Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 177

۞لَّيۡسَ ٱلۡبِرَّ أَن تُوَلُّواْ وُجُوهَكُمۡ قِبَلَ ٱلۡمَشۡرِقِ وَٱلۡمَغۡرِبِ وَلَٰكِنَّ ٱلۡبِرَّ مَنۡ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَٱلۡمَلَـٰٓئِكَةِ وَٱلۡكِتَٰبِ وَٱلنَّبِيِّـۧنَ وَءَاتَى ٱلۡمَالَ عَلَىٰ حُبِّهِۦ ذَوِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينَ وَٱبۡنَ ٱلسَّبِيلِ وَٱلسَّآئِلِينَ وَفِي ٱلرِّقَابِ وَأَقَامَ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَى ٱلزَّكَوٰةَ وَٱلۡمُوفُونَ بِعَهۡدِهِمۡ إِذَا عَٰهَدُواْۖ وَٱلصَّـٰبِرِينَ فِي ٱلۡبَأۡسَآءِ وَٱلضَّرَّآءِ وَحِينَ ٱلۡبَأۡسِۗ أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ صَدَقُواْۖ وَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُتَّقُونَ

Ba wai aikin xa’a shi ne ku juyar da fuskokinku mahudar rana ko mafaxarta ba ; sai dai aikin xa’a shi ne, wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira da mala’iku da littattafai da annabawa, kuma ya bayar da dukiyarsa, alhalin yana son ta, ga dangi na kusa da marayu da mabuqata da matafiyi da kuma masu roqo (bisa larura) da ‘yantar da bayi, sannan kuma ya tsayar da salla, kuma ya bayar da zakka, da kuma masu cika alqawarinsu idan suka qulla alqawari ; da masu haquri a cikin halin talauci da halin rashin lafiya da lokacin yaqi. Waxannan su ne waxanda suka yi gaskiya, kuma waxannan su ne masu taqawa



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 185

شَهۡرُ رَمَضَانَ ٱلَّذِيٓ أُنزِلَ فِيهِ ٱلۡقُرۡءَانُ هُدٗى لِّلنَّاسِ وَبَيِّنَٰتٖ مِّنَ ٱلۡهُدَىٰ وَٱلۡفُرۡقَانِۚ فَمَن شَهِدَ مِنكُمُ ٱلشَّهۡرَ فَلۡيَصُمۡهُۖ وَمَن كَانَ مَرِيضًا أَوۡ عَلَىٰ سَفَرٖ فَعِدَّةٞ مِّنۡ أَيَّامٍ أُخَرَۗ يُرِيدُ ٱللَّهُ بِكُمُ ٱلۡيُسۡرَ وَلَا يُرِيدُ بِكُمُ ٱلۡعُسۡرَ وَلِتُكۡمِلُواْ ٱلۡعِدَّةَ وَلِتُكَبِّرُواْ ٱللَّهَ عَلَىٰ مَا هَدَىٰكُمۡ وَلَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ

Watan Ramadan shi ne wanda aka saukar da Alqur’ani a cikinsa, shiriya ne ga mutane kuma ayoyi ne bayyanannu na shiriya, kuma mai rarrabewa (tsakanin qarya da gaskiya). Don haka duk wanda ya halarci wannan watan daga cikinku, to ya azumce shi, kuma wanda ya kasance marar lafiya ko a kan wata tafiya, to (idan ya sha azumi) sai ya rama a waxansu kwanakin na daban. Allah Yana nufin sauqi a gare ku, kuma ba Ya nufin tsanani a gare ku, don ku cika adadin (kwanakin Ramadan), kuma domin ku girmama Allah bisa ga shiryar da ku da Ya yi, don ku yi godiya