Capítulo: Suratul Furqan

Verso : 29

لَّقَدۡ أَضَلَّنِي عَنِ ٱلذِّكۡرِ بَعۡدَ إِذۡ جَآءَنِيۗ وَكَانَ ٱلشَّيۡطَٰنُ لِلۡإِنسَٰنِ خَذُولٗا

“Haqiqa ya vatar da ni daga bin Alqur’ani, bayan ya zo mini.” Shaixan kuwa ya kasance mai tavar da mutum ne



Capítulo: Suratul Furqan

Verso : 30

وَقَالَ ٱلرَّسُولُ يَٰرَبِّ إِنَّ قَوۡمِي ٱتَّخَذُواْ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانَ مَهۡجُورٗا

Manzo kuma ya ce: “Ya Ubangijina, lalle mutanena sun riqi wannan Alqur’ani abin qaurace wa[1].”


1- Watau ta hanyar guje wa sauraron sa da rashin karanta shi da aiki da koyarwarsa.


Capítulo: Suratun Namli

Verso : 87

وَيَوۡمَ يُنفَخُ فِي ٱلصُّورِ فَفَزِعَ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَن فِي ٱلۡأَرۡضِ إِلَّا مَن شَآءَ ٱللَّهُۚ وَكُلٌّ أَتَوۡهُ دَٰخِرِينَ

(Ka tuna) kuma ranar da za a busa qaho sai duk mahaluqin da yake cikin sammai da qasa ya firgita, sai dai wanda Allah Ya toge. Kuma gaba xayansu za su zo masa suna masu miqa wuya



Capítulo: Suratun Namli

Verso : 88

وَتَرَى ٱلۡجِبَالَ تَحۡسَبُهَا جَامِدَةٗ وَهِيَ تَمُرُّ مَرَّ ٱلسَّحَابِۚ صُنۡعَ ٱللَّهِ ٱلَّذِيٓ أَتۡقَنَ كُلَّ شَيۡءٍۚ إِنَّهُۥ خَبِيرُۢ بِمَا تَفۡعَلُونَ

Kuma za ka ga duwatsu ka zaci a tsaye suke cak, alhali kuwa su suna tafiya ne irin tafiyar gizagizai. Aikin Allah kenan wanda Ya kyautata halittar kowane irin abu. Lalle Shi Masanin abin da kuke aikatawa ne



Capítulo: Suratun Namli

Verso : 89

مَن جَآءَ بِٱلۡحَسَنَةِ فَلَهُۥ خَيۡرٞ مِّنۡهَا وَهُم مِّن فَزَعٖ يَوۡمَئِذٍ ءَامِنُونَ

Duk waxanda suka zo da kyakkyawan (aiki), to suna da (lada) fiye da shi, kuma su amintattu ne daga firgitar wannan ranar



Capítulo: Suratun Namli

Verso : 90

وَمَن جَآءَ بِٱلسَّيِّئَةِ فَكُبَّتۡ وُجُوهُهُمۡ فِي ٱلنَّارِ هَلۡ تُجۡزَوۡنَ إِلَّا مَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

Waxanda kuwa suka zo da mummunan (aiki), to an kifar da fuskokinsu cikin wuta, to ba za a saka muku ba sai da irin abin da kuka zamanto kuna aikatawa



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 12

وَيَوۡمَ تَقُومُ ٱلسَّاعَةُ يُبۡلِسُ ٱلۡمُجۡرِمُونَ

Kuma ranar da alqiyama za ta tashi, a wannan ranar ne masu manyan laifuka (kafirai) za su yanke qauna daga rahama



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 13

وَلَمۡ يَكُن لَّهُم مِّن شُرَكَآئِهِمۡ شُفَعَـٰٓؤُاْ وَكَانُواْ بِشُرَكَآئِهِمۡ كَٰفِرِينَ

Daga abokan tarayyar tasu kuwa ba su da wasu masu ceton su, za su ma kasance masu kafirce wa abokan tarayyar tasu



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 14

وَيَوۡمَ تَقُومُ ٱلسَّاعَةُ يَوۡمَئِذٖ يَتَفَرَّقُونَ

Kuma ranar da alqiyama za ta tashi, a wannan ranar ne (mutane) za su rarrabu[1]


1- Watau qungiya biyu, qungiyar muminai masu shiga Aljanna da ta kafirai masu shiga wuta.


