Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 6

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ سَوَآءٌ عَلَيۡهِمۡ ءَأَنذَرۡتَهُمۡ أَمۡ لَمۡ تُنذِرۡهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ

Lalle waxanda suka kafirta, duk xaya ne a gare su, ka yi musu gargaxi ko ba ka yi musu ba, ba za su yi imani ba



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 7

خَتَمَ ٱللَّهُ عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ وَعَلَىٰ سَمۡعِهِمۡۖ وَعَلَىٰٓ أَبۡصَٰرِهِمۡ غِشَٰوَةٞۖ وَلَهُمۡ عَذَابٌ عَظِيمٞ

Allah Ya toshe zukatansu da jinsu, kuma akwai wani lulluvi a kan idanunsu, kuma suna da azaba mai girma



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 8

وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَقُولُ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ وَبِٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَمَا هُم بِمُؤۡمِنِينَ

A cikin mutane kuma akwai waxanda suke cewa: “Mun yi imani da Allah kuma mun yi imani da ranar lahira,” alhalin su ba muminai ne ba



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 9

يُخَٰدِعُونَ ٱللَّهَ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَمَا يَخۡدَعُونَ إِلَّآ أَنفُسَهُمۡ وَمَا يَشۡعُرُونَ

Suna ganin suna yaudarar Allah ne da waxanda suka yi imani, amma kuwa ba kowa suke yaudara ba sai kawunansu, kuma su ba sa jin hakan



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 171

وَمَثَلُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ كَمَثَلِ ٱلَّذِي يَنۡعِقُ بِمَا لَا يَسۡمَعُ إِلَّا دُعَآءٗ وَنِدَآءٗۚ صُمُّۢ بُكۡمٌ عُمۡيٞ فَهُمۡ لَا يَعۡقِلُونَ

Misalin wadanda suka kafirta kamar misalin wanda yake daga sauti ne ga wanda ba ya jin (komai) sai kira da sowa. Kurame ne, bebaye ne, makafi ne, don haka su ba sa hankalta



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 212

زُيِّنَ لِلَّذِينَ كَفَرُواْ ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَا وَيَسۡخَرُونَ مِنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْۘ وَٱلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْ فَوۡقَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۗ وَٱللَّهُ يَرۡزُقُ مَن يَشَآءُ بِغَيۡرِ حِسَابٖ

An qawata wa kafirai rayuwar duniya, kuma suna yin izgili ga waxanda suka yi imani. Waxanda kuwa suka yi taqawa su ne a samansu a ranar alqiyama. Kuma Allah Yana arzurta wanda ya ga dama, ba tare da lissafi ba



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 257

ٱللَّهُ وَلِيُّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ يُخۡرِجُهُم مِّنَ ٱلظُّلُمَٰتِ إِلَى ٱلنُّورِۖ وَٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَوۡلِيَآؤُهُمُ ٱلطَّـٰغُوتُ يُخۡرِجُونَهُم مِّنَ ٱلنُّورِ إِلَى ٱلظُّلُمَٰتِۗ أُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ

Allah Shi ne Majivincin lamarin waxanda suka yi imani, Yana fitar da su daga duffai zuwa ga haske; waxanda suka kafirce kuwa, majivinta lamarinsu su ne xagutai, suna fitar da su daga haske zuwa duffai. Waxannan su ne ‘yan wuta; su masu dawwama ne a cikinta



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 90

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بَعۡدَ إِيمَٰنِهِمۡ ثُمَّ ٱزۡدَادُواْ كُفۡرٗا لَّن تُقۡبَلَ تَوۡبَتُهُمۡ وَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلضَّآلُّونَ

Lalle waxanda suka kafirta bayan imaninsu, sannan suka qara zurfi cikin kafirci, to ba za a karvi tubansu ba, kuma waxannan su ne vatattu



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 98

قُلۡ يَـٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ لِمَ تَكۡفُرُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَٱللَّهُ شَهِيدٌ عَلَىٰ مَا تَعۡمَلُونَ

Ka ce: “Ya ku Ma’abota Littafi, don me kuke kafirce wa ayoyin Allah, kuma alhalin Allah Mai ba da shaida ne ga abin da kuke aikatawa?”



