَٰحِدٖ فَٱدۡعُ لَنَا رَبَّكَ يُخۡرِجۡ لَنَا مِمَّا تُنۢبِتُ ٱلۡأَرۡضُ مِنۢ بَقۡلِهَا وَقِثَّآئِهَا وَفُومِهَا وَعَدَسِهَا وَبَصَلِهَاۖ قَالَ أَتَسۡتَبۡدِلُونَ ٱلَّذِي هُوَ أَدۡنَىٰ بِٱلَّذِي هُوَ خَيۡرٌۚ ٱهۡبِطُواْ مِصۡرٗا فَإِنَّ لَكُم مَّا سَأَلۡتُمۡۗ وَضُرِبَتۡ عَلَيۡهِمُ ٱلذِّلَّةُ وَٱلۡمَسۡكَنَةُ وَبَآءُو بِغَضَبٖ مِّنَ ٱللَّهِۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ كَانُواْ يَكۡفُرُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَيَقۡتُلُونَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّۚ ذَٰلِكَ بِمَا عَصَواْ وَّكَانُواْ يَعۡتَدُونَ

Kuma ku tuna lokacin da kuka ce: “Ya Musa, ba za mu iya haquri a kan abinci iri xaya ba, don haka ka roqa mana Ubangijinka Ya fitar mana (wani abincin) daga abin da qasa take tsirarwa, daga mabunqusanta da gurjinta da alkamarta da wakenta da albasarta.” Sai ya ce, “Yanzu kwa nemi musanya qasqantaccen abu da wanda yake shi ne mafifici? To ku sauka kowane gari, domin za ku samu abin da kuka roqa (a cikinsa).” Don haka sai aka sanya musu qasqanci da talauci, kuma suka koma da fushin Allah. Hakan ya faru gare su ne saboda sun kasance suna kafirce wa ayoyin Allah, kuma suna kashe annabawa ba tare da wani haqqi ba. Hakan ya faru saboda savon da suka yi da kuma ta’addancin da suka riqa yi



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 89

وَلَمَّا جَآءَهُمۡ كِتَٰبٞ مِّنۡ عِندِ ٱللَّهِ مُصَدِّقٞ لِّمَا مَعَهُمۡ وَكَانُواْ مِن قَبۡلُ يَسۡتَفۡتِحُونَ عَلَى ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فَلَمَّا جَآءَهُم مَّا عَرَفُواْ كَفَرُواْ بِهِۦۚ فَلَعۡنَةُ ٱللَّهِ عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ

Yayin da kuma wani littafi ya zo musu daga Allah, yana mai gaskata abin da yake tare da su, alhali kuma a da sun kasance suna addu’ar neman nasara a kan waxanda suka kafirta (mushrikai). To yayin da abin da suka sani ya zo musu sai suka kafirce masa[1]. Don haka la’anar Allah ta tabbata a kan kafirai


1- Kafin aiko Annabi Muhammadu (), idan faxa ya varke tsaknin Yahudu da Larabawa, Yahudu sukan ce, za a aiko wani annabi, idan ya bayyana za mu bi shi, mu haxa qarfi da shi mu yaqe ku. Yayin da Annabi () ya bayyana ba a cikinsu ba sai suka kafirce masa.


Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 90

بِئۡسَمَا ٱشۡتَرَوۡاْ بِهِۦٓ أَنفُسَهُمۡ أَن يَكۡفُرُواْ بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ بَغۡيًا أَن يُنَزِّلَ ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦ عَلَىٰ مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦۖ فَبَآءُو بِغَضَبٍ عَلَىٰ غَضَبٖۚ وَلِلۡكَٰفِرِينَ عَذَابٞ مُّهِينٞ

Tir da wannan abu da suka sayar da kawunansu da shi, wato suka kafirce wa abin da Allah Ya saukar, don hassadar cewa, (don me) Allah zai saukar da falalarsa ga wanda Ya ga dama daga bayinsa, sai suka wayi gari da fushin Allah a kan wani fushin. Kuma azaba ta wulaqanci ta tabbata ga kafirai



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 112

ضُرِبَتۡ عَلَيۡهِمُ ٱلذِّلَّةُ أَيۡنَ مَا ثُقِفُوٓاْ إِلَّا بِحَبۡلٖ مِّنَ ٱللَّهِ وَحَبۡلٖ مِّنَ ٱلنَّاسِ وَبَآءُو بِغَضَبٖ مِّنَ ٱللَّهِ وَضُرِبَتۡ عَلَيۡهِمُ ٱلۡمَسۡكَنَةُۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ كَانُواْ يَكۡفُرُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَيَقۡتُلُونَ ٱلۡأَنۢبِيَآءَ بِغَيۡرِ حَقّٖۚ ذَٰلِكَ بِمَا عَصَواْ وَّكَانُواْ يَعۡتَدُونَ

An haxa su da qasqanci a duk inda aka same su, sai dai waxanda suke riqe da wani alqawari daga Allah ko wani alqawari daga mutane, kuma sun dawo da wani fushi daga Allah, kuma an haxa su da talauci. Hakan kuwa saboda sun kasance suna kafirce wa ayoyin Allah, kuma suna kashe annabawa ba tare da wani haqqi ba, hakan yana faruwa ne saboda savo da suka yi, kuma sun kasance suna qetare iyaka



