Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 168

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ كُلُواْ مِمَّا فِي ٱلۡأَرۡضِ حَلَٰلٗا طَيِّبٗا وَلَا تَتَّبِعُواْ خُطُوَٰتِ ٱلشَّيۡطَٰنِۚ إِنَّهُۥ لَكُمۡ عَدُوّٞ مُّبِينٌ

Ya ku mutane, ku ci halal mai daxi na abin da ke bayan qasa, kada kuma ku bi hanyoyin Shaixan, lalle shi maqiyi ne mai bayyana qiyayya a gare ku



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 172

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ كُلُواْ مِن طَيِّبَٰتِ مَا رَزَقۡنَٰكُمۡ وَٱشۡكُرُواْ لِلَّهِ إِن كُنتُمۡ إِيَّاهُ تَعۡبُدُونَ

Ya ku waxanda suka yi imani, ku ci daga daxaxan abin da Muka arzuta ku (da shi), kuma ku yi godiya ga Allah in har kun kasance Shi kaxai kuke bauta wa



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 173

إِنَّمَا حَرَّمَ عَلَيۡكُمُ ٱلۡمَيۡتَةَ وَٱلدَّمَ وَلَحۡمَ ٱلۡخِنزِيرِ وَمَآ أُهِلَّ بِهِۦ لِغَيۡرِ ٱللَّهِۖ فَمَنِ ٱضۡطُرَّ غَيۡرَ بَاغٖ وَلَا عَادٖ فَلَآ إِثۡمَ عَلَيۡهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٌ

(Allah) Ya haramta muku mushe ne kawai da jini da naman alade da abin da aka kira sunan wani ba Allah ba (lokacin yanka shi). Don haka duk wanda ya matsu, ba mai zalunci ba, kuma ba mai qetare iyaka ba, to babu laifi a kansa ya ci. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 93

۞كُلُّ ٱلطَّعَامِ كَانَ حِلّٗا لِّبَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ إِلَّا مَا حَرَّمَ إِسۡرَـٰٓءِيلُ عَلَىٰ نَفۡسِهِۦ مِن قَبۡلِ أَن تُنَزَّلَ ٱلتَّوۡرَىٰةُۚ قُلۡ فَأۡتُواْ بِٱلتَّوۡرَىٰةِ فَٱتۡلُوهَآ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

Duk wani abinci ya kasance halal ne ga Banu Israila sai abin da shi Isra’ilu[1] ya haramta wa kansa tun kafin a saukar da Attaura. Ka ce: “To ku zo da Attaura, sai ku karanta ta in kun kasance masu gaskiya.”


1- Isra’ilu: shi ne Annabi Ya’aqub (). Ya haramta wa kansa ne cin naman raquma da shan nononsu. Sannan daga baya su ma ‘ya’yansa suka yi koyi da shi.


Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 3

حُرِّمَتۡ عَلَيۡكُمُ ٱلۡمَيۡتَةُ وَٱلدَّمُ وَلَحۡمُ ٱلۡخِنزِيرِ وَمَآ أُهِلَّ لِغَيۡرِ ٱللَّهِ بِهِۦ وَٱلۡمُنۡخَنِقَةُ وَٱلۡمَوۡقُوذَةُ وَٱلۡمُتَرَدِّيَةُ وَٱلنَّطِيحَةُ وَمَآ أَكَلَ ٱلسَّبُعُ إِلَّا مَا ذَكَّيۡتُمۡ وَمَا ذُبِحَ عَلَى ٱلنُّصُبِ وَأَن تَسۡتَقۡسِمُواْ بِٱلۡأَزۡلَٰمِۚ ذَٰلِكُمۡ فِسۡقٌۗ ٱلۡيَوۡمَ يَئِسَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِن دِينِكُمۡ فَلَا تَخۡشَوۡهُمۡ وَٱخۡشَوۡنِۚ ٱلۡيَوۡمَ أَكۡمَلۡتُ لَكُمۡ دِينَكُمۡ وَأَتۡمَمۡتُ عَلَيۡكُمۡ نِعۡمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ ٱلۡإِسۡلَٰمَ دِينٗاۚ فَمَنِ ٱضۡطُرَّ فِي مَخۡمَصَةٍ غَيۡرَ مُتَجَانِفٖ لِّإِثۡمٖ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