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 37

ٱلَّذِينَ يَبۡخَلُونَ وَيَأۡمُرُونَ ٱلنَّاسَ بِٱلۡبُخۡلِ وَيَكۡتُمُونَ مَآ ءَاتَىٰهُمُ ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦۗ وَأَعۡتَدۡنَا لِلۡكَٰفِرِينَ عَذَابٗا مُّهِينٗا

Su ne waxanda suke rowa kuma suke umartar mutane da rowa kuma suke voye abin da Allah Ya ba su na falalarsa. Mun kuwa yi tanadin azaba mai wulaqantarwa ga kafirai



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 38

وَٱلَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمۡوَٰلَهُمۡ رِئَآءَ ٱلنَّاسِ وَلَا يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَلَا بِٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۗ وَمَن يَكُنِ ٱلشَّيۡطَٰنُ لَهُۥ قَرِينٗا فَسَآءَ قَرِينٗا

Waxanda kuma suke ciyar da dukiyoyinsu don mutane su gani, kuma ba sa yin imani da Allah, ba sa kuma yin imani da ranar qarshe. Duk wanda Shaixan ya kasance shi ne abokinsa, to tir da aboki irin wannan



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 150

إِنَّ ٱلَّذِينَ يَكۡفُرُونَ بِٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦ وَيُرِيدُونَ أَن يُفَرِّقُواْ بَيۡنَ ٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦ وَيَقُولُونَ نُؤۡمِنُ بِبَعۡضٖ وَنَكۡفُرُ بِبَعۡضٖ وَيُرِيدُونَ أَن يَتَّخِذُواْ بَيۡنَ ذَٰلِكَ سَبِيلًا

Lalle waxanda suke kafirce wa Allah da manzanninsa, kuma suke nufin su nuna bambanci tsakanin Allah da manzanninsa, kuma suna cewa: “Mun yi imani da wasu, mun kuma kafirce wa wasu,” kuma suna son su riqi wani tafarki tsakanin wannan (imani da kafirci)



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 151

أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡكَٰفِرُونَ حَقّٗاۚ وَأَعۡتَدۡنَا لِلۡكَٰفِرِينَ عَذَابٗا مُّهِينٗا

Waxannan su ne kafirai na haqiqa. Kuma Mun yi wa kafirai tanadin wata azaba mai wulaqantarwa



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 10

وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَكَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَآ أُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَحِيمِ

Kuma waxanda suka kafirta, suka kuma qaryata ayoyinmu, waxannan su ne ‘yan wuta



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 17

لَّقَدۡ كَفَرَ ٱلَّذِينَ قَالُوٓاْ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡمَسِيحُ ٱبۡنُ مَرۡيَمَۚ قُلۡ فَمَن يَمۡلِكُ مِنَ ٱللَّهِ شَيۡـًٔا إِنۡ أَرَادَ أَن يُهۡلِكَ ٱلۡمَسِيحَ ٱبۡنَ مَرۡيَمَ وَأُمَّهُۥ وَمَن فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗاۗ وَلِلَّهِ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَاۚ يَخۡلُقُ مَا يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Lalle haqiqa, waxannan da suka ce: “Lalle Allah Shi ne Almasihu xan Maryamu” sun kafirta. Ka ce: “To wane ne ya isa ya hana Allah, idan Ya yi nufin Ya hallaka Almasihu xan Maryamu da mahaifiyarsa da duk wanda yake ban qasa gaba xaya? Allah kuwa Shi Yake mallakar abin da yake cikin sammai da qasa da kuma abin da yake tsakaninsu. Yana halittar abin da Ya ga dama. Kuma Allah Mai cikakken iko ne a kan komai.”