Capítulo: Suratur Rum

Verso : 15

فَأَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ فَهُمۡ فِي رَوۡضَةٖ يُحۡبَرُونَ

To amma waxanda suka yi imani suka kuma yi aiki nagari, to su kam suna cikin dausayin (Aljanna) ana faranta musu rai



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 16

وَأَمَّا ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَكَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَلِقَآيِٕ ٱلۡأٓخِرَةِ فَأُوْلَـٰٓئِكَ فِي ٱلۡعَذَابِ مُحۡضَرُونَ

Amma kuma waxanda suka kafirta suka kuma qaryata ayoyinmu da haxuwa da ranar lahira, to waxannan za a halartar da su cikin azaba



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 56

وَقَالَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ وَٱلۡإِيمَٰنَ لَقَدۡ لَبِثۡتُمۡ فِي كِتَٰبِ ٱللَّهِ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡبَعۡثِۖ فَهَٰذَا يَوۡمُ ٱلۡبَعۡثِ وَلَٰكِنَّكُمۡ كُنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ

Waxanda kuwa aka bai wa ilimi da imani sai suka ce: “Haqiqa kun zauna ne gwargwadon yadda Allah Ya rubuta muku a littafinsa har zuwa ranar tashi; to wannan kuma ita ce ranar tashin, sai dai kuma ku kun kasance ba ku san (haka) ba.”



Capítulo: Suratu Luqman

Verso : 33

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱتَّقُواْ رَبَّكُمۡ وَٱخۡشَوۡاْ يَوۡمٗا لَّا يَجۡزِي وَالِدٌ عَن وَلَدِهِۦ وَلَا مَوۡلُودٌ هُوَ جَازٍ عَن وَالِدِهِۦ شَيۡـًٔاۚ إِنَّ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٞۖ فَلَا تَغُرَّنَّكُمُ ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَا وَلَا يَغُرَّنَّكُم بِٱللَّهِ ٱلۡغَرُورُ

Ya ku mutane, ku kiyaye dokokin Ubangijinku, kuma ku ji tsoron ranar da mahaifi ba zai amfana wa xansa komai ba, kuma xan shi ma ba zai amfana wa mahaifinsa komai ba. Lalle alqawarin Allah gaskiya ne; to kada rayuwar duniya ta ruxe ku, kuma (Shaixan) mai ruxarwa kada ya ruxe ku game da Allah



Capítulo: Suratus Sajda

Verso : 5

يُدَبِّرُ ٱلۡأَمۡرَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ إِلَى ٱلۡأَرۡضِ ثُمَّ يَعۡرُجُ إِلَيۡهِ فِي يَوۡمٖ كَانَ مِقۡدَارُهُۥٓ أَلۡفَ سَنَةٖ مِّمَّا تَعُدُّونَ

Yana shirya al’amari daga sama zuwa qasa sannan (al’amarin) ya hau zuwa gare Shi a cikin wani yini da gwargwadon (tsawonsa) yake shekara dubu ne daga abin da kuke qirgawa



Capítulo: Suratus Sajda

Verso : 29

قُلۡ يَوۡمَ ٱلۡفَتۡحِ لَا يَنفَعُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِيمَٰنُهُمۡ وَلَا هُمۡ يُنظَرُونَ

Ka ce: “Ranar hukuncin, waxanda suka kafirce, imaninsu ba zai amfane su ba, kuma ba ma za a saurara musu ba.”



Capítulo: Suratu Yasin

Verso : 51

وَنُفِخَ فِي ٱلصُّورِ فَإِذَا هُم مِّنَ ٱلۡأَجۡدَاثِ إِلَىٰ رَبِّهِمۡ يَنسِلُونَ

Aka kuma busa qaho[1], sai ga su suna fitowa daga qaburbura zuwa wurin Ubangijinsu


1- Watau busa ta biyu domin tashi.