An haramta muku (cin) mushe da jini da naman alade da abin da aka yanka shi da sunan wanin Allah, da (dabbar) da ta shaqe, da wadda aka doke ta, da wadda ta gangaro (daga sama), da dabbar da aka tunkura da qaho, da kuma abin da namun daji masu farauta suka ci, sai dai abin da kuka samu damar yankawa (daga cikinsu), da kuma abin da aka yanka a kan gumaka, da kuma neman sanin sa’a da kibau. Wannan fasiqanci ne. A yau kafirai sun xebe tsammani daga (karya) addininku, don haka kar ku ji tsoron su, ku ji tsoro Na Ni kaxai. A yau Na cika muku addininku, kuma Na cika muku ni’imata, kuma Na yardar muku Musulunci ya zamo shi ne addininku. Duk wanda ya matsu (ya ci abin da aka ambata a baya) saboda yunwa, ba yana mai karkata zuwa ga zunubi ba, to lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 4

يَسۡـَٔلُونَكَ مَاذَآ أُحِلَّ لَهُمۡۖ قُلۡ أُحِلَّ لَكُمُ ٱلطَّيِّبَٰتُ وَمَا عَلَّمۡتُم مِّنَ ٱلۡجَوَارِحِ مُكَلِّبِينَ تُعَلِّمُونَهُنَّ مِمَّا عَلَّمَكُمُ ٱللَّهُۖ فَكُلُواْ مِمَّآ أَمۡسَكۡنَ عَلَيۡكُمۡ وَٱذۡكُرُواْ ٱسۡمَ ٱللَّهِ عَلَيۡهِۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَرِيعُ ٱلۡحِسَابِ

Suna tambayar ka, mene ne aka halatta musu? Ka ce: “An halatta muku kyawawan abubuwa da kuma abin da dabbobinku da kuka koyar da su (farauta) suka kamo muku, kuna koya musu abin da Allah Ya koya muku, don haka ku ci daga duk abin da suka kamo muku, sannan ku ambaci sunan Allah a kansa; kuma ku kiyaye dokokin Allah. Lalle Allah Mai gaggawar hisabi ne



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 5

ٱلۡيَوۡمَ أُحِلَّ لَكُمُ ٱلطَّيِّبَٰتُۖ وَطَعَامُ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ حِلّٞ لَّكُمۡ وَطَعَامُكُمۡ حِلّٞ لَّهُمۡۖ وَٱلۡمُحۡصَنَٰتُ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ وَٱلۡمُحۡصَنَٰتُ مِنَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ مِن قَبۡلِكُمۡ إِذَآ ءَاتَيۡتُمُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ مُحۡصِنِينَ غَيۡرَ مُسَٰفِحِينَ وَلَا مُتَّخِذِيٓ أَخۡدَانٖۗ وَمَن يَكۡفُرۡ بِٱلۡإِيمَٰنِ فَقَدۡ حَبِطَ عَمَلُهُۥ وَهُوَ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ

A yau an halatta muku kyawawan abubuwa; kuma abincin waxanda aka bai wa Littafi halal ne a gare ku, ku ma abincinku halal ne a gare su; sannan kuma (Na halatta muku auren) mata kamammu daga cikin muminai, da kuma kamammu daga cikin waxanda aka bai wa Littafi a gabaninku, idan har kun ba su sadakinsu, kuna masu kame kawunanku, ba kuna mazinata ba, ba kuma kuna masu yin daduro ba. Duk kuwa wanda ya kafirce wa imani, haqiqa aikinsa ya rushe, kuma a ranar lahira yana cikin asararru



Capítulo: Suratul Ma’ida

Verso : 88

وَكُلُواْ مِمَّا رَزَقَكُمُ ٱللَّهُ حَلَٰلٗا طَيِّبٗاۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ ٱلَّذِيٓ أَنتُم بِهِۦ مُؤۡمِنُونَ

Kuma ku ci daga abin da Allah Ya arzuta ku da shi, wanda yake halal, mai daxi. Kuma ku kiyaye dokokin Allah Wanda kuke yin imani da Shi



