Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 188

وَلَا تَأۡكُلُوٓاْ أَمۡوَٰلَكُم بَيۡنَكُم بِٱلۡبَٰطِلِ وَتُدۡلُواْ بِهَآ إِلَى ٱلۡحُكَّامِ لِتَأۡكُلُواْ فَرِيقٗا مِّنۡ أَمۡوَٰلِ ٱلنَّاسِ بِٱلۡإِثۡمِ وَأَنتُمۡ تَعۡلَمُونَ

Kuma kada ku ci dukiyoyinku a tsakaninku ta hanyar rashin gaskiya, haka kuma kada ku miqa dukiyoyinku zuwa ga masu shari’a, don kawai ku ci wani vangare na dukiyar mutane ta hanyar savo, alhali kuna sane



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 275

ٱلَّذِينَ يَأۡكُلُونَ ٱلرِّبَوٰاْ لَا يَقُومُونَ إِلَّا كَمَا يَقُومُ ٱلَّذِي يَتَخَبَّطُهُ ٱلشَّيۡطَٰنُ مِنَ ٱلۡمَسِّۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ قَالُوٓاْ إِنَّمَا ٱلۡبَيۡعُ مِثۡلُ ٱلرِّبَوٰاْۗ وَأَحَلَّ ٱللَّهُ ٱلۡبَيۡعَ وَحَرَّمَ ٱلرِّبَوٰاْۚ فَمَن جَآءَهُۥ مَوۡعِظَةٞ مِّن رَّبِّهِۦ فَٱنتَهَىٰ فَلَهُۥ مَا سَلَفَ وَأَمۡرُهُۥٓ إِلَى ٱللَّهِۖ وَمَنۡ عَادَ فَأُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ

Waxanda suke cin riba ba za su tashi ba (daga qaburburansu) sai kamar tashin mutumin da Shaixan yake bige shi da hauka. Hakan zai faru ne don sun ce: “Lalle kasuwanci kamar riba yake.” Kuma Allah Ya halatta kasuwanci, kuma Ya haramta riba. To duk wanda wa’azi ya zo masa daga wurin Ubangijinsa, sai ya daina, to abin da ya wuce a baya ya zama nasa, kuma al’amarinsa yana wurin Allah; wanda kuma ya sake komawa daga baya, to waxannan su ne ma’abota wuta, suna masu dawwama a cikinta



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 282

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا تَدَايَنتُم بِدَيۡنٍ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗى فَٱكۡتُبُوهُۚ وَلۡيَكۡتُب بَّيۡنَكُمۡ كَاتِبُۢ بِٱلۡعَدۡلِۚ وَلَا يَأۡبَ كَاتِبٌ أَن يَكۡتُبَ كَمَا عَلَّمَهُ ٱللَّهُۚ فَلۡيَكۡتُبۡ وَلۡيُمۡلِلِ ٱلَّذِي عَلَيۡهِ ٱلۡحَقُّ وَلۡيَتَّقِ ٱللَّهَ رَبَّهُۥ وَلَا يَبۡخَسۡ مِنۡهُ شَيۡـٔٗاۚ فَإِن كَانَ ٱلَّذِي عَلَيۡهِ ٱلۡحَقُّ سَفِيهًا أَوۡ ضَعِيفًا أَوۡ لَا يَسۡتَطِيعُ أَن يُمِلَّ هُوَ فَلۡيُمۡلِلۡ وَلِيُّهُۥ بِٱلۡعَدۡلِۚ وَٱسۡتَشۡهِدُواْ شَهِيدَيۡنِ مِن رِّجَالِكُمۡۖ فَإِن لَّمۡ يَكُونَا رَجُلَيۡنِ فَرَجُلٞ وَٱمۡرَأَتَانِ مِمَّن تَرۡضَوۡنَ مِنَ ٱلشُّهَدَآءِ أَن تَضِلَّ إِحۡدَىٰهُمَا فَتُذَكِّرَ إِحۡدَىٰهُمَا ٱلۡأُخۡرَىٰۚ وَلَا يَأۡبَ ٱلشُّهَدَآءُ إِذَا مَا دُعُواْۚ وَلَا تَسۡـَٔمُوٓاْ أَن تَكۡتُبُوهُ صَغِيرًا أَوۡ كَبِيرًا إِلَىٰٓ أَجَلِهِۦۚ ذَٰلِكُمۡ أَقۡسَطُ عِندَ ٱللَّهِ وَأَقۡوَمُ لِلشَّهَٰدَةِ وَأَدۡنَىٰٓ أَلَّا تَرۡتَابُوٓاْ إِلَّآ أَن تَكُونَ تِجَٰرَةً حَاضِرَةٗ تُدِيرُونَهَا بَيۡنَكُمۡ فَلَيۡسَ عَلَيۡكُمۡ جُنَاحٌ أَلَّا تَكۡتُبُوهَاۗ وَأَشۡهِدُوٓاْ إِذَا تَبَايَعۡتُمۡۚ وَلَا يُضَآرَّ كَاتِبٞ وَلَا شَهِيدٞۚ وَإِن تَفۡعَلُواْ فَإِنَّهُۥ فُسُوقُۢ بِكُمۡۗ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۖ وَيُعَلِّمُكُمُ ٱللَّهُۗ وَٱللَّهُ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٞ

