ثُمَّ تَوَلَّيۡتُم مِّنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَۖ فَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَرَحۡمَتُهُۥ لَكُنتُم مِّنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ
Sannan bayan haka sai kuka juya da baya, to ba domin falalar Allah da rahamarsa a gare ku ba, lalle da kun kasance daga cikin asararru
مَّا يَوَدُّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ وَلَا ٱلۡمُشۡرِكِينَ أَن يُنَزَّلَ عَلَيۡكُم مِّنۡ خَيۡرٖ مِّن رَّبِّكُمۡۚ وَٱللَّهُ يَخۡتَصُّ بِرَحۡمَتِهِۦ مَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ ذُو ٱلۡفَضۡلِ ٱلۡعَظِيمِ
Waxanda suka kafirta daga ma’abota littafi da mushrikai ba sa qaunar a saukar muku da wani alheri daga Ubangijinku, sai dai Allah kuwa Yana kevance wanda Ya ga dama da rahamarsa, Allah kuma Mai babbar falala ne
وَإِلَٰهُكُمۡ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۖ لَّآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلرَّحۡمَٰنُ ٱلرَّحِيمُ
Kuma abin bautarku abin bauta ne Guda Xaya, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi. Shi ne Mai rahama, Mai jin qai
يَخۡتَصُّ بِرَحۡمَتِهِۦ مَن يَشَآءُۗ وَٱللَّهُ ذُو ٱلۡفَضۡلِ ٱلۡعَظِيمِ
“Yana kevantar wanda Ya ga dama da rahamarsa, kuma Allah Ma’abocin falala ne wadda take mai girma.”
وَلَئِن قُتِلۡتُمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ أَوۡ مُتُّمۡ لَمَغۡفِرَةٞ مِّنَ ٱللَّهِ وَرَحۡمَةٌ خَيۡرٞ مِّمَّا يَجۡمَعُونَ
Kuma lalle idan ma har an kashe ku a hanyar Allah ko kuma kuka mutu, to kuna da gafara ta musamman a wajen Allah da kuma rahama, wanda shi ne mafi alheri fiye da abin da suke tarawa
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَأۡكُلُوٓاْ أَمۡوَٰلَكُم بَيۡنَكُم بِٱلۡبَٰطِلِ إِلَّآ أَن تَكُونَ تِجَٰرَةً عَن تَرَاضٖ مِّنكُمۡۚ وَلَا تَقۡتُلُوٓاْ أَنفُسَكُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِكُمۡ رَحِيمٗا
Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku ci dukiyoyinku a tsakaninku ta hanyar rashin gaskiya, sai dai in ya kasance kasuwanci ne bisa yarjejeniya a tsakaninku. Kuma kada ku kashe kawunanku. Lalle Allah Ya kasance Mai tausaya muku ne
وَإِذَا جَآءَهُمۡ أَمۡرٞ مِّنَ ٱلۡأَمۡنِ أَوِ ٱلۡخَوۡفِ أَذَاعُواْ بِهِۦۖ وَلَوۡ رَدُّوهُ إِلَى ٱلرَّسُولِ وَإِلَىٰٓ أُوْلِي ٱلۡأَمۡرِ مِنۡهُمۡ لَعَلِمَهُ ٱلَّذِينَ يَسۡتَنۢبِطُونَهُۥ مِنۡهُمۡۗ وَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَرَحۡمَتُهُۥ لَٱتَّبَعۡتُمُ ٱلشَّيۡطَٰنَ إِلَّا قَلِيلٗا
Kuma idan wani lamari ya zo musu wanda ya shafi zaman lafiya ko tsoro, sai su yaxa shi. Da a ce sun mayar da shi zuwa ga wannan Manzo da shugabanni daga cikinsu, da lalle wanxanda suke bin qwaqqwafin al’amarin sun san (dacewar a yaxa shi ko a’a). Kuma ba don falalar Allah da rahamarsa a gare ku ba, tabbas da kun bi Shaixan, in ban da ‘yan kaxan (daga cikinku)
دَرَجَٰتٖ مِّنۡهُ وَمَغۡفِرَةٗ وَرَحۡمَةٗۚ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمًا
Wasu darajoji masu yawa daga gare Shi da gafara da kuma jin qai. Kuma Allah Ya kasance Mai yawan gafara ne, Mai yawan jin qai
وَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكَ وَرَحۡمَتُهُۥ لَهَمَّت طَّآئِفَةٞ مِّنۡهُمۡ أَن يُضِلُّوكَ وَمَا يُضِلُّونَ إِلَّآ أَنفُسَهُمۡۖ وَمَا يَضُرُّونَكَ مِن شَيۡءٖۚ وَأَنزَلَ ٱللَّهُ عَلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَعَلَّمَكَ مَا لَمۡ تَكُن تَعۡلَمُۚ وَكَانَ فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكَ عَظِيمٗا
Ba don falalar Allah da rahamarsa a kanka ba kuwa, lalle da waxansu jama’a daga cikinsu sun yi niyyar su vatar da kai, ba kuwa kowa za su iya vatarwa ba sai dai kawunansu; kuma ba za su cuce ka da komai ba. Kuma Allah Ya saukar maka da Littafi da hikima, kuma Ya sanar da kai abin da a da ba ka sani ba. Kuma falalar Allah mai girma ce gare ka
فَأَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱللَّهِ وَٱعۡتَصَمُواْ بِهِۦ فَسَيُدۡخِلُهُمۡ فِي رَحۡمَةٖ مِّنۡهُ وَفَضۡلٖ وَيَهۡدِيهِمۡ إِلَيۡهِ صِرَٰطٗا مُّسۡتَقِيمٗا
To amma waxanda suka yi imani da Allah kuma suka yi garkuwa da Shi, to zai shigar da su cikin wata rahama tasa da kuma wata falala, kuma Ya shiryar da su tafarki madaidaici zuwa gare Shi
قُل لِّمَن مَّا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ قُل لِّلَّهِۚ كَتَبَ عَلَىٰ نَفۡسِهِ ٱلرَّحۡمَةَۚ لَيَجۡمَعَنَّكُمۡ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ لَا رَيۡبَ فِيهِۚ ٱلَّذِينَ خَسِرُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ فَهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ
Ka ce: “Abin da yake cikin sammai da qasa na wane ne?” Ka ce: “Na Allah ne.” Ya wajabta wa kansa yin rahama. Lalle tabbas zai tattara ku zuwa ranar tashin alqiyama wadda babu kokwanto game da ita. Waxanda suka yi hasarar kawunansu ba za su yi imani ba
وَإِذَا جَآءَكَ ٱلَّذِينَ يُؤۡمِنُونَ بِـَٔايَٰتِنَا فَقُلۡ سَلَٰمٌ عَلَيۡكُمۡۖ كَتَبَ رَبُّكُمۡ عَلَىٰ نَفۡسِهِ ٱلرَّحۡمَةَ أَنَّهُۥ مَنۡ عَمِلَ مِنكُمۡ سُوٓءَۢا بِجَهَٰلَةٖ ثُمَّ تَابَ مِنۢ بَعۡدِهِۦ وَأَصۡلَحَ فَأَنَّهُۥ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Kuma idan waxanda suke yin imani da ayoyinmu sun zo wurinka, to ka ce: “Sallama a gare ku;” Ubangijinku Ya wajabta wa kansa yin rahama cewa, lalle cikinku duk wanda ya aikata wani mummunan aiki bisa ga jahilci, sannan daga baya ya tuba kuma ya kyautata aiki, to Shi Mai gafara ne, Mai jin qai.”
وَرَبُّكَ ٱلۡغَنِيُّ ذُو ٱلرَّحۡمَةِۚ إِن يَشَأۡ يُذۡهِبۡكُمۡ وَيَسۡتَخۡلِفۡ مِنۢ بَعۡدِكُم مَّا يَشَآءُ كَمَآ أَنشَأَكُم مِّن ذُرِّيَّةِ قَوۡمٍ ءَاخَرِينَ
Kuma Ubangijinka Shi ne Mawadaci, Mai rahama. Idan Ya ga dama sai Ya tafiyar da ku, kuma Ya maye gurbinku da waxanda Ya ga dama, kamar yadda Ya fare ku daga zurriyar waxansu mutanen daban
فَإِن كَذَّبُوكَ فَقُل رَّبُّكُمۡ ذُو رَحۡمَةٖ وَٰسِعَةٖ وَلَا يُرَدُّ بَأۡسُهُۥ عَنِ ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡمُجۡرِمِينَ
Sannan idan sun qaryata ka, to ka ce: “Ubangijinku Ma’abocin rahama mayalwaciya ne. Kuma ba a iya mayar da azabarsa daga mutanen da suke masu laifi.”