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 145

قُل لَّآ أَجِدُ فِي مَآ أُوحِيَ إِلَيَّ مُحَرَّمًا عَلَىٰ طَاعِمٖ يَطۡعَمُهُۥٓ إِلَّآ أَن يَكُونَ مَيۡتَةً أَوۡ دَمٗا مَّسۡفُوحًا أَوۡ لَحۡمَ خِنزِيرٖ فَإِنَّهُۥ رِجۡسٌ أَوۡ فِسۡقًا أُهِلَّ لِغَيۡرِ ٱللَّهِ بِهِۦۚ فَمَنِ ٱضۡطُرَّ غَيۡرَ بَاغٖ وَلَا عَادٖ فَإِنَّ رَبَّكَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Ka ce: “Daga cikin abin da aka sauqar mini na manzanci ban samu wani abinci da aka haramta cinsa ba, sai fa idan ya zamo mushe ne ko jini mai kwarara, ko kuma naman alade, to lalle wannan qazanta ne, ko kuma abin da ya zamo fasiqanci ne wanda aka yanka shi ba da sunan Allah ba.” Sannan wanda ya matsu, ba tare da shisshigi ba, kuma ba yana mai qetare iyaka ba, to lalle Ubangijinka Mai gafara ne, Mai jin qai



Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 114

فَكُلُواْ مِمَّا رَزَقَكُمُ ٱللَّهُ حَلَٰلٗا طَيِّبٗا وَٱشۡكُرُواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ إِن كُنتُمۡ إِيَّاهُ تَعۡبُدُونَ

To ku ci halal mai daxi daga abin da Allah Ya arzuta ku da shi, kuma ku gode ni’imomin Allah in kun kasance Shi kaxai kuke bauta wa



Capítulo: Suratul Hajji

Verso : 28

لِّيَشۡهَدُواْ مَنَٰفِعَ لَهُمۡ وَيَذۡكُرُواْ ٱسۡمَ ٱللَّهِ فِيٓ أَيَّامٖ مَّعۡلُومَٰتٍ عَلَىٰ مَا رَزَقَهُم مِّنۢ بَهِيمَةِ ٱلۡأَنۡعَٰمِۖ فَكُلُواْ مِنۡهَا وَأَطۡعِمُواْ ٱلۡبَآئِسَ ٱلۡفَقِيرَ

Don su halarci amfanin da za su samu, kuma su ambaci sunan Allah cikin kwanaki sanannu a kan abin da Ya arzuta su da shi na dabbobin ni’ima (watau raquma da tumaki da awakai da shanu); sai ku ci daga gare su kuma ku ciyar da galavaitaccen matalauci



Capítulo: Suratul Hajji

Verso : 36

وَٱلۡبُدۡنَ جَعَلۡنَٰهَا لَكُم مِّن شَعَـٰٓئِرِ ٱللَّهِ لَكُمۡ فِيهَا خَيۡرٞۖ فَٱذۡكُرُواْ ٱسۡمَ ٱللَّهِ عَلَيۡهَا صَوَآفَّۖ فَإِذَا وَجَبَتۡ جُنُوبُهَا فَكُلُواْ مِنۡهَا وَأَطۡعِمُواْ ٱلۡقَانِعَ وَٱلۡمُعۡتَرَّۚ كَذَٰلِكَ سَخَّرۡنَٰهَا لَكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ

(Raquma) kuma masu qiba Mun sanya muku su alamomi ne na bautar Allah; kuna da amfani game da su (na rayuwarku). To sai ku ambaci sunan Allah a kansu suna tsaye a kan qafa uku (lokacin soke su). To idan ransu ya fita bayan sun faxi, sai ku ci daga gare su kuma ku ciyar da mai wadatar zuci da kuma mai bara. Kamar haka Muka hore muku su don ku yi godiya