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 162

أَفَمَنِ ٱتَّبَعَ رِضۡوَٰنَ ٱللَّهِ كَمَنۢ بَآءَ بِسَخَطٖ مِّنَ ٱللَّهِ وَمَأۡوَىٰهُ جَهَنَّمُۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ

Shin yanzu wanda ya bi yardar Allah, zai yi kamar wanda ya dawo da fushin Allah, kuma makomarsa ta zamo Jahannama? Kuma tir da wannan makoma



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 93

وَمَن يَقۡتُلۡ مُؤۡمِنٗا مُّتَعَمِّدٗا فَجَزَآؤُهُۥ جَهَنَّمُ خَٰلِدٗا فِيهَا وَغَضِبَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِ وَلَعَنَهُۥ وَأَعَدَّ لَهُۥ عَذَابًا عَظِيمٗا

Duk kuwa wanda ya kashe mumini da gangan, to sakamakonsa wutar Jahannama ce, yana mai dawwama a cikinta, kuma Allah Ya yi fushi da shi, kuma Ya la’ance shi, kuma Ya yi masa tanadin azaba mai girma



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 80

تَرَىٰ كَثِيرٗا مِّنۡهُمۡ يَتَوَلَّوۡنَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْۚ لَبِئۡسَ مَا قَدَّمَتۡ لَهُمۡ أَنفُسُهُمۡ أَن سَخِطَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِمۡ وَفِي ٱلۡعَذَابِ هُمۡ خَٰلِدُونَ

Za ka ga yawancinsu suna nuna qauna ga waxanda suka kafirta. Lalle tir da irin abin da kawunansu suka gabatar, don kuwa Allah Ya yi fushi da su, kuma su masu dawwama ne cikin azaba



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 152

إِنَّ ٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ ٱلۡعِجۡلَ سَيَنَالُهُمۡ غَضَبٞ مِّن رَّبِّهِمۡ وَذِلَّةٞ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۚ وَكَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُفۡتَرِينَ

Lalle waxannan da suka riqi xan maraqi (abin bauta) fushin Ubangijinsu zai same su da qasqanci a cikin rayuwar duniya. Kuma kamar haka ne Muke saka wa masu qage



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 16

وَمَن يُوَلِّهِمۡ يَوۡمَئِذٖ دُبُرَهُۥٓ إِلَّا مُتَحَرِّفٗا لِّقِتَالٍ أَوۡ مُتَحَيِّزًا إِلَىٰ فِئَةٖ فَقَدۡ بَآءَ بِغَضَبٖ مِّنَ ٱللَّهِ وَمَأۡوَىٰهُ جَهَنَّمُۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ

Duk kuwa wanda ya ba su baya a wannan ranar idan dai ba wanda ya gudu da niyyar juyowa ya kai xauki ko kuma mai niyyar haxuwa da wata jama’a (ta mayaqa) ba, to haqiqa ya komo da fushin Allah, kuma makomarsa Jahannama ce; wannan makoma kuwa ta munana



Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 106

مَن كَفَرَ بِٱللَّهِ مِنۢ بَعۡدِ إِيمَٰنِهِۦٓ إِلَّا مَنۡ أُكۡرِهَ وَقَلۡبُهُۥ مُطۡمَئِنُّۢ بِٱلۡإِيمَٰنِ وَلَٰكِن مَّن شَرَحَ بِٱلۡكُفۡرِ صَدۡرٗا فَعَلَيۡهِمۡ غَضَبٞ مِّنَ ٱللَّهِ وَلَهُمۡ عَذَابٌ عَظِيمٞ

Wanda ya kafirce wa Allah bayan imaninsa, sai dai wanda aka tilasta wa alhali kuwa zuciyarsa ta cika da imani, amma kuma wanda ya buxe wa kafirci qirjinsa, to (waxannan) fushin Allah ya tabbata a kansu kuma suna da azaba mai girma



Capítulo: Suratu Xa Ha

Verso : 81

كُلُواْ مِن طَيِّبَٰتِ مَا رَزَقۡنَٰكُمۡ وَلَا تَطۡغَوۡاْ فِيهِ فَيَحِلَّ عَلَيۡكُمۡ غَضَبِيۖ وَمَن يَحۡلِلۡ عَلَيۡهِ غَضَبِي فَقَدۡ هَوَىٰ

Ku ci daga daxaxan abin da Muka arzuta ku da shi (na halal), kada kuwa ku qetare shi (zuwa haramun), sai fushina ya faxa muku; wanda kuwa fushina ya faxa masa, to haqiqa ya hallaka



Capítulo: Suratun Nur

Verso : 9

وَٱلۡخَٰمِسَةَ أَنَّ غَضَبَ ٱللَّهِ عَلَيۡهَآ إِن كَانَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ

(Rantsuwa) ta biyar kuwa kan cewa lalle fushin Allah ya hau kanta idan ya kasance daga masu gaskiya



