لَّا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ إِن طَلَّقۡتُمُ ٱلنِّسَآءَ مَا لَمۡ تَمَسُّوهُنَّ أَوۡ تَفۡرِضُواْ لَهُنَّ فَرِيضَةٗۚ وَمَتِّعُوهُنَّ عَلَى ٱلۡمُوسِعِ قَدَرُهُۥ وَعَلَى ٱلۡمُقۡتِرِ قَدَرُهُۥ مَتَٰعَۢا بِٱلۡمَعۡرُوفِۖ حَقًّا عَلَى ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Babu laifi (sadaqi) a kanku idan kun saki mata, matuqar ba ku riga kun sadu da su ko kuma kun yanka musu sadaki sananne ba. Sai ku yi musu kyauta (ta kwantar da hankali); mai yalwa daidai yalwarsa; talaka ma daidai qarfinsa. (Wannan) wata kyauta ce (da za a bayar) ta hanyar da aka saba; haqqi ne a kan masu kyautatawa[1]
1- Allah ya yi umarni ga mijin wanda ya saki matarsa kafin ya tare da ita, lalle ya yi mata wata kyauta ta kwantar da hankali gwargwadon qarfinsa.
وَإِن طَلَّقۡتُمُوهُنَّ مِن قَبۡلِ أَن تَمَسُّوهُنَّ وَقَدۡ فَرَضۡتُمۡ لَهُنَّ فَرِيضَةٗ فَنِصۡفُ مَا فَرَضۡتُمۡ إِلَّآ أَن يَعۡفُونَ أَوۡ يَعۡفُوَاْ ٱلَّذِي بِيَدِهِۦ عُقۡدَةُ ٱلنِّكَاحِۚ وَأَن تَعۡفُوٓاْ أَقۡرَبُ لِلتَّقۡوَىٰۚ وَلَا تَنسَوُاْ ٱلۡفَضۡلَ بَيۡنَكُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٌ
Idan kuwa kun sake su ne tun kafin ku sadu da su, alhalin kuma kun yanka musu sadaki, to sai (ku bayar) da rabin abin da kuka yanka, sai fa in su matan sun yi afuwa ko kuma wanda a hannunsa igiyar aure take ya yi afuwa[1]; kuma ku yi afuwa shi ya fi kusa ga taqawa. Kuma kada ku manta da kyautatawar da take tsakaninku. Lalle Allah Mai ganin abin da kuke aikatawa ne
1- Wanda igiyar aure take hannusa, shi ne mijin. Yana iya yafe wa, ya bar mata duk sadakin baki xaya.
وَلِلۡمُطَلَّقَٰتِ مَتَٰعُۢ بِٱلۡمَعۡرُوفِۖ حَقًّا عَلَى ٱلۡمُتَّقِينَ
Kuma matan da aka sake su suna da wata kyauta ta kwantar da hankali ta hanyar da aka saba, (wannan) haqqi ne a kan masu taqawa
وَإِنۡ أَرَدتُّمُ ٱسۡتِبۡدَالَ زَوۡجٖ مَّكَانَ زَوۡجٖ وَءَاتَيۡتُمۡ إِحۡدَىٰهُنَّ قِنطَارٗا فَلَا تَأۡخُذُواْ مِنۡهُ شَيۡـًٔاۚ أَتَأۡخُذُونَهُۥ بُهۡتَٰنٗا وَإِثۡمٗا مُّبِينٗا
Kuma idan kun yi nufin musanya wata mace a gurbin wata macen, kuma kun riga kun ba wa xayarsu dukiya mai yawa (ta sadaki), to kar ku karvi komai daga cikinsa. Shin za ku karve shi ne a kan zalunci da laifi qarara?
وَكَيۡفَ تَأۡخُذُونَهُۥ وَقَدۡ أَفۡضَىٰ بَعۡضُكُمۡ إِلَىٰ بَعۡضٖ وَأَخَذۡنَ مِنكُم مِّيثَٰقًا غَلِيظٗا
Kuma ta yaya za ku karve shi alhali kuma kun riga kun sadu da juna, kuma sun riqi wani alqawari mai qarfi daga wajenku?
