Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 251

فَهَزَمُوهُم بِإِذۡنِ ٱللَّهِ وَقَتَلَ دَاوُۥدُ جَالُوتَ وَءَاتَىٰهُ ٱللَّهُ ٱلۡمُلۡكَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَعَلَّمَهُۥ مِمَّا يَشَآءُۗ وَلَوۡلَا دَفۡعُ ٱللَّهِ ٱلنَّاسَ بَعۡضَهُم بِبَعۡضٖ لَّفَسَدَتِ ٱلۡأَرۡضُ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ ذُو فَضۡلٍ عَلَى ٱلۡعَٰلَمِينَ

Sai suka murqushe su da izinin Allah, kuma Dawudu ya kashe Jalutu, sai Allah Ya ba shi mulki da hikima, kuma Ya sanar da shi irin abin da Ya ga dama. Ba don yadda Allah Yake kare wani sashin mutane da wani sashi ba, to lalle da qasa ta lalace, sai dai kuma Allah Ma’abocin falala ne ga talikai



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 163

۞إِنَّآ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ كَمَآ أَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ نُوحٖ وَٱلنَّبِيِّـۧنَ مِنۢ بَعۡدِهِۦۚ وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰٓ إِبۡرَٰهِيمَ وَإِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ وَٱلۡأَسۡبَاطِ وَعِيسَىٰ وَأَيُّوبَ وَيُونُسَ وَهَٰرُونَ وَسُلَيۡمَٰنَۚ وَءَاتَيۡنَا دَاوُۥدَ زَبُورٗا

Lalle Mun yi maka wahayi irin wahayin da Muka yi wa Nuhu da kuma annabawan da suka biyo bayansa, kuma Mun yi wahayi ga Ibrahimu da Isma’ila da Ishaqa da Ya’aqubu da kuma jikokin (Ya’aqubu) da Isa da Ayyuba da Yunusa da Haruna da Sulaimanu; kuma Muka bai wa Dawuda littafin Zabura



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 78

لُعِنَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۢ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ عَلَىٰ لِسَانِ دَاوُۥدَ وَعِيسَى ٱبۡنِ مَرۡيَمَۚ ذَٰلِكَ بِمَا عَصَواْ وَّكَانُواْ يَعۡتَدُونَ

An la’anci waxanda suka kafirta daga cikin Bani-Isra’ila a bisa harshen Dawuda da kuma Isa xan Maryamu. Hakan kuwa saboda abin da suka riqa yi ne na savo, kuma sun kasance suna qetare iyaka



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 84

وَوَهَبۡنَا لَهُۥٓ إِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَۚ كُلًّا هَدَيۡنَاۚ وَنُوحًا هَدَيۡنَا مِن قَبۡلُۖ وَمِن ذُرِّيَّتِهِۦ دَاوُۥدَ وَسُلَيۡمَٰنَ وَأَيُّوبَ وَيُوسُفَ وَمُوسَىٰ وَهَٰرُونَۚ وَكَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Kuma Muka ba shi Ishaqa da Ya’aqubu. Kowanne daga cikinsu Mun shiryar da shi, kuma Mun shiryar da Nuhu tun gabaninsu. Kuma daga cikin zurriyarsa akwai Dawudu da Sulaimanu da Ayyuba da Yusufu da Musa da Haruna. Kuma kamar haka ne Muke saka wa masu kyautata (ayyukansu)



Capítulo: Suratul Isra’i

Verso : 55

وَرَبُّكَ أَعۡلَمُ بِمَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۗ وَلَقَدۡ فَضَّلۡنَا بَعۡضَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ عَلَىٰ بَعۡضٖۖ وَءَاتَيۡنَا دَاوُۥدَ زَبُورٗا

Ubangijinka kuma (Shi ne) Mafi sanin abin da yake cikin sammai da qasa. Haqiqa kuma Mun fifita wasu annabawa a kan wasu; Muka kuma bai wa Dawuda (littafin) Zabura



Capítulo: Suratul Anbiya

Verso : 78

وَدَاوُۥدَ وَسُلَيۡمَٰنَ إِذۡ يَحۡكُمَانِ فِي ٱلۡحَرۡثِ إِذۡ نَفَشَتۡ فِيهِ غَنَمُ ٱلۡقَوۡمِ وَكُنَّا لِحُكۡمِهِمۡ شَٰهِدِينَ

(Ka tuna) kuma Dawuda da Sulaimanu lokacin da suke yin hukunci a kan amfanin gona lokacin da dabbobin wasu mutane suka cinye shi da daddare, Mun kuwa zamanto Muna sane da irin hukuncin nasu