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 72

لَقَدۡ كَفَرَ ٱلَّذِينَ قَالُوٓاْ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡمَسِيحُ ٱبۡنُ مَرۡيَمَۖ وَقَالَ ٱلۡمَسِيحُ يَٰبَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ رَبِّي وَرَبَّكُمۡۖ إِنَّهُۥ مَن يُشۡرِكۡ بِٱللَّهِ فَقَدۡ حَرَّمَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِ ٱلۡجَنَّةَ وَمَأۡوَىٰهُ ٱلنَّارُۖ وَمَا لِلظَّـٰلِمِينَ مِنۡ أَنصَارٖ

Lalle haqiqa waxanda suka ce: “Lalle Allah Shi ne Almasihu xan Maryamu” sun kafirta. Shi kuwa Almasihu cewa ya yi: “Ya ku Bani-Isra’ila, ku bauta wa Allah Ubangijina kuma Ubangijinku. Lalle yadda al’amarin yake, duk wanda ya yi shirka da Allah, to haqiqa Allah Ya haramta masa shiga Aljanna, kuma makomarsa ita ce wuta, kuma azzalumai ba su da wasu mataimaka.”



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 73

لَّقَدۡ كَفَرَ ٱلَّذِينَ قَالُوٓاْ إِنَّ ٱللَّهَ ثَالِثُ ثَلَٰثَةٖۘ وَمَا مِنۡ إِلَٰهٍ إِلَّآ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۚ وَإِن لَّمۡ يَنتَهُواْ عَمَّا يَقُولُونَ لَيَمَسَّنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۡهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٌ

Lalle haqiqa waxannan da suka ce: “Lalle Allah Shi ne na cikon (alloli) uku,”[1] sun kafirta. Babu kuwa wani abin bautawa na gaskiya, sai abin bauta Xaya tal. Idan ba su bar abin da suke faxa xin nan ba, lalle azaba mai raxaxi za ta shafi waxanda suka kafirta daga cikinsu


1- Ana nufin aqidar Nasara da suke cewa, abu uku ne suka haxu suka zama Allah, watau Isa da mahaifiyarsa Maryamu da kuma Allah.


Capítulo: Suratul An’am

Verso : 122

أَوَمَن كَانَ مَيۡتٗا فَأَحۡيَيۡنَٰهُ وَجَعَلۡنَا لَهُۥ نُورٗا يَمۡشِي بِهِۦ فِي ٱلنَّاسِ كَمَن مَّثَلُهُۥ فِي ٱلظُّلُمَٰتِ لَيۡسَ بِخَارِجٖ مِّنۡهَاۚ كَذَٰلِكَ زُيِّنَ لِلۡكَٰفِرِينَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Shin yanzu wanda ya kasance matacce (kafiri), sai Muka rayar da shi, kuma Muka sanya masa haske (na shiriya), yana tafiya da shi cikin mutane, (yanzu) zai zama kamar wanda yake cikin duhu (na kafirci), ta yadda ba zai iya fita daga cikinsa ba? Kamar haka ne aka qawata wa kafirai abin da suka kasance suna aikatawa



Capítulo: Suratul A’araf

Verso : 101

تِلۡكَ ٱلۡقُرَىٰ نَقُصُّ عَلَيۡكَ مِنۡ أَنۢبَآئِهَاۚ وَلَقَدۡ جَآءَتۡهُمۡ رُسُلُهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ فَمَا كَانُواْ لِيُؤۡمِنُواْ بِمَا كَذَّبُواْ مِن قَبۡلُۚ كَذَٰلِكَ يَطۡبَعُ ٱللَّهُ عَلَىٰ قُلُوبِ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Waxancan alqaryun Muna ba ka labarinsu ne. Kuma lalle haqiqa manzanninsu sun zo musu da hujjoji bayyanannu, amma ba su kasance masu yin imani ba, saboda qaryatawar da suka yi a da. Kamar haka ne Allah Yake rufe zukatan kafirai



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 36

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ يُنفِقُونَ أَمۡوَٰلَهُمۡ لِيَصُدُّواْ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِۚ فَسَيُنفِقُونَهَا ثُمَّ تَكُونُ عَلَيۡهِمۡ حَسۡرَةٗ ثُمَّ يُغۡلَبُونَۗ وَٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِلَىٰ جَهَنَّمَ يُحۡشَرُونَ