وَلَا تُفۡسِدُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ بَعۡدَ إِصۡلَٰحِهَا وَٱدۡعُوهُ خَوۡفٗا وَطَمَعًاۚ إِنَّ رَحۡمَتَ ٱللَّهِ قَرِيبٞ مِّنَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Kuma kada ku yi varna a bayan qasa bayan gyara ta, kuma ku bauta masa kuna masu tsoro da kwaxayi. Lalle rahamar Allah a kusa take da masu kyautatawa
۞وَٱكۡتُبۡ لَنَا فِي هَٰذِهِ ٱلدُّنۡيَا حَسَنَةٗ وَفِي ٱلۡأٓخِرَةِ إِنَّا هُدۡنَآ إِلَيۡكَۚ قَالَ عَذَابِيٓ أُصِيبُ بِهِۦ مَنۡ أَشَآءُۖ وَرَحۡمَتِي وَسِعَتۡ كُلَّ شَيۡءٖۚ فَسَأَكۡتُبُهَا لِلَّذِينَ يَتَّقُونَ وَيُؤۡتُونَ ٱلزَّكَوٰةَ وَٱلَّذِينَ هُم بِـَٔايَٰتِنَا يُؤۡمِنُونَ
“Kuma Ka rubuta mana kyakkyawan abu a cikin wannan duniyar, haka ma a lahira, lalle mu mun tuba zuwa gare Ka.” (Allah) Ya ce: “Ina saukar da azabata a kan wanda Na ga dama; rahamata kuwa ta yalwaci komai. Don haka da sannu zan rubuta ta ga waxanda suke kiyaye dokokin Allah, kuma suke bayar da zakka da kuma waxanda suke yin imani da ayoyinmu
وَمِنۡهُمُ ٱلَّذِينَ يُؤۡذُونَ ٱلنَّبِيَّ وَيَقُولُونَ هُوَ أُذُنٞۚ قُلۡ أُذُنُ خَيۡرٖ لَّكُمۡ يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَيُؤۡمِنُ لِلۡمُؤۡمِنِينَ وَرَحۡمَةٞ لِّلَّذِينَ ءَامَنُواْ مِنكُمۡۚ وَٱلَّذِينَ يُؤۡذُونَ رَسُولَ ٱللَّهِ لَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ
Daga cikinsu kuma akwai waxanda suke cutar Annabi suna kuma cewa: “Shi mai saurare ne kawai[1].” Ka ce (da su: Shi) “Mai sauraren alheri ne dominku; yana imani da Allah, yana kuma gaskata muminai, kuma rahama ne ga waxanda suka yi imani daga cikinku.” Waxanda kuwa suke cutar Manzon Allah suna da azaba mai raxaxi
1- Wai shi mai xaukar maganganu ne kawai yana yarda da su ba tare da ya tantance gaskiyarsu da rashinta ba.
وَمِنَ ٱلۡأَعۡرَابِ مَن يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَيَتَّخِذُ مَا يُنفِقُ قُرُبَٰتٍ عِندَ ٱللَّهِ وَصَلَوَٰتِ ٱلرَّسُولِۚ أَلَآ إِنَّهَا قُرۡبَةٞ لَّهُمۡۚ سَيُدۡخِلُهُمُ ٱللَّهُ فِي رَحۡمَتِهِۦٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Daga mutanen qauye xin kuma akwai waxanda suke yin imani da Allah da ranar lahira, suke kuma xaukar abin da suke ciyarwa (hanyoyi ne) na samun kusanci ga Allah da kuma addu’o’in Manzo. Lalle wannan ibada ce gare su. Allah zai shigar da su cikin rahamarsa. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai
قُلۡ بِفَضۡلِ ٱللَّهِ وَبِرَحۡمَتِهِۦ فَبِذَٰلِكَ فَلۡيَفۡرَحُواْ هُوَ خَيۡرٞ مِّمَّا يَجۡمَعُونَ
Ka ce: “Da falalar Allah da rahamarsa, sai su yi farin ciki da wannan; shi ya fi alheri daga abin da suke tarawa (na dukiya).”
وَلَئِنۡ أَذَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ مِنَّا رَحۡمَةٗ ثُمَّ نَزَعۡنَٰهَا مِنۡهُ إِنَّهُۥ لَيَـُٔوسٞ كَفُورٞ
Kuma tabbas idan Muka xanxana wa mutum wata rahama daga gare Mu sannan Muka karve ta daga gare shi, lalle shi mai yawan yanke qauna ne, mai kuma yawan kafirci
وَكَذَٰلِكَ مَكَّنَّا لِيُوسُفَ فِي ٱلۡأَرۡضِ يَتَبَوَّأُ مِنۡهَا حَيۡثُ يَشَآءُۚ نُصِيبُ بِرَحۡمَتِنَا مَن نَّشَآءُۖ وَلَا نُضِيعُ أَجۡرَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Kamar haka ne Muka kafa Yusufu a bayan qasa; yana zama a cikinta inda ya ga dama. Muna bayar da rahamarmu ga wanda Muka ga dama, ba kuwa za Mu tozarta ladan masu kyautatawa ba
قَالَ وَمَن يَقۡنَطُ مِن رَّحۡمَةِ رَبِّهِۦٓ إِلَّا ٱلضَّآلُّونَ
Ya ce: “Ba wanda zai xebe qauna daga rahamar Ubangijinsa, sai vatattun (mutane).”
