Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 97

إِنَّ ٱلَّذِينَ تَوَفَّىٰهُمُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ ظَالِمِيٓ أَنفُسِهِمۡ قَالُواْ فِيمَ كُنتُمۡۖ قَالُواْ كُنَّا مُسۡتَضۡعَفِينَ فِي ٱلۡأَرۡضِۚ قَالُوٓاْ أَلَمۡ تَكُنۡ أَرۡضُ ٱللَّهِ وَٰسِعَةٗ فَتُهَاجِرُواْ فِيهَاۚ فَأُوْلَـٰٓئِكَ مَأۡوَىٰهُمۡ جَهَنَّمُۖ وَسَآءَتۡ مَصِيرًا

Lalle waxanda mala’iku suke karvar rayukansu suna masu zaluntar kawunansu[1], (mala’ikun) za su ce (da su): “Cikin wane hali kuka kasance?” Sai su ce: “Mu mun kasance masu rauni a bayan qasa.” Sai su ce: “Ashe qasar Allah ba mai yalwa ba ce, ta yadda za ku sami damar yin hijira a cikinta?” To waxannan, makomarsu ita ce wutar Jahannama, kuma wannan makoma ta munana


1- Watau sun qi yin hijira zuwa cikin ‘yan’uwansu Musulmi, sun ci gaba da zama a qasar kafirci, tare da cewa suna da ikon yin hijirar.


Capítulo: Suratul An’am

Verso : 61

وَهُوَ ٱلۡقَاهِرُ فَوۡقَ عِبَادِهِۦۖ وَيُرۡسِلُ عَلَيۡكُمۡ حَفَظَةً حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءَ أَحَدَكُمُ ٱلۡمَوۡتُ تَوَفَّتۡهُ رُسُلُنَا وَهُمۡ لَا يُفَرِّطُونَ

“Kuma Shi ne wanda Yake da iko a kan bayinsa, kuma Yana aiko muku masu tsaro, har zuwa lokacin da mutuwa za ta zo wa xayanku, sai manzanninmu su karvi ransa, kuma su ba sa yin sakaci



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 93

وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا أَوۡ قَالَ أُوحِيَ إِلَيَّ وَلَمۡ يُوحَ إِلَيۡهِ شَيۡءٞ وَمَن قَالَ سَأُنزِلُ مِثۡلَ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُۗ وَلَوۡ تَرَىٰٓ إِذِ ٱلظَّـٰلِمُونَ فِي غَمَرَٰتِ ٱلۡمَوۡتِ وَٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ بَاسِطُوٓاْ أَيۡدِيهِمۡ أَخۡرِجُوٓاْ أَنفُسَكُمُۖ ٱلۡيَوۡمَ تُجۡزَوۡنَ عَذَابَ ٱلۡهُونِ بِمَا كُنتُمۡ تَقُولُونَ عَلَى ٱللَّهِ غَيۡرَ ٱلۡحَقِّ وَكُنتُمۡ عَنۡ ءَايَٰتِهِۦ تَسۡتَكۡبِرُونَ

Kuma wane ne ya fi zalunci kamar wanda ya qagi qarya ya jingina wa Allah, ko kuma ya ce: “An yiwo mini wahayi,” alhalin kuma ba a yi masa wahayin komai ba, da kuma wanda ya ce: “Zan saukar da irin abin da Allah Ya saukar?” Kuma da za ka ga lokacin da kafirai suke cikin magagin mutuwa, mala’iku kuma suna miqa hannayensu suna cewa: “Ku fito da rayukanku (da kanku), a yau ne za a saka muku da azabar wulaqanci, saboda irin abin da kuke faxa game da Allah wanda ba gaskiya ba, kuma kun kasance kuna girman kai game da ayoyinsa.”



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 37

فَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا أَوۡ كَذَّبَ بِـَٔايَٰتِهِۦٓۚ أُوْلَـٰٓئِكَ يَنَالُهُمۡ نَصِيبُهُم مِّنَ ٱلۡكِتَٰبِۖ حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءَتۡهُمۡ رُسُلُنَا يَتَوَفَّوۡنَهُمۡ قَالُوٓاْ أَيۡنَ مَا كُنتُمۡ تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِۖ قَالُواْ ضَلُّواْ عَنَّا وَشَهِدُواْ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِمۡ أَنَّهُمۡ كَانُواْ كَٰفِرِينَ

To wa ya fi wanda ya yi wa Allah qarya zalunci, ko ya qaryata ayoyinsa? Waxannan rabonsu da aka rubuta a cikin littafi zai same su; har ya zuwa lokacin da manzannimu za su zo su karvi ransu, sai su ce: “Ina waxanda kuka kasance kuna kira ba Allah ba?” Sai su ce: “Sun vace mana.” Kuma za su ba da shaida a kansu cewa, lalle su sun kasance kafirai



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 50

وَلَوۡ تَرَىٰٓ إِذۡ يَتَوَفَّى ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ يَضۡرِبُونَ وُجُوهَهُمۡ وَأَدۡبَٰرَهُمۡ وَذُوقُواْ عَذَابَ ٱلۡحَرِيقِ

Kuma da za ka ga lokacin da mala’iku suke xaukan ran waxanda suka kafirta, suna dukan fuskokinsu da kuma bayansu, suna kuma (cewa da su): “Ku xanxani azabar quna.”



Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 28

ٱلَّذِينَ تَتَوَفَّىٰهُمُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ ظَالِمِيٓ أَنفُسِهِمۡۖ فَأَلۡقَوُاْ ٱلسَّلَمَ مَا كُنَّا نَعۡمَلُ مِن سُوٓءِۭۚ بَلَىٰٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمُۢ بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

Waxanda mala’iku suke karvar ransu suna masu zaluntar kawunansu; sai suka ba da kai (suna cewa,): “Ba mu kasance muna yin wani mummunan aiki ba.” A’a, ba haka ba ne, lalle Allah Masanin abin da kuka zamanto kuna aikatawa ne



Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 32

ٱلَّذِينَ تَتَوَفَّىٰهُمُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ طَيِّبِينَ يَقُولُونَ سَلَٰمٌ عَلَيۡكُمُ ٱدۡخُلُواْ ٱلۡجَنَّةَ بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

Waxanda mala’iku suke xaukar ransu suna tsarkaka, suna cewa: “Aminci ya tabbata a gare ku, ku shiga Aljanna saboda abin da kuka zamanto kuna aikatawa (a duniya)



Capítulo: Suratus Sajda

Verso : 11

۞قُلۡ يَتَوَفَّىٰكُم مَّلَكُ ٱلۡمَوۡتِ ٱلَّذِي وُكِّلَ بِكُمۡ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّكُمۡ تُرۡجَعُونَ

Ka ce (da su): “Mala’ikan mutuwa ne wanda aka wakilta muku zai karvi ranku sannan kuma ga Ubangijinku za a komar da ku



Capítulo: Suratu Muhammad

Verso : 27

فَكَيۡفَ إِذَا تَوَفَّتۡهُمُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ يَضۡرِبُونَ وُجُوهَهُمۡ وَأَدۡبَٰرَهُمۡ

To yaya za su zama lokacin da mala’iku za su karvi rayukansu suna dukan fuskokinsu da bayansu?