إِنَّ فِي خَلۡقِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَٱخۡتِلَٰفِ ٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِ وَٱلۡفُلۡكِ ٱلَّتِي تَجۡرِي فِي ٱلۡبَحۡرِ بِمَا يَنفَعُ ٱلنَّاسَ وَمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مِن مَّآءٖ فَأَحۡيَا بِهِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَا وَبَثَّ فِيهَا مِن كُلِّ دَآبَّةٖ وَتَصۡرِيفِ ٱلرِّيَٰحِ وَٱلسَّحَابِ ٱلۡمُسَخَّرِ بَيۡنَ ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَعۡقِلُونَ
Lalle a cikin halittar sammai da qasa da sassavawar dare da rana da jiragen ruwa da suke tafiya a kan ruwa da abin da yake amfanar mutane da kuma abin da Allah Ya saukar daga sama na ruwa, Ya rayar da qasa da shi bayan mutuwarta, Ya kuma yaxa duk wata halitta mai tafiya a cikin (qasa) da jujjuyawar iska, da kuma girgije da aka hore shi tsakanin sama da qasa, lalle akwai ayoyi ga mutane masu hankali
وَهُوَ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَخۡرَجۡنَا بِهِۦ نَبَاتَ كُلِّ شَيۡءٖ فَأَخۡرَجۡنَا مِنۡهُ خَضِرٗا نُّخۡرِجُ مِنۡهُ حَبّٗا مُّتَرَاكِبٗا وَمِنَ ٱلنَّخۡلِ مِن طَلۡعِهَا قِنۡوَانٞ دَانِيَةٞ وَجَنَّـٰتٖ مِّنۡ أَعۡنَابٖ وَٱلزَّيۡتُونَ وَٱلرُّمَّانَ مُشۡتَبِهٗا وَغَيۡرَ مُتَشَٰبِهٍۗ ٱنظُرُوٓاْ إِلَىٰ ثَمَرِهِۦٓ إِذَآ أَثۡمَرَ وَيَنۡعِهِۦٓۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكُمۡ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ
Kuma Shi ne Wanda Ya saukar da ruwa daga sama, sai Muka fitar da kowane irin dangin tsiro da shi, sannan Muka fitar da shi (tsiron) (wasu) koraye, daga gare shi kuma Muke fitar da qwayoyi a cunkushe daga gare shi. Kuma daga hudar dabino (ake samun) nonuna waxanda suke dab da qasa; da kuma waxansu lambuna na inabi da zaitun da ruman, masu kama da juna da kuma mabambanta. Ku kalli ‘ya’yansu idan suka yi ‘ya’ya da kuma lokacin da suka nuna. Lalle game da wannan akwai ayoyi ga mutanen da suka yi imani
قَالَ ٱهۡبِطُواْ بَعۡضُكُمۡ لِبَعۡضٍ عَدُوّٞۖ وَلَكُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ مُسۡتَقَرّٞ وَمَتَٰعٌ إِلَىٰ حِينٖ
Sai Ya ce: “Ku sauka, sashinku zai zama abokin adawa ga sashi; kuma kuna da wurin zama a qasa da abin jin daxi zuwa xan wani lokaci.”
قَالَ فِيهَا تَحۡيَوۡنَ وَفِيهَا تَمُوتُونَ وَمِنۡهَا تُخۡرَجُونَ
Ya ce: “A cikinta za ku rayu, kuma a cikinta za ku mutu, kuma daga cikinta za a fito da ku.”
