Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 43

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَقۡرَبُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَأَنتُمۡ سُكَٰرَىٰ حَتَّىٰ تَعۡلَمُواْ مَا تَقُولُونَ وَلَا جُنُبًا إِلَّا عَابِرِي سَبِيلٍ حَتَّىٰ تَغۡتَسِلُواْۚ وَإِن كُنتُم مَّرۡضَىٰٓ أَوۡ عَلَىٰ سَفَرٍ أَوۡ جَآءَ أَحَدٞ مِّنكُم مِّنَ ٱلۡغَآئِطِ أَوۡ لَٰمَسۡتُمُ ٱلنِّسَآءَ فَلَمۡ تَجِدُواْ مَآءٗ فَتَيَمَّمُواْ صَعِيدٗا طَيِّبٗا فَٱمۡسَحُواْ بِوُجُوهِكُمۡ وَأَيۡدِيكُمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَفُوًّا غَفُورًا

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku kusanci salla alhalin kuna cikin maye har sai kun san abin da kuke faxa[1], haka mai janaba, sai dai in masu qetara hanya ne, har sai kun yi wanka. Idan kuma kun kasance marasa lafiya ko a halin tafiya, ko xaya daga cikinku ya dawo daga bahaya ko kuma kuka sadu da mata kuma ba ku sami ruwa ba, to sai ku nufi doron qasa mai tsarki ku yi taimama, sai ku shafi fuskokinku da hannayenku. Lalle Allah Ya kasance Mai afuwa ne, Mai gafara


1- Wannan ayar an shafe ta da ayar haramta shan giya baki xaya da ke cikin Suratun Ma’idah, aya ta 90.


Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 6

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا قُمۡتُمۡ إِلَى ٱلصَّلَوٰةِ فَٱغۡسِلُواْ وُجُوهَكُمۡ وَأَيۡدِيَكُمۡ إِلَى ٱلۡمَرَافِقِ وَٱمۡسَحُواْ بِرُءُوسِكُمۡ وَأَرۡجُلَكُمۡ إِلَى ٱلۡكَعۡبَيۡنِۚ وَإِن كُنتُمۡ جُنُبٗا فَٱطَّهَّرُواْۚ وَإِن كُنتُم مَّرۡضَىٰٓ أَوۡ عَلَىٰ سَفَرٍ أَوۡ جَآءَ أَحَدٞ مِّنكُم مِّنَ ٱلۡغَآئِطِ أَوۡ لَٰمَسۡتُمُ ٱلنِّسَآءَ فَلَمۡ تَجِدُواْ مَآءٗ فَتَيَمَّمُواْ صَعِيدٗا طَيِّبٗا فَٱمۡسَحُواْ بِوُجُوهِكُمۡ وَأَيۡدِيكُم مِّنۡهُۚ مَا يُرِيدُ ٱللَّهُ لِيَجۡعَلَ عَلَيۡكُم مِّنۡ حَرَجٖ وَلَٰكِن يُرِيدُ لِيُطَهِّرَكُمۡ وَلِيُتِمَّ نِعۡمَتَهُۥ عَلَيۡكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ

Ya ku waxanda suka yi imani, idan kun tashi za ku yi salla, to ku wanke fuskokinku da hannayenku zuwa gwiwoyinsu, kuma ku shafi kawunanku, kuma (ku wanke) qafafunku zuwa idon sawu. Kuma idan kun kasance masu janaba, to sai ku tsarkaka. Idan kuma kun kasance marasa lafiya, ko a halin tafiya, ko xaya daga cikinku ya dawo daga bayan gari, ko kuka sadu da mata, kuma sai ba ku sami ruwa ba, to ku yi taimama a doron qasa mai tsarki, ku shafi fuskokinku da hannayenku daga shi. Allah ba Yana nufin Ya sanya qunci a tare da ku ba ne, a’a, Yana nufi ne Ya tsarkake ku, kuma Ya cika ni’imarsa a gare ku, don ku zamo masu godiya