Ya ku waxanda suka yi imani, idan kuka ba wa junanku bashi zuwa wani lokaci sananne, to ku rubuta shi, kuma a sami wani marubuci da zai rubuta a tsakaninku da adalci, kuma marubucin kar ya qi rubutawa kamar yadda Allah ya sanar da shi. Don haka ya rubuta, kuma shi wanda haqqi yake kansa sai ya yi shifta gare shi, kuma ya ji tsoron Allah Ubangijinsa, kuma kada ya tauye wani abu a cikinsa. To idan wanda haqqi yake kansa ya kasance wawa ne ko mai rauni ko ba shi da ikon ya yi shifta shi da kansa, to sai majivincin lamarinsa ya yi shifta (a madadinsa) da adalci. Kuma ku kafa shaidu biyu cikin mazajenku; kuma idan ba su kasance mazaje biyu ba, to sai a nemi namiji xaya da mata biyu daga shaidun da kuka yarda da su, saboda idan xaya daga cikinsu ta manta sai xayar ta tuna mata, kuma kada shaidun su qi zuwa idan an kiraye su, kuma kada ku qosa, ku rubuta shi, kaxan ne ko da yawa, zuwa cikar wa’adinsa. Abin da aka ambata mukun nan shi ne ya fi zama adalci a wajen Allah, kuma ya fi daidaita shaida, kuma shi ya fi kusata ku ta yadda ba za ku yi shakka ba, sai dai idan ya kasance ciniki ne hannu da hannu da kuke gudanar da shi tsakaninku; to babu laifi a kanku idan ba ku rubuta shi ba. Kuma ku kafa shaida idan kun yi hulxa ta ciniki, kuma kada marubuci ya yi cuta, haka shi ma mai shaida (kada ya yi cuta)[1]. Idan kuwa har kuka aikata haka, to lalle wannan fasiqanci ne a gare ku. Kuma ku kiyaye dokokin Allah, kuma Allah Yana sanar da ku (dokokinsa). Kuma Allah Masanin komai ne


1- Hakanan ayar tana nufin cewa, su ma kuma kada a cutar da su.


Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 283

۞وَإِن كُنتُمۡ عَلَىٰ سَفَرٖ وَلَمۡ تَجِدُواْ كَاتِبٗا فَرِهَٰنٞ مَّقۡبُوضَةٞۖ فَإِنۡ أَمِنَ بَعۡضُكُم بَعۡضٗا فَلۡيُؤَدِّ ٱلَّذِي ٱؤۡتُمِنَ أَمَٰنَتَهُۥ وَلۡيَتَّقِ ٱللَّهَ رَبَّهُۥۗ وَلَا تَكۡتُمُواْ ٱلشَّهَٰدَةَۚ وَمَن يَكۡتُمۡهَا فَإِنَّهُۥٓ ءَاثِمٞ قَلۡبُهُۥۗ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ عَلِيمٞ

Kuma idan kun kasance a halin tafiya, kuma ba ku sami marubuci ba, to sai a ba da jingina da za a karva, kuma idan sashinku ya amince wa sashi, to shi wanda aka amincewan ya bayar da amanarsa, kuma ya kiyayi Allah Ubangijinsa. Kuma kada ku voye shaida; duk wanda ya voye ta kuwa, to lalle shi zuciyarsa a cike take da savo. Kuma Allah Masanin abin da kuke aikatawa ne



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 77

إِنَّ ٱلَّذِينَ يَشۡتَرُونَ بِعَهۡدِ ٱللَّهِ وَأَيۡمَٰنِهِمۡ ثَمَنٗا قَلِيلًا أُوْلَـٰٓئِكَ لَا خَلَٰقَ لَهُمۡ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ وَلَا يُكَلِّمُهُمُ ٱللَّهُ وَلَا يَنظُرُ إِلَيۡهِمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَلَا يُزَكِّيهِمۡ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