Capítulo: Suratul Ahzab

Verso : 53

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَدۡخُلُواْ بُيُوتَ ٱلنَّبِيِّ إِلَّآ أَن يُؤۡذَنَ لَكُمۡ إِلَىٰ طَعَامٍ غَيۡرَ نَٰظِرِينَ إِنَىٰهُ وَلَٰكِنۡ إِذَا دُعِيتُمۡ فَٱدۡخُلُواْ فَإِذَا طَعِمۡتُمۡ فَٱنتَشِرُواْ وَلَا مُسۡتَـٔۡنِسِينَ لِحَدِيثٍۚ إِنَّ ذَٰلِكُمۡ كَانَ يُؤۡذِي ٱلنَّبِيَّ فَيَسۡتَحۡيِۦ مِنكُمۡۖ وَٱللَّهُ لَا يَسۡتَحۡيِۦ مِنَ ٱلۡحَقِّۚ وَإِذَا سَأَلۡتُمُوهُنَّ مَتَٰعٗا فَسۡـَٔلُوهُنَّ مِن وَرَآءِ حِجَابٖۚ ذَٰلِكُمۡ أَطۡهَرُ لِقُلُوبِكُمۡ وَقُلُوبِهِنَّۚ وَمَا كَانَ لَكُمۡ أَن تُؤۡذُواْ رَسُولَ ٱللَّهِ وَلَآ أَن تَنكِحُوٓاْ أَزۡوَٰجَهُۥ مِنۢ بَعۡدِهِۦٓ أَبَدًاۚ إِنَّ ذَٰلِكُمۡ كَانَ عِندَ ٱللَّهِ عَظِيمًا

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku shiga gidajen Annabi sai idan an yi muku izini zuwa (cin) abinci, alhali ba tare da kuna jiran dahuwarsa ba, sai dai kuma idan aka kira ku, to ku shiga, sannan idan kuka ci sai ku fice, ba tare da yin wata hira ta xebe kewa ba. Lalle wannan ya kasance yana cutar Annabi, sai yakan ji kunyar ku; Allah kuwa ba Ya jin kunyar (faxar) gaskiya. Idan kuma za ku tambaye su (wato matan Annabi) wani abu na amfani, sai ku tambaye su ta bayan shamaki. Yin wannan shi ya fi tsarki ga zukatanku da kuma zukatansu. Kuma bai kamace ku ba ku cuci Manzon Allah ko kuma ku auri matansa a bayansa har abada. Lalle (yin) wannan ya kasance abu mai girma a wurin Allah



Capítulo: Suratul Insan

Verso : 8

وَيُطۡعِمُونَ ٱلطَّعَامَ عَلَىٰ حُبِّهِۦ مِسۡكِينٗا وَيَتِيمٗا وَأَسِيرًا

Suna kuma ciyar da abinci tare da suna son sa ga miskini da maraya da kuma ribataccen yaqi



Capítulo: Suratu Abasa

Verso : 24

فَلۡيَنظُرِ ٱلۡإِنسَٰنُ إِلَىٰ طَعَامِهِۦٓ

To mutum ya yi duba zuwa ga abincinsa mana?



Capítulo: Suratu Abasa

Verso : 25

أَنَّا صَبَبۡنَا ٱلۡمَآءَ صَبّٗا

Cewa lalle Mu Muka zubo da ruwan sama zubowa



Capítulo: Suratu Abasa

Verso : 26

ثُمَّ شَقَقۡنَا ٱلۡأَرۡضَ شَقّٗا

Sannan Muka tsaga qasa tsagawa



Capítulo: Suratu Abasa

Verso : 27

فَأَنۢبَتۡنَا فِيهَا حَبّٗا

Sai Muka tsiro da qwaya daga cikinta



Capítulo: Suratu Abasa

Verso : 28

وَعِنَبٗا وَقَضۡبٗا

Da inabai da ciyayi



Capítulo: Suratu Abasa

Verso : 29

وَزَيۡتُونٗا وَنَخۡلٗا

Da zaitun da dabino



Capítulo: Suratu Abasa

Verso : 30

وَحَدَآئِقَ غُلۡبٗا

Da gonaki cike da itatuwa



Capítulo: Suratu Abasa

Verso : 31

وَفَٰكِهَةٗ وَأَبّٗا

Da kayan marmari da makiyaya



Capítulo: Suratu Abasa

Verso : 32

مَّتَٰعٗا لَّكُمۡ وَلِأَنۡعَٰمِكُمۡ

Don jin daxinku da na dabbobinku