وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَتَّخِذُ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَندَادٗا يُحِبُّونَهُمۡ كَحُبِّ ٱللَّهِۖ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَشَدُّ حُبّٗا لِّلَّهِۗ وَلَوۡ يَرَى ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓاْ إِذۡ يَرَوۡنَ ٱلۡعَذَابَ أَنَّ ٱلۡقُوَّةَ لِلَّهِ جَمِيعٗا وَأَنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعَذَابِ
Kuma akwai wasu mutane waxanda suke bauta wa wasu kishiyoyi ba Allah ba; suna son su kamar son Allah; waxanda kuwa suka yi imani sun fi son Allah (fiye da komai). Da a ce waxanda suka yi zalunci za su ga lokacin da suke ido huxu da azaba (to da sun gane) cewa, lalle duk wani qarfi na Allah ne gaba xaya, kuma lalle Allah Mai tsananin azaba ne
ءَامَنَ ٱلرَّسُولُ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡهِ مِن رَّبِّهِۦ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَۚ كُلٌّ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَمَلَـٰٓئِكَتِهِۦ وَكُتُبِهِۦ وَرُسُلِهِۦ لَا نُفَرِّقُ بَيۡنَ أَحَدٖ مِّن رُّسُلِهِۦۚ وَقَالُواْ سَمِعۡنَا وَأَطَعۡنَاۖ غُفۡرَانَكَ رَبَّنَا وَإِلَيۡكَ ٱلۡمَصِيرُ
Manzon ya yi imani da abin da aka saukar masa daga Ubangijinsa, muminai ma haka, kowanne ya yi imani da Allah da mala’ikunsa da littattafansa da manzanninsa, (suna cewa) : “Ba ma nuna bambanci tsakanin xaya daga cikin manzanninsa.” Kuma suka ce: “Mun ji kuma mun bi ; muna neman gafararka ya Ubangijinmu, kuma zuwa gare Ka ne makoma take
يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَيَأۡمُرُونَ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَيَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلۡمُنكَرِ وَيُسَٰرِعُونَ فِي ٱلۡخَيۡرَٰتِۖ وَأُوْلَـٰٓئِكَ مِنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ
Suna yin imani da Allah da ranar qarshe, kuma suna umarni da kyakkyawan aiki, kuma suna hana mummuna, kuma suna hanzari wajen ayyukan alheri, waxannan kuwa suna cikin salihan bayi
ٱلَّذِينَ قَالَ لَهُمُ ٱلنَّاسُ إِنَّ ٱلنَّاسَ قَدۡ جَمَعُواْ لَكُمۡ فَٱخۡشَوۡهُمۡ فَزَادَهُمۡ إِيمَٰنٗا وَقَالُواْ حَسۡبُنَا ٱللَّهُ وَنِعۡمَ ٱلۡوَكِيلُ
Su ne waxanda mutane suka ce da su: “Lalle mutanen (Makka) fa sun tara muku runduna, to sai ku tsorace su.” Amma sai hakan ya qara musu imani, sai suka riqa cewa: “Allah Ya wadace mu, kuma madalla da abin dogara (idan har Shi ne Allah).”
لَّـٰكِنِ ٱلرَّـٰسِخُونَ فِي ٱلۡعِلۡمِ مِنۡهُمۡ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَ يُؤۡمِنُونَ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ وَمَآ أُنزِلَ مِن قَبۡلِكَۚ وَٱلۡمُقِيمِينَ ٱلصَّلَوٰةَۚ وَٱلۡمُؤۡتُونَ ٱلزَّكَوٰةَ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ أُوْلَـٰٓئِكَ سَنُؤۡتِيهِمۡ أَجۡرًا عَظِيمًا
Amma masu zurfin ilimi daga cikinsu da muminai, suna imani da abin da aka saukar maka da abin da aka saukar gabaninka; musamman ma masu tsayar da salla, da kuma masu bayar da zakka, kuma masu imani da Allah da ranar qarshe. Waxannan ba da jimawa ba za Mu ba su lada mai girma
ٱلَّذِينَ يَتَّبِعُونَ ٱلرَّسُولَ ٱلنَّبِيَّ ٱلۡأُمِّيَّ ٱلَّذِي يَجِدُونَهُۥ مَكۡتُوبًا عِندَهُمۡ فِي ٱلتَّوۡرَىٰةِ وَٱلۡإِنجِيلِ يَأۡمُرُهُم بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَيَنۡهَىٰهُمۡ عَنِ ٱلۡمُنكَرِ وَيُحِلُّ لَهُمُ ٱلطَّيِّبَٰتِ وَيُحَرِّمُ عَلَيۡهِمُ ٱلۡخَبَـٰٓئِثَ وَيَضَعُ عَنۡهُمۡ إِصۡرَهُمۡ وَٱلۡأَغۡلَٰلَ ٱلَّتِي كَانَتۡ عَلَيۡهِمۡۚ فَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِهِۦ وَعَزَّرُوهُ وَنَصَرُوهُ وَٱتَّبَعُواْ ٱلنُّورَ ٱلَّذِيٓ أُنزِلَ مَعَهُۥٓ أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ
“(Su ne) waxanda suke bin Manzo Annabi Ummiyyi, wanda suke samun sa a rubuce a wurinsu a cikin Attaura da Linjila, yana umartar su da kyakkyawan abu, kuma yana hana su mummuna, kuma yana halatta musu daxaxan abubuwa, yana kuma haramta musu qazantattu, kuma yana sauke musu nauyaye-nauyayensu da ququmce-ququmcen da suka kasance a kansu[1]. Don haka waxanda suka yi imani da shi, kuma suka qarfafe shi, suka kuma taimake shi, suka bi hasken da aka saukar tare da shi, waxannan su ne masu rabauta.”