وَهُوَ ٱلَّذِي مَدَّ ٱلۡأَرۡضَ وَجَعَلَ فِيهَا رَوَٰسِيَ وَأَنۡهَٰرٗاۖ وَمِن كُلِّ ٱلثَّمَرَٰتِ جَعَلَ فِيهَا زَوۡجَيۡنِ ٱثۡنَيۡنِۖ يُغۡشِي ٱلَّيۡلَ ٱلنَّهَارَۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَتَفَكَّرُونَ
Shi ne kuma Wanda Ya shimfixa qasa Ya kuma sanya turaku (na duwatsu) a cikinta da qoramu; kuma daga kowaxanne ‘ya’yan itace Ya sanya ma’aura biyu (mace da namiji); dare yana rufe rana. Lalle a game da waxannan abubuwan tabbas akwai ayoyi ga mutanen da suke tunani
وَفِي ٱلۡأَرۡضِ قِطَعٞ مُّتَجَٰوِرَٰتٞ وَجَنَّـٰتٞ مِّنۡ أَعۡنَٰبٖ وَزَرۡعٞ وَنَخِيلٞ صِنۡوَانٞ وَغَيۡرُ صِنۡوَانٖ يُسۡقَىٰ بِمَآءٖ وَٰحِدٖ وَنُفَضِّلُ بَعۡضَهَا عَلَىٰ بَعۡضٖ فِي ٱلۡأُكُلِۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَعۡقِلُونَ
A cikin qasa kuma da akwai yankuna masu maqotaka da juna, da gonakai na inabai da shuke-shuke da dabinai masu tushiya xaya da kuma waxanda suke kowane tushiyarsa daban, ana shayar da su da ruwa xaya[1], Muna kuma fifita wasunsu a kan wasu wajen xanxano. Haqiqa a game da wannan da akwai ayoyi ga mutanen da suke da hankali
1- To amma sai su fito mabambanta a kamanni da xanxano da girma, duk kuwa da cewa an shuka su a qasa xaya kuma s`un sha ruwa xaya.
وَٱلۡأَرۡضَ مَدَدۡنَٰهَا وَأَلۡقَيۡنَا فِيهَا رَوَٰسِيَ وَأَنۢبَتۡنَا فِيهَا مِن كُلِّ شَيۡءٖ مَّوۡزُونٖ
Qasa kuma Mun shimfixa ta Muka sanya manyan duwatsu a cikinta, Muka kuma tsiro da kowane abu a cikinta qayyadajje
يُنۢبِتُ لَكُم بِهِ ٱلزَّرۡعَ وَٱلزَّيۡتُونَ وَٱلنَّخِيلَ وَٱلۡأَعۡنَٰبَ وَمِن كُلِّ ٱلثَّمَرَٰتِۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّقَوۡمٖ يَتَفَكَّرُونَ
Da shi (ruwan) Yake tsiro muku da shuke-shuke da zaitun da dabinai da inabai da kuma kowanne irin ‘ya’yan itace. Lalle a game da wannan tabbas akwai aya ga mutanen da suke tunani
وَمَا ذَرَأَ لَكُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ مُخۡتَلِفًا أَلۡوَٰنُهُۥٓۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّقَوۡمٖ يَذَّكَّرُونَ
Da kuma abubuwan da Ya halitta muku a qasa masu launi iri daban-daban. Lalle a game da wannan tabbas akwai aya ga mutanen da suke wa’azantuwa
وَهُوَ ٱلَّذِي سَخَّرَ ٱلۡبَحۡرَ لِتَأۡكُلُواْ مِنۡهُ لَحۡمٗا طَرِيّٗا وَتَسۡتَخۡرِجُواْ مِنۡهُ حِلۡيَةٗ تَلۡبَسُونَهَاۖ وَتَرَى ٱلۡفُلۡكَ مَوَاخِرَ فِيهِ وَلِتَبۡتَغُواْ مِن فَضۡلِهِۦ وَلَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ
Shi ne kuma wanda Ya hore muku kogi don ku ci daddaxan nama mai taushi daga gare shi, ku kuma riqa fito da kayan ado daga cikinsa waxanda kuke xaurawa, kuma ka ga jiragen ruwa suna keta shi don kuma ku nema daga falalarsa (Ubangiji) don kuma ku riqa godiya
وَأَلۡقَىٰ فِي ٱلۡأَرۡضِ رَوَٰسِيَ أَن تَمِيدَ بِكُمۡ وَأَنۡهَٰرٗا وَسُبُلٗا لَّعَلَّكُمۡ تَهۡتَدُونَ