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ إِذَا طَلَّقۡتُمُ ٱلنِّسَآءَ فَطَلِّقُوهُنَّ لِعِدَّتِهِنَّ وَأَحۡصُواْ ٱلۡعِدَّةَۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ رَبَّكُمۡۖ لَا تُخۡرِجُوهُنَّ مِنۢ بُيُوتِهِنَّ وَلَا يَخۡرُجۡنَ إِلَّآ أَن يَأۡتِينَ بِفَٰحِشَةٖ مُّبَيِّنَةٖۚ وَتِلۡكَ حُدُودُ ٱللَّهِۚ وَمَن يَتَعَدَّ حُدُودَ ٱللَّهِ فَقَدۡ ظَلَمَ نَفۡسَهُۥۚ لَا تَدۡرِي لَعَلَّ ٱللَّهَ يُحۡدِثُ بَعۡدَ ذَٰلِكَ أَمۡرٗا
Ya kai wannan Annabi, (ka ce da jama’arka): “Idan za ku saki mata sai ku sake su a farkon iddarsu[1], kuma ku kula da kiyaye qidaya idda[2]; kuma ku kiyaye dokokin Ubangijinku; kada ku fitar da su daga xakunansu, su ma kada su fita sai dai idan sun aikata alfasha bayayyananna. Waxannan kuwa su ne iyakokin Allah. Wanda kuwa duk ya qetare iyakokin Allah, to haqiqa ya zalunci kansa. Ba ka sani ba ko Allah zai farar da wani al’amari bayan wannan[3]
1- Watau lokacin da suka yi tsarkin haila wanda kuma ba su sadu da su ba a cikinsa, ko kuma idan ciki ya bayyana.
2- Domin su iya dawo da matansu kafin qarewarta idan suna buqatar yin haka.
3- Watau Allah ya sake kawo jituwa a tsakanin mijin da matar su fahimci juna su mayar da aurensu.
فَإِذَا بَلَغۡنَ أَجَلَهُنَّ فَأَمۡسِكُوهُنَّ بِمَعۡرُوفٍ أَوۡ فَارِقُوهُنَّ بِمَعۡرُوفٖ وَأَشۡهِدُواْ ذَوَيۡ عَدۡلٖ مِّنكُمۡ وَأَقِيمُواْ ٱلشَّهَٰدَةَ لِلَّهِۚ ذَٰلِكُمۡ يُوعَظُ بِهِۦ مَن كَانَ يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۚ وَمَن يَتَّقِ ٱللَّهَ يَجۡعَل لَّهُۥ مَخۡرَجٗا
Idan kuma sun kusa isa qarshen iddarsu, to ku riqe su da kyautatawa (ku yi kome), ko kuma ku rabu da su da kyautatawa, kuma ku kafa shaidar adilai guda biyu daga cikinku, ku kuma tsayar da shaidarku saboda Allah. Wannan shi ne ake yin wa’azi da shi ga wanda ya kasance yana yin imani da Allah da ranar lahira. Wanda kuma ya kiyaye dokokin Allah to zai sanya masa mafita
وَيَرۡزُقۡهُ مِنۡ حَيۡثُ لَا يَحۡتَسِبُۚ وَمَن يَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِ فَهُوَ حَسۡبُهُۥٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ بَٰلِغُ أَمۡرِهِۦۚ قَدۡ جَعَلَ ٱللَّهُ لِكُلِّ شَيۡءٖ قَدۡرٗا
Ya kuma arzuta shi ta inda ba ya tsammani. Duk wanda kuma ya dogara ga Allah to Shi Ya ishe shi. Lalle Allah Mai zartar da al’amarinsa ne. Haqiqa kuma Allah Ya sanya iyaka ga kowane abu
وَٱلَّـٰٓـِٔي يَئِسۡنَ مِنَ ٱلۡمَحِيضِ مِن نِّسَآئِكُمۡ إِنِ ٱرۡتَبۡتُمۡ فَعِدَّتُهُنَّ ثَلَٰثَةُ أَشۡهُرٖ وَٱلَّـٰٓـِٔي لَمۡ يَحِضۡنَۚ وَأُوْلَٰتُ ٱلۡأَحۡمَالِ أَجَلُهُنَّ أَن يَضَعۡنَ حَمۡلَهُنَّۚ وَمَن يَتَّقِ ٱللَّهَ يَجۡعَل لَّهُۥ مِنۡ أَمۡرِهِۦ يُسۡرٗا
Waxanda kuma suka xebe qauna ta yin al’ada daga matanku, idan kun yi kokwanto, to iddarsu wata uku ne, da kuma waxanda ba su tava yin al’ada ba. Mata masu ciki kuma qarewar iddarsu ita ce haife cikinsu[1]. Duk kuma wanda ya kiyaye dokokin Allah, to zai sanya masa sauqi game da al’amarinsa
1- Hakanan iddar matar da mijinta ya rasu.
