Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 46

وَبَيۡنَهُمَا حِجَابٞۚ وَعَلَى ٱلۡأَعۡرَافِ رِجَالٞ يَعۡرِفُونَ كُلَّۢا بِسِيمَىٰهُمۡۚ وَنَادَوۡاْ أَصۡحَٰبَ ٱلۡجَنَّةِ أَن سَلَٰمٌ عَلَيۡكُمۡۚ لَمۡ يَدۡخُلُوهَا وَهُمۡ يَطۡمَعُونَ

A tsakaninsu kuma akwai wani shamaki. Kuma a kan tozon La’arafi akwai waxansu mazaje suna gane kowane (xan Aljanna da xan wuta) da alamominsu[1]. Kuma sai su kira ‘yan Aljanna cewa: “Amincin Allah ya tabbata a gare ku.” (Lokacin) ba su shige ta ba, amma suna kwaxayin (shigar ta)


1- Waxannan mazaje su ne waxanda kyawawan ayyukansu suka yi daidai da munanansu.


Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 47

۞وَإِذَا صُرِفَتۡ أَبۡصَٰرُهُمۡ تِلۡقَآءَ أَصۡحَٰبِ ٱلنَّارِ قَالُواْ رَبَّنَا لَا تَجۡعَلۡنَا مَعَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Idan kuma an juyar da idanuwansu vangaren ‘yan wuta sai su ce: “Ya Ubangijinmu, kada Ka sanya mu tare da mutane azzalumai.”



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 48

وَنَادَىٰٓ أَصۡحَٰبُ ٱلۡأَعۡرَافِ رِجَالٗا يَعۡرِفُونَهُم بِسِيمَىٰهُمۡ قَالُواْ مَآ أَغۡنَىٰ عَنكُمۡ جَمۡعُكُمۡ وَمَا كُنتُمۡ تَسۡتَكۡبِرُونَ

Sai ‘yan tozon La’arafi su kira waxansu mazaje da suke gane su da alamominsu[1], sai su ce: “Taronku bai wadatar da ku da komai ba, da girman kan da kuka kasance kuna yi


1- Su ne shugabannin mushirikai waxanda sun san su tun a duniya, kuma a nan ma lahira sun shaida su da alamominsu na ‘yan wuta.