Capítulo: Suratul Anbiya

Verso : 79

فَفَهَّمۡنَٰهَا سُلَيۡمَٰنَۚ وَكُلًّا ءَاتَيۡنَا حُكۡمٗا وَعِلۡمٗاۚ وَسَخَّرۡنَا مَعَ دَاوُۥدَ ٱلۡجِبَالَ يُسَبِّحۡنَ وَٱلطَّيۡرَۚ وَكُنَّا فَٰعِلِينَ

Sai Muka ganar da Sulaimanu shi (hukuncin)[1]. Kuma dukkaninsu Mun ba su annabta da ilimi. Muka kuma hore wa Dawuda duwatsu da tsuntsaye, suna tasbihi tare da shi. Mun kuwa kasance Masu aikata (haka)


1- Da farko Annabi Dawud () ya yi hukunci da cewa, manomin zai karvi dabbobin a madadin amfanin gonarsa da suka cinye. Amma sai Sulaiman () ya sake hukunci da cewa, manomin zai riqe dabbobin yana amfanuwa da su har zuwa lokacin da masu dabbobin za su sake noma musu gonarsa ta dawo kamar farko sai su karvi dabbobinsu.


Capítulo: Suratul Anbiya

Verso : 80

وَعَلَّمۡنَٰهُ صَنۡعَةَ لَبُوسٖ لَّكُمۡ لِتُحۡصِنَكُم مِّنۢ بَأۡسِكُمۡۖ فَهَلۡ أَنتُمۡ شَٰكِرُونَ

Muka kuma koya masa yadda ake qera silke dominku don ya kare ku lokacin yaqinku; to shin ku masu godiya ne?



Capítulo: Suratu Saba’i

Verso : 10

۞وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا دَاوُۥدَ مِنَّا فَضۡلٗاۖ يَٰجِبَالُ أَوِّبِي مَعَهُۥ وَٱلطَّيۡرَۖ وَأَلَنَّا لَهُ ٱلۡحَدِيدَ

Kuma haqiqa Mun bai wa Dawuda falala daga gare Mu; cewa: “Ya ku duwatsu ku riqa amsa tasbihi tare da shi,” da kuma tsuntsaye; Muka kuma tausasa masa qarfe



Capítulo: Suratu Saba’i

Verso : 11

أَنِ ٱعۡمَلۡ سَٰبِغَٰتٖ وَقَدِّرۡ فِي ٱلسَّرۡدِۖ وَٱعۡمَلُواْ صَٰلِحًاۖ إِنِّي بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ

(Muka ce da shi): “Ka riqa yin cikakken silke, kuma ka kintata wajen yin saqar; kuma (kai Dawuda da iyalinka) ku yi ayyuka nagari; lalle Ni Mai ganin abin da kuke aikatawa ne.”



Capítulo: Suratu Sad

Verso : 17

ٱصۡبِرۡ عَلَىٰ مَا يَقُولُونَ وَٱذۡكُرۡ عَبۡدَنَا دَاوُۥدَ ذَا ٱلۡأَيۡدِۖ إِنَّهُۥٓ أَوَّابٌ

(Sai Allah Ya ce): “Ka yi haquri a kan abin da suke faxa, ka kuma tuna bawanmu Dawuda ma’abocin qarfi; lalle shi ya kasance mai yawan komawa ne (ga Allah)



Capítulo: Suratu Sad

Verso : 18

إِنَّا سَخَّرۡنَا ٱلۡجِبَالَ مَعَهُۥ يُسَبِّحۡنَ بِٱلۡعَشِيِّ وَٱلۡإِشۡرَاقِ

Lalle Mu Mun hore masa duwatsu suna yin tasbihi tare da shi a yamma da hantsi



Capítulo: Suratu Sad

Verso : 19

وَٱلطَّيۡرَ مَحۡشُورَةٗۖ كُلّٞ لَّهُۥٓ أَوَّابٞ

Da kuma tsuntsaye a tattare; dukkaninsu suna biyayya a gare shi



Capítulo: Suratu Sad

Verso : 20

وَشَدَدۡنَا مُلۡكَهُۥ وَءَاتَيۡنَٰهُ ٱلۡحِكۡمَةَ وَفَصۡلَ ٱلۡخِطَابِ

Kuma Muka qarfafa mulkinsa, Muka kuma ba shi hikima da bayyana hukunce-hukunce (tsakanin masu husuma)



Capítulo: Suratu Sad

Verso : 21

۞وَهَلۡ أَتَىٰكَ نَبَؤُاْ ٱلۡخَصۡمِ إِذۡ تَسَوَّرُواْ ٱلۡمِحۡرَابَ

Shin labarin abokan husuma ya zo maka, yayin da suka haura wurin ibada?