Lalle waxanda suke musanya alqawarin Allah da rantse-rantsensu da wani xan farashi qanqani, waxannan ba su da wani rabo a lahira, kuma Allah ba zai yi musu magana ba, kuma ba zai dube su (duba na rahama) ba a ranar alqiyama, kuma ba zai tsarkake su ba, kuma suna da azaba mai raxaxi



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 130

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَأۡكُلُواْ ٱلرِّبَوٰٓاْ أَضۡعَٰفٗا مُّضَٰعَفَةٗۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku ci riba ninki-ba-ninkin, kuma ku kiyaye dokokin Allah don ku rabauta



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 29

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَأۡكُلُوٓاْ أَمۡوَٰلَكُم بَيۡنَكُم بِٱلۡبَٰطِلِ إِلَّآ أَن تَكُونَ تِجَٰرَةً عَن تَرَاضٖ مِّنكُمۡۚ وَلَا تَقۡتُلُوٓاْ أَنفُسَكُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِكُمۡ رَحِيمٗا

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku ci dukiyoyinku a tsakaninku ta hanyar rashin gaskiya, sai dai in ya kasance kasuwanci ne bisa yarjejeniya a tsakaninku. Kuma kada ku kashe kawunanku. Lalle Allah Ya kasance Mai tausaya muku ne



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 58

۞إِنَّ ٱللَّهَ يَأۡمُرُكُمۡ أَن تُؤَدُّواْ ٱلۡأَمَٰنَٰتِ إِلَىٰٓ أَهۡلِهَا وَإِذَا حَكَمۡتُم بَيۡنَ ٱلنَّاسِ أَن تَحۡكُمُواْ بِٱلۡعَدۡلِۚ إِنَّ ٱللَّهَ نِعِمَّا يَعِظُكُم بِهِۦٓۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ سَمِيعَۢا بَصِيرٗا

Lalle Allah Yana umartar ku da ku mayar da amanoni ga masu su, kuma idan za ku yi hukunci a tsakanin mutane, to ku yi hukunci da adalci. Lalle kam madalla da abin da Allah Yake muku wa’azi da shi. Lalle Allah Ya kasance Mai ji ne, Mai gani



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 1

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَوۡفُواْ بِٱلۡعُقُودِۚ أُحِلَّتۡ لَكُم بَهِيمَةُ ٱلۡأَنۡعَٰمِ إِلَّا مَا يُتۡلَىٰ عَلَيۡكُمۡ غَيۡرَ مُحِلِّي ٱلصَّيۡدِ وَأَنتُمۡ حُرُمٌۗ إِنَّ ٱللَّهَ يَحۡكُمُ مَا يُرِيدُ

Ya ku waxanda suka yi imani, ku cika alqawura. An halatta muku dabbobin ni’ima, sai dai abin da ake karanta muku (haramcinsa), ba kuna masu halatta farauta ba alhalin kuna cikin Harami, lalle Allah Yana hukunta abin da Yake nufi



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 152

وَلَا تَقۡرَبُواْ مَالَ ٱلۡيَتِيمِ إِلَّا بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُ حَتَّىٰ يَبۡلُغَ أَشُدَّهُۥۚ وَأَوۡفُواْ ٱلۡكَيۡلَ وَٱلۡمِيزَانَ بِٱلۡقِسۡطِۖ لَا نُكَلِّفُ نَفۡسًا إِلَّا وُسۡعَهَاۖ وَإِذَا قُلۡتُمۡ فَٱعۡدِلُواْ وَلَوۡ كَانَ ذَا قُرۡبَىٰۖ وَبِعَهۡدِ ٱللَّهِ أَوۡفُواْۚ ذَٰلِكُمۡ وَصَّىٰكُم بِهِۦ لَعَلَّكُمۡ تَذَكَّرُونَ

“Kuma kada ku kusanci dukiyar maraya sai da kyakkyawar niyya, har sai qarfinsa ya kawo; kuma ku cika ma’auni na mudu da na nauyi bisa adalci; ba ma xora wa rai sai abin da zai iya. Kuma idan za ku yi magana to ku yi adalci, ko da kuwa a kan xan’uwa ne na kusa; kuma lalle ku cika alqawarin Allah. Wannan ne abin da (Allah) Yake yi muku wasicci da shi, don ku wa’azantu.”