Capítulo: Suratu Yasin

Verso : 52

قَالُواْ يَٰوَيۡلَنَا مَنۢ بَعَثَنَا مِن مَّرۡقَدِنَاۜۗ هَٰذَا مَا وَعَدَ ٱلرَّحۡمَٰنُ وَصَدَقَ ٱلۡمُرۡسَلُونَ

Suka ce: “Kaiconmu, wane ne ya tashe mu daga makwancinmu?” (Sai a ce da su): “Ai wannnan shi ne abin da (Allah) Mai rahama Ya yi alqawarinsa, manzanni kuma sun yi gaskiya.”



Capítulo: Suratu Yasin

Verso : 53

إِن كَانَتۡ إِلَّا صَيۡحَةٗ وَٰحِدَةٗ فَإِذَا هُمۡ جَمِيعٞ لَّدَيۡنَا مُحۡضَرُونَ

Ba abin da zai kasance sai tsawa guda xaya, sai ga su gaba xaya an tattaro su gabanmu



Capítulo: Suratu Yasin

Verso : 54

فَٱلۡيَوۡمَ لَا تُظۡلَمُ نَفۡسٞ شَيۡـٔٗا وَلَا تُجۡزَوۡنَ إِلَّا مَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

To a yau fa ba za a zalunci wani rai da komai ba, ba kuma za a saka muku ba sai da irin abin da kuka zamanto kuna aikatawa



Capítulo: Suratuz Zumar

Verso : 31

ثُمَّ إِنَّكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ عِندَ رَبِّكُمۡ تَخۡتَصِمُونَ

Sannan kuma lalle ku xin nan a ranar alqiyama a wurin Ubangijinku za ku yi husuma



Capítulo: Suratuz Zumar

Verso : 60

وَيَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ تَرَى ٱلَّذِينَ كَذَبُواْ عَلَى ٱللَّهِ وُجُوهُهُم مُّسۡوَدَّةٌۚ أَلَيۡسَ فِي جَهَنَّمَ مَثۡوٗى لِّلۡمُتَكَبِّرِينَ

A ranar alqiyama kuwa za ka ga waxanda suka yi wa Allah qarya fuskokinsu baqi qirin. Yanzu a cikin wutar Jahannama ashe babu mazaunar masu girman kai?



Capítulo: Suratuz Zumar

Verso : 61

وَيُنَجِّي ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْ بِمَفَازَتِهِمۡ لَا يَمَسُّهُمُ ٱلسُّوٓءُ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ

Allah kuma zai tserar da waxanda suka yi taqawa da ayyukansu, wani mummunan abu ba zai shafe su ba, kuma ba za su yi baqin ciki ba



Capítulo: Suratuz Zumar

Verso : 67

وَمَا قَدَرُواْ ٱللَّهَ حَقَّ قَدۡرِهِۦ وَٱلۡأَرۡضُ جَمِيعٗا قَبۡضَتُهُۥ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَٱلسَّمَٰوَٰتُ مَطۡوِيَّـٰتُۢ بِيَمِينِهِۦۚ سُبۡحَٰنَهُۥ وَتَعَٰلَىٰ عَمَّا يُشۡرِكُونَ

Ba su kuma girmama Allah ba kamar yadda Ya cancanta a girmama Shi, alhali qasa ga baki xayanta tana cikin Damqarsa ranar alqiyama, sammai kuma suna nannaxe a Hannunsa na dama. Tsarki ya tabbata a gare Shi, Ya kuma xaukaka game da abin da suke yin shirka (da shi)



Capítulo: Suratuz Zumar

Verso : 68

وَنُفِخَ فِي ٱلصُّورِ فَصَعِقَ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَن فِي ٱلۡأَرۡضِ إِلَّا مَن شَآءَ ٱللَّهُۖ ثُمَّ نُفِخَ فِيهِ أُخۡرَىٰ فَإِذَا هُمۡ قِيَامٞ يَنظُرُونَ

Aka kuma busa qaho, sai duk abin da yake cikin sammai da qasa ya halaka sai wanda Allah Ya ga dama; sannan aka sake yin wata busar, sai ga su a tsaye suna jiran tsammani



Capítulo: Suratuz Zumar

Verso : 69

وَأَشۡرَقَتِ ٱلۡأَرۡضُ بِنُورِ رَبِّهَا وَوُضِعَ ٱلۡكِتَٰبُ وَجِاْيٓءَ بِٱلنَّبِيِّـۧنَ وَٱلشُّهَدَآءِ وَقُضِيَ بَيۡنَهُم بِٱلۡحَقِّ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ

Qasa kuma ta yi haske da hasken Ubangijinta, aka kuma ajiye takardu (na ayyuka), kuma aka zo da annabawa da masu shaida, kuma aka yi hukunci a tsakaninsu da gaskiya, ba kuma za a zalunce su ba



Capítulo: Suratuz Zumar

Verso : 70

وَوُفِّيَتۡ كُلُّ نَفۡسٖ مَّا عَمِلَتۡ وَهُوَ أَعۡلَمُ بِمَا يَفۡعَلُونَ

Aka kuma yi wa kowane rai cikakken sakamakon abin da ya aikata, Shi ko (Allah) Yana sane da abin da suke aikatawa



Capítulo: Suratuz Zumar

Verso : 71

وَسِيقَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِلَىٰ جَهَنَّمَ زُمَرًاۖ حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءُوهَا فُتِحَتۡ أَبۡوَٰبُهَا وَقَالَ لَهُمۡ خَزَنَتُهَآ أَلَمۡ يَأۡتِكُمۡ رُسُلٞ مِّنكُمۡ يَتۡلُونَ عَلَيۡكُمۡ ءَايَٰتِ رَبِّكُمۡ وَيُنذِرُونَكُمۡ لِقَآءَ يَوۡمِكُمۡ هَٰذَاۚ قَالُواْ بَلَىٰ وَلَٰكِنۡ حَقَّتۡ كَلِمَةُ ٱلۡعَذَابِ عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ

Aka kuma ingiza qeyar waxanda suka kafirta zuwa (wutar) Jahannama qungiya-qungiya; har yayin da suka zo wurinta sai aka buxe qofofinta, masu tsaronta suka ce (da su): “Yanzu manzanni daga cikinku ba su zo muku ba ne suna karanta muku ayoyin Ubangijinku, suna kuma gargaxin ku game da haxuwa da wannan ranar taku?” Sai suka ce: “Haka ne, (sun zo mana),” sai dai kuma kalmar azaba ta tabbata a kan kafirai.”



Capítulo: Suratuz Zumar

Verso : 72

قِيلَ ٱدۡخُلُوٓاْ أَبۡوَٰبَ جَهَنَّمَ خَٰلِدِينَ فِيهَاۖ فَبِئۡسَ مَثۡوَى ٱلۡمُتَكَبِّرِينَ

Aka ce: “Ku shiga qofofin Jahannama, kuna masu dawwama a cikinta;” to makomar masu girman kai ta munana



Capítulo: Suratuz Zumar

Verso : 73

وَسِيقَ ٱلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْ رَبَّهُمۡ إِلَى ٱلۡجَنَّةِ زُمَرًاۖ حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءُوهَا وَفُتِحَتۡ أَبۡوَٰبُهَا وَقَالَ لَهُمۡ خَزَنَتُهَا سَلَٰمٌ عَلَيۡكُمۡ طِبۡتُمۡ فَٱدۡخُلُوهَا خَٰلِدِينَ

Aka kuma raka waxanda suka kiyaye dokokin Ubangijinsu zuwa Aljanna qungiya-qungiya; har yayin da suka zo wurinta, alhali an bubbuxe qofofinta, kuma masu tsaronta suka ce (da su): “Aminci ya tabbata a gare ku, kun kyautata (ayyukanku), sai ku shige ta kuna masu dawwama.”



Capítulo: Suratuz Zumar

Verso : 74

وَقَالُواْ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِي صَدَقَنَا وَعۡدَهُۥ وَأَوۡرَثَنَا ٱلۡأَرۡضَ نَتَبَوَّأُ مِنَ ٱلۡجَنَّةِ حَيۡثُ نَشَآءُۖ فَنِعۡمَ أَجۡرُ ٱلۡعَٰمِلِينَ

Suka ce: “Mun gode wa Allah Wanda Ya tabbatar mana da alqawarinsa, Ya kuma gadar mana da qasa muna sauka a Aljanna a duk inda muka ga dama; to madalla da sakamakon masu aiki!”