ذَٰلِكَ أَمۡرُ ٱللَّهِ أَنزَلَهُۥٓ إِلَيۡكُمۡۚ وَمَن يَتَّقِ ٱللَّهَ يُكَفِّرۡ عَنۡهُ سَيِّـَٔاتِهِۦ وَيُعۡظِمۡ لَهُۥٓ أَجۡرًا
Wannan shi ne hukuncin Allah da Ya saukar da shi a gare ku. Duk kuma wanda ya kiyaye dokokin Allah, to zai kankare masa zunubbansa Ya kuma girmama masa lada
أَسۡكِنُوهُنَّ مِنۡ حَيۡثُ سَكَنتُم مِّن وُجۡدِكُمۡ وَلَا تُضَآرُّوهُنَّ لِتُضَيِّقُواْ عَلَيۡهِنَّۚ وَإِن كُنَّ أُوْلَٰتِ حَمۡلٖ فَأَنفِقُواْ عَلَيۡهِنَّ حَتَّىٰ يَضَعۡنَ حَمۡلَهُنَّۚ فَإِنۡ أَرۡضَعۡنَ لَكُمۡ فَـَٔاتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ وَأۡتَمِرُواْ بَيۡنَكُم بِمَعۡرُوفٖۖ وَإِن تَعَاسَرۡتُمۡ فَسَتُرۡضِعُ لَهُۥٓ أُخۡرَىٰ
Ku zaunar da su (matayen) a inda kuka zauna daidai da samunku, kada kuma ku cuce su don ku quntata musu. Idan kuwa sun kasance masu ciki to sai ku ciyar da su har sai sun haife cikinsu. Sannan idan sun shayar muku da (‘ya’yanku) sai ku ba su ladansu; ku kuma daidaita a tsakaninku ta hanya tagari; idan kuma kuka kasa daidaitawa, to wata mai shayarwar sai ta shayar masa
لِيُنفِقۡ ذُو سَعَةٖ مِّن سَعَتِهِۦۖ وَمَن قُدِرَ عَلَيۡهِ رِزۡقُهُۥ فَلۡيُنفِقۡ مِمَّآ ءَاتَىٰهُ ٱللَّهُۚ لَا يُكَلِّفُ ٱللَّهُ نَفۡسًا إِلَّا مَآ ءَاتَىٰهَاۚ سَيَجۡعَلُ ٱللَّهُ بَعۡدَ عُسۡرٖ يُسۡرٗا
Mawadaci ya ciyar daidai da wadatarsa; wanda kuwa aka quntata masa arzikinsa, to ya ciyar daidai da abin da Allah Ya ba shi. Allah ba Ya xora wa rai sai gwargwadon abin da Ya ba shi. Kuma da sannu Allah zai sanya sauqi bayan tsanani