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 85

وَإِلَىٰ مَدۡيَنَ أَخَاهُمۡ شُعَيۡبٗاۚ قَالَ يَٰقَوۡمِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرُهُۥۖ قَدۡ جَآءَتۡكُم بَيِّنَةٞ مِّن رَّبِّكُمۡۖ فَأَوۡفُواْ ٱلۡكَيۡلَ وَٱلۡمِيزَانَ وَلَا تَبۡخَسُواْ ٱلنَّاسَ أَشۡيَآءَهُمۡ وَلَا تُفۡسِدُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ بَعۡدَ إِصۡلَٰحِهَاۚ ذَٰلِكُمۡ خَيۡرٞ لَّكُمۡ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ

Kuma (Mun) aika wa mutanen Madyana xan’uwansu Shu’aibu, ya ce: “Ya ku mutanena, ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi, haqiqa hujja ta zo muku daga Ubangijinku; don haka ku riqa cika mudu, kuma ku (kiyaye) ma’auni, kuma kada ku tauye wa mutane abubuwansu, kuma kada ku yi varna a bayan qasa bayan an gyara ta. Wannan shi ne mafi alheri a gare ku in kun kasance muminai



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 20

وَشَرَوۡهُ بِثَمَنِۭ بَخۡسٖ دَرَٰهِمَ مَعۡدُودَةٖ وَكَانُواْ فِيهِ مِنَ ٱلزَّـٰهِدِينَ

Suka kuma sayar da shi araha da ‘yan dirhamai qirgaggu, suka zamanto kuma suna masu tsantsami game da shi



Capítulo: Suratul Isra’i

Verso : 34

وَلَا تَقۡرَبُواْ مَالَ ٱلۡيَتِيمِ إِلَّا بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُ حَتَّىٰ يَبۡلُغَ أَشُدَّهُۥۚ وَأَوۡفُواْ بِٱلۡعَهۡدِۖ إِنَّ ٱلۡعَهۡدَ كَانَ مَسۡـُٔولٗا

Kuma kada ku kusanci dukiyar maraya sai dai ta (hanya) wadda take mafi kyau[1], har sai ya kawo qarfi. Kuma ku cika alqawari; lalle alqawari ya kasance abin tambaya ne (a lahira)


1- Watau ta hanyar yi masa kasuwanci da ita.


Capítulo: Suratul Isra’i

Verso : 35

وَأَوۡفُواْ ٱلۡكَيۡلَ إِذَا كِلۡتُمۡ وَزِنُواْ بِٱلۡقِسۡطَاسِ ٱلۡمُسۡتَقِيمِۚ ذَٰلِكَ خَيۡرٞ وَأَحۡسَنُ تَأۡوِيلٗا

Kuma ku cika mudu idan kuka yi awo, kuma ku auna nauyi da ma’auni na adalci. Wannan (shi ya fi) alheri ya kuma fi kyakkyawan qarshe



Capítulo: Suratul Mu’uminun

Verso : 8

وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِأَمَٰنَٰتِهِمۡ وَعَهۡدِهِمۡ رَٰعُونَ

Kuma waxanda suke masu kiyaye amanarsu da kuma alqawarinsu



Capítulo: Suratun Nur

Verso : 36

فِي بُيُوتٍ أَذِنَ ٱللَّهُ أَن تُرۡفَعَ وَيُذۡكَرَ فِيهَا ٱسۡمُهُۥ يُسَبِّحُ لَهُۥ فِيهَا بِٱلۡغُدُوِّ وَٱلۡأٓصَالِ

(Hasken) yana cikin wasu xakuna (watau masallatai) waxanda Allah Ya yi umarni a xaukaka, a kuma ambaci sunansa a cikinsu. (Wasu mazaje) suna tasbihi gare Shi a cikinsu safe da yamma



Capítulo: Suratun Nur

Verso : 37

رِجَالٞ لَّا تُلۡهِيهِمۡ تِجَٰرَةٞ وَلَا بَيۡعٌ عَن ذِكۡرِ ٱللَّهِ وَإِقَامِ ٱلصَّلَوٰةِ وَإِيتَآءِ ٱلزَّكَوٰةِ يَخَافُونَ يَوۡمٗا تَتَقَلَّبُ فِيهِ ٱلۡقُلُوبُ وَٱلۡأَبۡصَٰرُ

Wasu mazaje ne waxanda kasuwanci da saye da sayarwa ba ya shagaltar da su daga ambaton Allah da kuma tsai da salla da ba da zakka, suna jin tsoron ranar da zukata da idanuwa suke raurawa