Ya kuma sanya wa qasa turaku don kada ta riqa tangal-tangal da ku da kuma qoramu da hanyoyi don ku riqa gane (inda kuka dosa)
وَٱللَّهُ أَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَحۡيَا بِهِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَآۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّقَوۡمٖ يَسۡمَعُونَ
Allah kuma Ya saukar da ruwa daga sama, sai Ya raya qasa da shi bayan mutuwarta. Lalle a game da wannan akwai aya ga mutanen da suke ji
تُسَبِّحُ لَهُ ٱلسَّمَٰوَٰتُ ٱلسَّبۡعُ وَٱلۡأَرۡضُ وَمَن فِيهِنَّۚ وَإِن مِّن شَيۡءٍ إِلَّا يُسَبِّحُ بِحَمۡدِهِۦ وَلَٰكِن لَّا تَفۡقَهُونَ تَسۡبِيحَهُمۡۚ إِنَّهُۥ كَانَ حَلِيمًا غَفُورٗا
Sammai bakwai da qasa da abin da yake cikinsu (duka) suna tsarkake Shi. Ba wani abu wanda ba ya tasbihi tare da gode masa, sai dai ba kwa fahimtar tasbihinsu. Lalle Shi Ya kasance Mai yawan haquri ne, Mai yawan gafara
إِنَّا جَعَلۡنَا مَا عَلَى ٱلۡأَرۡضِ زِينَةٗ لَّهَا لِنَبۡلُوَهُمۡ أَيُّهُمۡ أَحۡسَنُ عَمَلٗا
Lalle Mu Mun sanya abin da yake bayan qasa ya zama ado a gare ta, don (kuma) Mu jarraba su, wane ne daga cikinsu ya fi kyakkyawan aiki?
وَإِنَّا لَجَٰعِلُونَ مَا عَلَيۡهَا صَعِيدٗا جُرُزًا
Lalle kuma Mu za Mu mai da abin da yake kanta (ya zama) turvaya qeqasasshiya
تَكَادُ ٱلسَّمَٰوَٰتُ يَتَفَطَّرۡنَ مِنۡهُ وَتَنشَقُّ ٱلۡأَرۡضُ وَتَخِرُّ ٱلۡجِبَالُ هَدًّا
Sama ta kusa ta kece saboda shi (mummunan furucin), qasa kuma ta tsage, duwatsu kuma su zube su yi rugu-rugu
ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلۡأَرۡضَ مَهۡدٗا وَسَلَكَ لَكُمۡ فِيهَا سُبُلٗا وَأَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَخۡرَجۡنَا بِهِۦٓ أَزۡوَٰجٗا مِّن نَّبَاتٖ شَتَّىٰ
“(Shi ne) Wanda Ya sanya muku qasa a shimfixe, Ya kuma sanya muku hanyoyi na tafiya cikinta, kuma Ya saukar da ruwa daga sama”, sannan Muka fitar da dangogin shuke-shuke iri-iri da shi (ruwa)
كُلُواْ وَٱرۡعَوۡاْ أَنۡعَٰمَكُمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّأُوْلِي ٱلنُّهَىٰ
Ku ci (daga tsirran) kuma ku yi kiwon dabbobinku. Lalle a game da wannan akwai ayoyi ga ma’abota hankula
۞مِنۡهَا خَلَقۡنَٰكُمۡ وَفِيهَا نُعِيدُكُمۡ وَمِنۡهَا نُخۡرِجُكُمۡ تَارَةً أُخۡرَىٰ
Daga ita (qasar) Muka halicce ku, kuma a cikinta za Mu mayar da ku, daga ita kuma za Mu fito da ku a wani karon
أَوَلَمۡ يَرَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَنَّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ كَانَتَا رَتۡقٗا فَفَتَقۡنَٰهُمَاۖ وَجَعَلۡنَا مِنَ ٱلۡمَآءِ كُلَّ شَيۡءٍ حَيٍّۚ أَفَلَا يُؤۡمِنُونَ
Yanzu waxanda suka kafirta ba sa ganin cewa a da can sammai da qasa a haxe suke, sannan Muka raba su[1]; Muka kuma halicci duk wani abu mai rai daga ruwa? To me ya sa ba za su yi imani ba?