Lalle waxanda suka kafirta suna kashe dukiyoyinsu don su toshe hanyar Allah. To da sannu za su kashe ta (dukiyar) sannan ta zama nadama a gare su, sannan kuma a rinjaye su. Waxanda kuwa suka kafirta a Jahannama za a tattara su



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 73

وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بَعۡضُهُمۡ أَوۡلِيَآءُ بَعۡضٍۚ إِلَّا تَفۡعَلُوهُ تَكُن فِتۡنَةٞ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَفَسَادٞ كَبِيرٞ

Waxanda kuwa suka kafirta, su masu qaunar juna ne. Idan ku ma ba ku aikata haka ba, to za a samu wata fitina a bayan qasa da kuma wata varna mai girma



Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 37

إِنَّمَا ٱلنَّسِيٓءُ زِيَادَةٞ فِي ٱلۡكُفۡرِۖ يُضَلُّ بِهِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ يُحِلُّونَهُۥ عَامٗا وَيُحَرِّمُونَهُۥ عَامٗا لِّيُوَاطِـُٔواْ عِدَّةَ مَا حَرَّمَ ٱللَّهُ فَيُحِلُّواْ مَا حَرَّمَ ٱللَّهُۚ زُيِّنَ لَهُمۡ سُوٓءُ أَعۡمَٰلِهِمۡۗ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Lalle jinkiri[1] ba wani abu ba ne ban da qari cikin kafirci, wanda da shi (jinkirin) ake vatar da waxanda suka kafirta, suna halatta shi a wata shekarar, su kuma haramta shi a wata, wai don su daidaita adadin abin da Allah Ya haramta, sai su halatta abin da Allah Ya haramta. An qawata musu munanan ayyukansu. Allah kuwa ba Ya shiryar da mutane kafirai


1- Wata mummunar al’ada ce ta Larabawa a jahiiyya, sukan jinkirta watan Muharram su musanya shi da Safar, domin su halatta wa kansu yin yaqi a cikinsa.


Capítulo: Suratut Tauba

Verso : 74

يَحۡلِفُونَ بِٱللَّهِ مَا قَالُواْ وَلَقَدۡ قَالُواْ كَلِمَةَ ٱلۡكُفۡرِ وَكَفَرُواْ بَعۡدَ إِسۡلَٰمِهِمۡ وَهَمُّواْ بِمَا لَمۡ يَنَالُواْۚ وَمَا نَقَمُوٓاْ إِلَّآ أَنۡ أَغۡنَىٰهُمُ ٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥ مِن فَضۡلِهِۦۚ فَإِن يَتُوبُواْ يَكُ خَيۡرٗا لَّهُمۡۖ وَإِن يَتَوَلَّوۡاْ يُعَذِّبۡهُمُ ٱللَّهُ عَذَابًا أَلِيمٗا فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِۚ وَمَا لَهُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ مِن وَلِيّٖ وَلَا نَصِيرٖ

Suna rantsewa da Allah kan ba su faxi (komai) ba, alhali kuwa tabbas sun faxi kalmar kafirci, suka kuma kafirta bayan musuluntarsu, suka kuma yi qudirin aikata abin da ba su samu (dama) ba[1]; ba kuwa abin da suke jin haushi sai kawai don Allah da Manzonsa sun wadata su daga falalarsa. To idan suka tuba zai fi musu alheri; idan kuwa suka juya baya to Allah zai azabtar da su azaba mai raxaxi a duniya da lahira; ba su da kuwa wani majivincin lamari ko wani mataimaki a bayan qasa


1- Watau mugun shirinsu na kashe Annabi () lokacin da yake komawa Madina daga yaqin Tabuka.