1- Nauyaye-nauyayensu su ne abubuwa masu wuya da aka wajabta musu aiki da su a littafin Attaura. Ququmce-ququmcensu kuwa su ne abubuwan da aka tsananta musu haramcinsu masu kama da ququmi.
إِنَّمَا ٱلۡمُؤۡمِنُونَ ٱلَّذِينَ إِذَا ذُكِرَ ٱللَّهُ وَجِلَتۡ قُلُوبُهُمۡ وَإِذَا تُلِيَتۡ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتُهُۥ زَادَتۡهُمۡ إِيمَٰنٗا وَعَلَىٰ رَبِّهِمۡ يَتَوَكَّلُونَ
Muminai na haqiqa (su ne) kaxai waxanda idan aka ambaci Allah, sai zukatansu su raurawa, idan kuma aka karanta musu ayoyinsa, sai su qara musu imani, kuma ga Ubangijinsu ne kawai suke dogara
ٱلَّذِينَ يُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَمِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ يُنفِقُونَ
Waxanda suke tsayar da salla kuma suke ciyarwa daga abin da muka arzurta su
أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ حَقّٗاۚ لَّهُمۡ دَرَجَٰتٌ عِندَ رَبِّهِمۡ وَمَغۡفِرَةٞ وَرِزۡقٞ كَرِيمٞ
Waxannan su ne muminai na haqiqa. Suna da muqamai a wurin Ubangijinsu da kuma gafara da arziki na karamci
وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَهَاجَرُواْ وَجَٰهَدُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَٱلَّذِينَ ءَاوَواْ وَّنَصَرُوٓاْ أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ حَقّٗاۚ لَّهُم مَّغۡفِرَةٞ وَرِزۡقٞ كَرِيمٞ
Waxanda kuma suka yi imani kuma suka yi hijira suka kuma yi yaqi saboda Allah, da waxanda kuma suka sauki (masu hijira) suka kuma taimaka, waxannan su ne muminai na gaskiya. Suna da (sakamakon) gafara da kuma arziki na karamci
لَا يَسۡتَـٔۡذِنُكَ ٱلَّذِينَ يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ أَن يُجَٰهِدُواْ بِأَمۡوَٰلِهِمۡ وَأَنفُسِهِمۡۗ وَٱللَّهُ عَلِيمُۢ بِٱلۡمُتَّقِينَ
Waxanda suka yi imani da Allah da ranar lahira ba sa neman izininka don kada su yi yaqi da dukiyoyinsu da kawunansu. Allah kuwa yana sane da masu taqawa
وَٱلۡمُؤۡمِنُونَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتُ بَعۡضُهُمۡ أَوۡلِيَآءُ بَعۡضٖۚ يَأۡمُرُونَ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَيَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلۡمُنكَرِ وَيُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَيُؤۡتُونَ ٱلزَّكَوٰةَ وَيُطِيعُونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥٓۚ أُوْلَـٰٓئِكَ سَيَرۡحَمُهُمُ ٱللَّهُۗ إِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٞ
Muminai maza da muninai mata kuwa masoyan juna ne: Suna yin umurni da kyakkyawan abu suna kuma hana mummunan, suna kuma tsai da salla suna ba da zakka suna kuma bin Allah da Manzonsa. Waxannan Allah zai yi musu rahama. Lalle Allah kuwa Mabuwayi ne Mai hikima
۞إِنَّ ٱللَّهَ ٱشۡتَرَىٰ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ أَنفُسَهُمۡ وَأَمۡوَٰلَهُم بِأَنَّ لَهُمُ ٱلۡجَنَّةَۚ يُقَٰتِلُونَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ فَيَقۡتُلُونَ وَيُقۡتَلُونَۖ وَعۡدًا عَلَيۡهِ حَقّٗا فِي ٱلتَّوۡرَىٰةِ وَٱلۡإِنجِيلِ وَٱلۡقُرۡءَانِۚ وَمَنۡ أَوۡفَىٰ بِعَهۡدِهِۦ مِنَ ٱللَّهِۚ فَٱسۡتَبۡشِرُواْ بِبَيۡعِكُمُ ٱلَّذِي بَايَعۡتُم بِهِۦۚ وَذَٰلِكَ هُوَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ
Lalle Allah Ya sayi rayuka da dukiyoyin muminai daga wurinsu cewa suna da Aljanna: Za su yi yaqi saboda Allah, sai su kashe su ma kuma a kashe su. Alqawari ne na gaskiya da Ya xaukar wa kansa a cikin Attaura da Linjila da Alqur’ani. Wane ne ya fi Allah cika alqawarinsa? Saboda haka sai ku yi farin ciki da cinikin nan naku da kuka yi da Shi. Wannan kuwa shi ne rabo mai girma
ٱلتَّـٰٓئِبُونَ ٱلۡعَٰبِدُونَ ٱلۡحَٰمِدُونَ ٱلسَّـٰٓئِحُونَ ٱلرَّـٰكِعُونَ ٱلسَّـٰجِدُونَ ٱلۡأٓمِرُونَ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَٱلنَّاهُونَ عَنِ ٱلۡمُنكَرِ وَٱلۡحَٰفِظُونَ لِحُدُودِ ٱللَّهِۗ وَبَشِّرِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Masu tuba, masu bauta, masu godiya, masu azumi, masu ruku’i, masu sujjada, masu yin umarni da aikin alheri masu kuma hani ga mummunan aiki, da masu kiyaye iyakokin Allah. To sai ka yi wa muminai (masu irin waxannan siffofin) albishir
وَإِذَا مَآ أُنزِلَتۡ سُورَةٞ فَمِنۡهُم مَّن يَقُولُ أَيُّكُمۡ زَادَتۡهُ هَٰذِهِۦٓ إِيمَٰنٗاۚ فَأَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ فَزَادَتۡهُمۡ إِيمَٰنٗا وَهُمۡ يَسۡتَبۡشِرُونَ
Idan kuwa aka saukar da wata sura, daga cikinsu akwai waxanda suke cewa: “Wane ne daga cikinku wannan ta qara masa imani?” To amma waxanda suka yi imani su kam ta qara musu imani alhali suna cike da farin ciki
قَدۡ أَفۡلَحَ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ
Haqiqa muminai sun rabauta
ٱلَّذِينَ هُمۡ فِي صَلَاتِهِمۡ خَٰشِعُونَ
(Su ne) waxanda suke masu qasqantar da kai a cikin sallarsu
وَٱلَّذِينَ هُمۡ عَنِ ٱللَّغۡوِ مُعۡرِضُونَ
Kuma waxanda suke masu kau da kai daga yasasshiyar magana
وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِلزَّكَوٰةِ فَٰعِلُونَ
Kuma waxanda suke masu aiwatar da zakka
وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِفُرُوجِهِمۡ حَٰفِظُونَ
Kuma waxanda suke masu kiyaye farjinsu
إِلَّا عَلَىٰٓ أَزۡوَٰجِهِمۡ أَوۡ مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُهُمۡ فَإِنَّهُمۡ غَيۡرُ مَلُومِينَ
Sai dai ga matayensu ko kuma qwara-qwaransu, to lalle su ba abin zargi ba ne
فَمَنِ ٱبۡتَغَىٰ وَرَآءَ ذَٰلِكَ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡعَادُونَ
Sannan duk wanda ya nemi (wata hanya) ba waxannan ba, to waxannan su ne masu qetare iyaka
وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِأَمَٰنَٰتِهِمۡ وَعَهۡدِهِمۡ رَٰعُونَ
Kuma waxanda suke masu kiyaye amanarsu da kuma alqawarinsu
وَٱلَّذِينَ هُمۡ عَلَىٰ صَلَوَٰتِهِمۡ يُحَافِظُونَ
Kuma waxanda suke kiyaye sallolinsu
أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡوَٰرِثُونَ
Waxannan su ne magada
ٱلَّذِينَ يَرِثُونَ ٱلۡفِرۡدَوۡسَ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ
Waxanda suke gadar (Aljannar) Firdausi, su madawwama ne a cikinta
إِنَّ ٱلَّذِينَ هُم مِّنۡ خَشۡيَةِ رَبِّهِم مُّشۡفِقُونَ
Lalle waxanda su suke cike da tsoron Ubangijinsu
وَٱلَّذِينَ هُم بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِمۡ يُؤۡمِنُونَ
Kuma waxanda suke imani da ayoyin Ubangijinsu
وَٱلَّذِينَ هُم بِرَبِّهِمۡ لَا يُشۡرِكُونَ
Kuma waxanda ba sa shirka da Ubangijinsu
وَٱلَّذِينَ يُؤۡتُونَ مَآ ءَاتَواْ وَّقُلُوبُهُمۡ وَجِلَةٌ أَنَّهُمۡ إِلَىٰ رَبِّهِمۡ رَٰجِعُونَ
Kuma waxanda suke ba da abin da suka bayar (na ayyukan kirki), alhali kuwa zukatansu suna tsorace[1], don kuwa lalle su masu komawa ne zuwa ga Ubangijinsu
1- Watau suna cike da tsoron za a karva ko ba za a karva ba.