1- Watau Allah () ya fara halittar sammai da qasa a manne da juna daga bisani ya raba tsakaninsu.
وَجَعَلۡنَا فِي ٱلۡأَرۡضِ رَوَٰسِيَ أَن تَمِيدَ بِهِمۡ وَجَعَلۡنَا فِيهَا فِجَاجٗا سُبُلٗا لَّعَلَّهُمۡ يَهۡتَدُونَ
Muka kuma sanya kafaffun duwatsu a qasa don kar ta yi tangal-tangal da su, Muka kuma sanya wuraren tafiya a cikinta (su zama) hanyoyi don su gane (inda za su)
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِن كُنتُمۡ فِي رَيۡبٖ مِّنَ ٱلۡبَعۡثِ فَإِنَّا خَلَقۡنَٰكُم مِّن تُرَابٖ ثُمَّ مِن نُّطۡفَةٖ ثُمَّ مِنۡ عَلَقَةٖ ثُمَّ مِن مُّضۡغَةٖ مُّخَلَّقَةٖ وَغَيۡرِ مُخَلَّقَةٖ لِّنُبَيِّنَ لَكُمۡۚ وَنُقِرُّ فِي ٱلۡأَرۡحَامِ مَا نَشَآءُ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗى ثُمَّ نُخۡرِجُكُمۡ طِفۡلٗا ثُمَّ لِتَبۡلُغُوٓاْ أَشُدَّكُمۡۖ وَمِنكُم مَّن يُتَوَفَّىٰ وَمِنكُم مَّن يُرَدُّ إِلَىٰٓ أَرۡذَلِ ٱلۡعُمُرِ لِكَيۡلَا يَعۡلَمَ مِنۢ بَعۡدِ عِلۡمٖ شَيۡـٔٗاۚ وَتَرَى ٱلۡأَرۡضَ هَامِدَةٗ فَإِذَآ أَنزَلۡنَا عَلَيۡهَا ٱلۡمَآءَ ٱهۡتَزَّتۡ وَرَبَتۡ وَأَنۢبَتَتۡ مِن كُلِّ زَوۡجِۭ بَهِيجٖ
Ya ku mutane, idan kun zamanto cikin kokwanton tashi (bayan mutuwa), to lalle Mu Muka halicce ku daga qasa, sannan daga maniyyi, sannan daga gudan jini, sannan daga tsoka, mai cikakkiyar halitta da kuma wadda ba cikakkiya ba[1], don Mu bayyana muku (Ikonmu). Kuma Muna tabbatar da abin da Muka ga dama a cikin mahaifa har zuwa wani lokaci qayyadajje, sannan kuma Mu fito da ku kuna jarirai, sannan kuma don ku kai cikar qarfinku; daga cikinku akwai wanda za a karvi ransa, akwai kuma wanda za a bari har zuwa mafi qasqantar rayuwa don ya kai ga halin da ba zai san komai ba bayan kuwa da can ya sani. Za ka kuma ga qasa a qeqashe, sannan idan Muka saukar mata da ruwa sai ta girgiza ta kumbura kuma ta fitar da kowanne irin tsiro mai qayatarwa
1- Watau tsokar ta zama wata halitta wadda ba cikakken mutum ba, daga bisani a yi varin ta.