Capítulo: Suratu Faxir

Verso : 39

هُوَ ٱلَّذِي جَعَلَكُمۡ خَلَـٰٓئِفَ فِي ٱلۡأَرۡضِۚ فَمَن كَفَرَ فَعَلَيۡهِ كُفۡرُهُۥۖ وَلَا يَزِيدُ ٱلۡكَٰفِرِينَ كُفۡرُهُمۡ عِندَ رَبِّهِمۡ إِلَّا مَقۡتٗاۖ وَلَا يَزِيدُ ٱلۡكَٰفِرِينَ كُفۡرُهُمۡ إِلَّا خَسَارٗا

Shi ne wanda Ya sanya ku halifofi a bayan qasa. Saboda haka wanda ya kafirta sakamakon kafircinsa yana kansa, kuma kafircin kafirai ba zai qara musu komai ba a wurin Ubangijinsu sai qiyayya; kuma kafircin kafirai ba zai qara musu komai ba sai hasara



Capítulo: Suratu Ghafir

Verso : 10

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ يُنَادَوۡنَ لَمَقۡتُ ٱللَّهِ أَكۡبَرُ مِن مَّقۡتِكُمۡ أَنفُسَكُمۡ إِذۡ تُدۡعَوۡنَ إِلَى ٱلۡإِيمَٰنِ فَتَكۡفُرُونَ

Lalle waxanda suka kafirta ana kiran su cewa: “Tabbas fushin Allah da ku ya fi girman fushinku ga kawunanku, lokacin da ake kiran ku zuwa imani (a duniya) sai kuke kafircewa.”



Capítulo: Suratu Ghafir

Verso : 35

ٱلَّذِينَ يُجَٰدِلُونَ فِيٓ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ بِغَيۡرِ سُلۡطَٰنٍ أَتَىٰهُمۡۖ كَبُرَ مَقۡتًا عِندَ ٱللَّهِ وَعِندَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْۚ كَذَٰلِكَ يَطۡبَعُ ٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ قَلۡبِ مُتَكَبِّرٖ جَبَّارٖ

Waxanda suke yin jayayya game da ayoyin Allah ba tare da wata hujja da ta zo musu ba; qyamar (wannan) a wurin Allah da wurin waxanda suka yi imani ta girmama. Kamar haka ne Allah Yake toshe zuciyar duk wani mai girman kai, mai tsaurin rai



Capítulo: Suratus Shura

Verso : 16

وَٱلَّذِينَ يُحَآجُّونَ فِي ٱللَّهِ مِنۢ بَعۡدِ مَا ٱسۡتُجِيبَ لَهُۥ حُجَّتُهُمۡ دَاحِضَةٌ عِندَ رَبِّهِمۡ وَعَلَيۡهِمۡ غَضَبٞ وَلَهُمۡ عَذَابٞ شَدِيدٌ

Waxanda kuma suke jayayya game da Allah bayan an amsa masa (kiransa), to hujjarsu vatacciya ce a wurin Ubangijinsu, kuma fushi ya hau kansu, kuma suna da azaba mai tsanani



Capítulo: Suratu Muhammad

Verso : 27

فَكَيۡفَ إِذَا تَوَفَّتۡهُمُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ يَضۡرِبُونَ وُجُوهَهُمۡ وَأَدۡبَٰرَهُمۡ

To yaya za su zama lokacin da mala’iku za su karvi rayukansu suna dukan fuskokinsu da bayansu?



Capítulo: Suratu Muhammad

Verso : 28

ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمُ ٱتَّبَعُواْ مَآ أَسۡخَطَ ٱللَّهَ وَكَرِهُواْ رِضۡوَٰنَهُۥ فَأَحۡبَطَ أَعۡمَٰلَهُمۡ

Wannan kuwa saboda lalle su, sun bi abin da yake fusata Allah suka kuma qi bin yardarsa, sai ya rusa ayyukansa



Capítulo: Suratul Fat’h

Verso : 6

وَيُعَذِّبَ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ وَٱلۡمُنَٰفِقَٰتِ وَٱلۡمُشۡرِكِينَ وَٱلۡمُشۡرِكَٰتِ ٱلظَّآنِّينَ بِٱللَّهِ ظَنَّ ٱلسَّوۡءِۚ عَلَيۡهِمۡ دَآئِرَةُ ٱلسَّوۡءِۖ وَغَضِبَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِمۡ وَلَعَنَهُمۡ وَأَعَدَّ لَهُمۡ جَهَنَّمَۖ وَسَآءَتۡ مَصِيرٗا

Ya kuma azabtar da munafukai maza da mata, da mushirikai maza da mata, masu munana zato ga Allah. Mummunar azaba ta koma a kansu; kuma Allah Ya yi fushi da su, Ya kuma la’ance su, Ya kuma tanadar musu Jahannama; makoma kuwa ta munana



Capítulo: Suratus Saff 

Verso : 3

كَبُرَ مَقۡتًا عِندَ ٱللَّهِ أَن تَقُولُواْ مَا لَا تَفۡعَلُونَ

Ya isa babban abin qi a wurin Allah, ku riqa faxin abin da ba kwa aikatawa