وَإِذِ ٱعۡتَزَلۡتُمُوهُمۡ وَمَا يَعۡبُدُونَ إِلَّا ٱللَّهَ فَأۡوُۥٓاْ إِلَى ٱلۡكَهۡفِ يَنشُرۡ لَكُمۡ رَبُّكُم مِّن رَّحۡمَتِهِۦ وَيُهَيِّئۡ لَكُم مِّنۡ أَمۡرِكُم مِّرۡفَقٗا
“Tun da kun qaurace musu tare da abin da suke bauta wa sai Allah, to sai ku tare a kogon, Ubangijinku zai yalwata muku rahamarsa ya kuma shirya muku hanyar rayuwa mai sauqi ga al’amuranku.”
وَرَبُّكَ ٱلۡغَفُورُ ذُو ٱلرَّحۡمَةِۖ لَوۡ يُؤَاخِذُهُم بِمَا كَسَبُواْ لَعَجَّلَ لَهُمُ ٱلۡعَذَابَۚ بَل لَّهُم مَّوۡعِدٞ لَّن يَجِدُواْ مِن دُونِهِۦ مَوۡئِلٗا
Ubangijinka kuwa Mai yawan gafara ne Ma’abocin rahama; da Yana kama su da abin da suka aikata, to da Ya gaggauta musu azaba. A’a, (ba Ya yin haka), sai dai suna da qayyadajjen lokaci wanda ba za su sami wata makauta ba daga gare shi
وَوَهَبۡنَا لَهُم مِّن رَّحۡمَتِنَا وَجَعَلۡنَا لَهُمۡ لِسَانَ صِدۡقٍ عَلِيّٗا
Muka kuma yi musu baiwa da rahamarmu, kuma Muka sanya musu kyakkyawan ambato maxaukaki[1]
1- Watau ya sa suka zamanto ababen yabo mai xorewa a gun kowa.
وَوَهَبۡنَا لَهُۥ مِن رَّحۡمَتِنَآ أَخَاهُ هَٰرُونَ نَبِيّٗا
Kuma cikin rahamarmu Muka yi masa baiwa da xan’uwansa Haruna (shi ma) Annabi
وَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَرَحۡمَتُهُۥ وَأَنَّ ٱللَّهَ تَوَّابٌ حَكِيمٌ
Ba don falalar Allah gare ku ba da rahamarsa, da kuma cewa Allah Mai karvar tuba ne, Mai hikima (to da ya kunyata maqaryaci)
وَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَرَحۡمَتُهُۥ فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِ لَمَسَّكُمۡ فِي مَآ أَفَضۡتُمۡ فِيهِ عَذَابٌ عَظِيمٌ
Ba don kuwa falalar Allah a gare ku da rahamarsa ba a duniya da lahira, to tabbas da azaba mai girma ta shafe ku game da abin da kuka kutsa cikinsa
وَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَرَحۡمَتُهُۥ وَأَنَّ ٱللَّهَ رَءُوفٞ رَّحِيمٞ
Ba don kuwa falalar Allah a gare ku da rahamarsa ba, da kuma cewa lalle Allah Mai tausayi ne, Mai rahama (da kun faxa cikin hallaka)
۞يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَتَّبِعُواْ خُطُوَٰتِ ٱلشَّيۡطَٰنِۚ وَمَن يَتَّبِعۡ خُطُوَٰتِ ٱلشَّيۡطَٰنِ فَإِنَّهُۥ يَأۡمُرُ بِٱلۡفَحۡشَآءِ وَٱلۡمُنكَرِۚ وَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَرَحۡمَتُهُۥ مَا زَكَىٰ مِنكُم مِّنۡ أَحَدٍ أَبَدٗا وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يُزَكِّي مَن يَشَآءُۗ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٞ
Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku bi hanyoyin Shaixan, wanda kuwa duk ya bi hanyoyin Shaixan, to lalle shi (Shaixan) umarni yake yi da aikata alfasha da abin qyama. Ba don kuma falalar Allah a gare ku da rahamarsa ba, da babu xaya daga cikinku da zai tsarkaka har abada, sai dai kuma Allah (Shi) Yake tsarkake wanda Ya ga dama, Allah kuwa Mai ji ne, Masani