أَلَمۡ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ أَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَتُصۡبِحُ ٱلۡأَرۡضُ مُخۡضَرَّةًۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَطِيفٌ خَبِيرٞ
Shin ba ka ga cewa Allah ne Ya saukar da ruwa daga sama ba, sai qasa ta zama koriya shar? Lalle Allah Mai tausasawa ne, Masani
وَأَنزَلۡنَا مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءَۢ بِقَدَرٖ فَأَسۡكَنَّـٰهُ فِي ٱلۡأَرۡضِۖ وَإِنَّا عَلَىٰ ذَهَابِۭ بِهِۦ لَقَٰدِرُونَ
Muka kuma saukar da ruwa daga sama daidai gwargwado, sai Muka zaunar da shi a cikin qasa, kuma lalle Mu Masu iko ne a kan kawar da shi
فَأَنشَأۡنَا لَكُم بِهِۦ جَنَّـٰتٖ مِّن نَّخِيلٖ وَأَعۡنَٰبٖ لَّكُمۡ فِيهَا فَوَٰكِهُ كَثِيرَةٞ وَمِنۡهَا تَأۡكُلُونَ
Sai Muka samar muku gonaki na dabinai da inabai da shi (ruwan), kuna kuma da kayan marmari masu yawa a cikinsu (gonakin), kuma daga gare su kuke ci
أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ إِلَى ٱلۡأَرۡضِ كَمۡ أَنۢبَتۡنَا فِيهَا مِن كُلِّ زَوۡجٖ كَرِيمٍ
Shin ba su yi duba zuwa ga qasa ba, (su ga) dangogin tsirrai masu kyau nawa ne Muka tsirar daga cikinta?
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ
Lalle a game da wannan tabbas akwai aya (mai nuna cikar ikon Allah); kuma yawancinsu ba su zamanto masu imani ba
أَمَّنۡ خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَأَنزَلَ لَكُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَنۢبَتۡنَا بِهِۦ حَدَآئِقَ ذَاتَ بَهۡجَةٖ مَّا كَانَ لَكُمۡ أَن تُنۢبِتُواْ شَجَرَهَآۗ أَءِلَٰهٞ مَّعَ ٱللَّهِۚ بَلۡ هُمۡ قَوۡمٞ يَعۡدِلُونَ
Ko kuwa wane ne ya halicci sammai da qasa, ya kuma saukar muku da ruwa daga sama, sannan Muka tsirar da (shukokin) gonaki masu qayatarwa, ba kuwa za ku iya tsirar da bishiyoyinsu ba? Shin akwai wani abin bauta na gaskiya tare da Allah? A’a, su dai mutane ne da suke kauce wa gaskiya
يَٰعِبَادِيَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِنَّ أَرۡضِي وَٰسِعَةٞ فَإِيَّـٰيَ فَٱعۡبُدُونِ
Ya ku bayina waxanda suka yi imani, lalle qasata yalwatacciya ce, to Ni kaxai sai ku bauta Mini
ٱللَّهُ ٱلَّذِي يُرۡسِلُ ٱلرِّيَٰحَ فَتُثِيرُ سَحَابٗا فَيَبۡسُطُهُۥ فِي ٱلسَّمَآءِ كَيۡفَ يَشَآءُ وَيَجۡعَلُهُۥ كِسَفٗا فَتَرَى ٱلۡوَدۡقَ يَخۡرُجُ مِنۡ خِلَٰلِهِۦۖ فَإِذَآ أَصَابَ بِهِۦ مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦٓ إِذَا هُمۡ يَسۡتَبۡشِرُونَ
Allah (Shi ne) wanda Yake aiko da iska sai ta motsa girgije, sai Ya shimfixa shi a (sararin) sama yadda Ya ga dama, Ya kuma sanya shi yanki-yanki, sai ka ga ruwa yana fitowa ta tsakaninsa, to idan Ya saukar da shi ga waxanda Ya ga dama daga bayinsa sai ka gan su suna ta murna