Capítulo: Suratu Sad

Verso : 22

إِذۡ دَخَلُواْ عَلَىٰ دَاوُۥدَ فَفَزِعَ مِنۡهُمۡۖ قَالُواْ لَا تَخَفۡۖ خَصۡمَانِ بَغَىٰ بَعۡضُنَا عَلَىٰ بَعۡضٖ فَٱحۡكُم بَيۡنَنَا بِٱلۡحَقِّ وَلَا تُشۡطِطۡ وَٱهۡدِنَآ إِلَىٰ سَوَآءِ ٱلصِّرَٰطِ

Yayin da suka shiga wurin Dawuda sai ya tsorata da su, suka ce: “Kada ka tsorata, (mu biyun nan) masu husuma ne, xayanmu ya zalunci xaya, sai ka yi hukunci a tsakaninmu da gaskiya, kada kuma ka yi zalunci, kuma ka shiryar da mu hanya madaidaiciya



Capítulo: Suratu Sad

Verso : 23

إِنَّ هَٰذَآ أَخِي لَهُۥ تِسۡعٞ وَتِسۡعُونَ نَعۡجَةٗ وَلِيَ نَعۡجَةٞ وَٰحِدَةٞ فَقَالَ أَكۡفِلۡنِيهَا وَعَزَّنِي فِي ٱلۡخِطَابِ

“Lalle wannan xan’uwana ne yana da awaki guda casa’in da tara, ni kuma ina da akuya guda xaya, sai ya ce: ‘Ka ba ni ita;’ ya kuma rinjaye ni game da maganar.”



Capítulo: Suratu Sad

Verso : 24

قَالَ لَقَدۡ ظَلَمَكَ بِسُؤَالِ نَعۡجَتِكَ إِلَىٰ نِعَاجِهِۦۖ وَإِنَّ كَثِيرٗا مِّنَ ٱلۡخُلَطَآءِ لَيَبۡغِي بَعۡضُهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٍ إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ وَقَلِيلٞ مَّا هُمۡۗ وَظَنَّ دَاوُۥدُ أَنَّمَا فَتَنَّـٰهُ فَٱسۡتَغۡفَرَ رَبَّهُۥ وَخَرَّۤ رَاكِعٗاۤ وَأَنَابَ۩

(Dawuda) Ya ce: “Haqiqa ya zalunce ka saboda neman haxe akuyarka cikin awakinsa; kuma lalle yawancin masu haxa dukiyarsu tabbas wasunsu suna zaluntar wasu, sai fa waxanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari, su kuwa kaxan ne qwarai. Sai kuma Dawuda ya tabbata cewa Mun jarraba shi ne, sai ya nemi gafarar Ubangijinsa, ya kuma faxi yana sujjada kuma ya koma (ga Allah)



Capítulo: Suratu Sad

Verso : 25

فَغَفَرۡنَا لَهُۥ ذَٰلِكَۖ وَإِنَّ لَهُۥ عِندَنَا لَزُلۡفَىٰ وَحُسۡنَ مَـَٔابٖ

Sai Muka gafarta masa wannan; lalle kuma yana da kusanci da Mu da kuma kyakkyawar makoma



Capítulo: Suratu Sad

Verso : 26

يَٰدَاوُۥدُ إِنَّا جَعَلۡنَٰكَ خَلِيفَةٗ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَٱحۡكُم بَيۡنَ ٱلنَّاسِ بِٱلۡحَقِّ وَلَا تَتَّبِعِ ٱلۡهَوَىٰ فَيُضِلَّكَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ يَضِلُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ لَهُمۡ عَذَابٞ شَدِيدُۢ بِمَا نَسُواْ يَوۡمَ ٱلۡحِسَابِ

Ya Dawuda, lalle Mun sanya ka halifa a bayan qasa, sai ka yi hukunci a tsakanin mutane da gaskiya, kada ka bi son zuciya sai ya vatar da kai daga hanyar Allah. Lalle waxanda suke vacewa daga hanyar Allah suna da (sakamakon) azaba mai tsanani saboda mantawar da suka yi da ranar hisabi



Capítulo: Suratu Sad

Verso : 30

وَوَهَبۡنَا لِدَاوُۥدَ سُلَيۡمَٰنَۚ نِعۡمَ ٱلۡعَبۡدُ إِنَّهُۥٓ أَوَّابٌ

Muka kuma yi wa Dawuda baiwar (xa) Sulaimanu. Madalla da wannan bawan; lalle shi mai yawan komawa ne (ga Allah)