Capítulo: Suratus Shu’ara

Verso : 182

وَزِنُواْ بِٱلۡقِسۡطَاسِ ٱلۡمُسۡتَقِيمِ

“Kuma ku riqa yin awon nauyi da ma’auni na adalci



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 39

وَمَآ ءَاتَيۡتُم مِّن رِّبٗا لِّيَرۡبُوَاْ فِيٓ أَمۡوَٰلِ ٱلنَّاسِ فَلَا يَرۡبُواْ عِندَ ٱللَّهِۖ وَمَآ ءَاتَيۡتُم مِّن زَكَوٰةٖ تُرِيدُونَ وَجۡهَ ٱللَّهِ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُضۡعِفُونَ

Kuma abin da kuka bayar na riba don ya qaru a cikin dukiyoyin mutane, to ba ya qaruwa a wurin Allah[1]; abin kuma da kuka bayar na zakka kuna masu nufin Fuskar Allah, to waxannan su ne masu ninninka (ladansu)


1- Da yawa daga cikin malamai sun fassara wannan gavar da cewa, ana nufin wanda zai bayar da kyauta yana nufin a mayar masa da fiye da abin da ya bayar, to ba shi da lada a wurin Allah.


Capítulo: Suratu Sad

Verso : 23

إِنَّ هَٰذَآ أَخِي لَهُۥ تِسۡعٞ وَتِسۡعُونَ نَعۡجَةٗ وَلِيَ نَعۡجَةٞ وَٰحِدَةٞ فَقَالَ أَكۡفِلۡنِيهَا وَعَزَّنِي فِي ٱلۡخِطَابِ

“Lalle wannan xan’uwana ne yana da awaki guda casa’in da tara, ni kuma ina da akuya guda xaya, sai ya ce: ‘Ka ba ni ita;’ ya kuma rinjaye ni game da maganar.”



Capítulo: Suratu Sad

Verso : 24

قَالَ لَقَدۡ ظَلَمَكَ بِسُؤَالِ نَعۡجَتِكَ إِلَىٰ نِعَاجِهِۦۖ وَإِنَّ كَثِيرٗا مِّنَ ٱلۡخُلَطَآءِ لَيَبۡغِي بَعۡضُهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٍ إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ وَقَلِيلٞ مَّا هُمۡۗ وَظَنَّ دَاوُۥدُ أَنَّمَا فَتَنَّـٰهُ فَٱسۡتَغۡفَرَ رَبَّهُۥ وَخَرَّۤ رَاكِعٗاۤ وَأَنَابَ۩

(Dawuda) Ya ce: “Haqiqa ya zalunce ka saboda neman haxe akuyarka cikin awakinsa; kuma lalle yawancin masu haxa dukiyarsu tabbas wasunsu suna zaluntar wasu, sai fa waxanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari, su kuwa kaxan ne qwarai. Sai kuma Dawuda ya tabbata cewa Mun jarraba shi ne, sai ya nemi gafarar Ubangijinsa, ya kuma faxi yana sujjada kuma ya koma (ga Allah)



Capítulo: Suratur Rahman

Verso : 9

وَأَقِيمُواْ ٱلۡوَزۡنَ بِٱلۡقِسۡطِ وَلَا تُخۡسِرُواْ ٱلۡمِيزَانَ

Kuma ku tabbatar da awo da adalci kada kuma ku tauye abin awo



Capítulo: Suratul Jumu’a

Verso : 9

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا نُودِيَ لِلصَّلَوٰةِ مِن يَوۡمِ ٱلۡجُمُعَةِ فَٱسۡعَوۡاْ إِلَىٰ ذِكۡرِ ٱللَّهِ وَذَرُواْ ٱلۡبَيۡعَۚ ذَٰلِكُمۡ خَيۡرٞ لَّكُمۡ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ

Ya ku waxanda suka yi imani, idan aka kira salla ranar Juma’a[1] sai ku tafi zuwa zikirin Allah, kuma ku bar ciniki. Wannan (shi) ya fi muku alheri, idan kun kasance kuna sane (da haka)


1- Watau kiran salla bayan liman ya hau kan mimbari. Wajibi a lokacin duk wani Musulmi ya bar duk wata sabga ta saye da sayarwa.


Capítulo: Suratul Ma’arij

Verso : 32

وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِأَمَٰنَٰتِهِمۡ وَعَهۡدِهِمۡ رَٰعُونَ

Waxanda kuma suke kiyaye amanoninsu da alqawuransu