Capítulo: Suratu Yunus

Verso : 96

إِنَّ ٱلَّذِينَ حَقَّتۡ عَلَيۡهِمۡ كَلِمَتُ رَبِّكَ لَا يُؤۡمِنُونَ

Lalle waxanda kalmar Ubangijinka ta tabbata a kansu (ta zamansu ‘yan wuta) ba za su yi imani ba



Capítulo: Suratu Yunus

Verso : 97

وَلَوۡ جَآءَتۡهُمۡ كُلُّ ءَايَةٍ حَتَّىٰ يَرَوُاْ ٱلۡعَذَابَ ٱلۡأَلِيمَ

Ko da kuwa dukkanin ayoyi sun zo musu har sai sun ga azaba mai raxaxi



Capítulo: Suratur Ra’ad

Verso : 33

أَفَمَنۡ هُوَ قَآئِمٌ عَلَىٰ كُلِّ نَفۡسِۭ بِمَا كَسَبَتۡۗ وَجَعَلُواْ لِلَّهِ شُرَكَآءَ قُلۡ سَمُّوهُمۡۚ أَمۡ تُنَبِّـُٔونَهُۥ بِمَا لَا يَعۡلَمُ فِي ٱلۡأَرۡضِ أَم بِظَٰهِرٖ مِّنَ ٱلۡقَوۡلِۗ بَلۡ زُيِّنَ لِلَّذِينَ كَفَرُواْ مَكۡرُهُمۡ وَصُدُّواْ عَنِ ٱلسَّبِيلِۗ وَمَن يُضۡلِلِ ٱللَّهُ فَمَا لَهُۥ مِنۡ هَادٖ

Yanzu wanda Yake tsaye a kan kula da kowane rai game da abin da ya aikata, (zai zama daidai da wanda ba haka ba?) Sun kuma sanya wa Allah abokan tarayya. Ka ce: (da su) “Ku faxa min sunayensu. Ko kuwa kuna ba Shi labarin abin da bai sani ba ne a bayan qasa, ko kuma dai kun riqe wata vatacciyar magana ce?” Bari dai; an dai qawata wa kafirai makircinsu ne kawai, aka kuma toshe musu hanyar (Allah). Wanda kuwa Allah Ya vatar to ba shi da wani mai shiryarwa



Capítulo: Suratu Ibrahim

Verso : 18

مَّثَلُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِرَبِّهِمۡۖ أَعۡمَٰلُهُمۡ كَرَمَادٍ ٱشۡتَدَّتۡ بِهِ ٱلرِّيحُ فِي يَوۡمٍ عَاصِفٖۖ لَّا يَقۡدِرُونَ مِمَّا كَسَبُواْ عَلَىٰ شَيۡءٖۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلضَّلَٰلُ ٱلۡبَعِيدُ

Misalin waxanda suka kafirce wa Ubangijnsu; ayyukansu sun yi kama da toka wadda iska mai tsananin qarfi ta kwasa a wata rana mai guguwa; ba za su sami iko a kan komai ba dangane da abin da suka aikata (na kirki). Wannan shi ne vata mai nisa



Capítulo: Suratu Ibrahim

Verso : 28

۞أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ بَدَّلُواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ كُفۡرٗا وَأَحَلُّواْ قَوۡمَهُمۡ دَارَ ٱلۡبَوَارِ

Shin ba ka ga waxanda suka musanya ni’imar Allah da kafirci ba[1], suka kuma jefa mutanensu gidan hallaka?


1- Su ne kafiran Quraishawa.


Capítulo: Suratu Ibrahim

Verso : 29

جَهَنَّمَ يَصۡلَوۡنَهَاۖ وَبِئۡسَ ٱلۡقَرَارُ

(Watau) Jahannama, za su shige ta; makoma kuwa ta munana



Capítulo: Suratu Ibrahim

Verso : 30

وَجَعَلُواْ لِلَّهِ أَندَادٗا لِّيُضِلُّواْ عَن سَبِيلِهِۦۗ قُلۡ تَمَتَّعُواْ فَإِنَّ مَصِيرَكُمۡ إِلَى ٱلنَّارِ

Sun sanya wa Allah abokan tarayya don su vatar (da mutane) daga hanyarsa. Ka ce: “Ku ji daxi (kaxan a duniya), to lalle makomarku wuta ce!”