لَيُدۡخِلَنَّهُم مُّدۡخَلٗا يَرۡضَوۡنَهُۥۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَعَلِيمٌ حَلِيمٞ
Lalle tabbas Zai shigar da su wata mashiga da za su yarda da ita. Kuma lalle Allah tabbas Masani ne, Mai hakuri
وَهُوَ ٱلَّذِيٓ أَحۡيَاكُمۡ ثُمَّ يُمِيتُكُمۡ ثُمَّ يُحۡيِيكُمۡۗ إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ لَكَفُورٞ
Shi ne kuma Wanda Ya raya ku sannan zai kashe ku sannan Ya (sake) raya ku. Lalle mutum tabbas mai yawan butulci ne
أَلَمۡ تَعۡلَمۡ أَنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا فِي ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِۚ إِنَّ ذَٰلِكَ فِي كِتَٰبٍۚ إِنَّ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٞ
Shin ba ka sani ba cewa lalle Allah Yana sane da abin da yake cikin sama da wanda yake qasa? Lalle wannan yana cikin littafi (wato Lauhul-Mahafuzu). Lalle wannan mai sauqi ne a wurin Allah
مَا قَدَرُواْ ٱللَّهَ حَقَّ قَدۡرِهِۦٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَقَوِيٌّ عَزِيزٌ
Ba su girmama Allah ba kamar yadda ya kamata su girmama Shi. Lalle Allah tabbas Qaqqarfa ne, Mabuwayi
ٱللَّهُ يَصۡطَفِي مِنَ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةِ رُسُلٗا وَمِنَ ٱلنَّاسِۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعُۢ بَصِيرٞ
Allah Yana zavar manzanni daga mala’iku kuma daga mutane. Lalle Allah Mai ji ne, Mai gani
يَعۡلَمُ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡۚ وَإِلَى ٱللَّهِ تُرۡجَعُ ٱلۡأُمُورُ
Yana sane da abin da yake gabansu da abin da yake bayansu. Zuwa ga Allah ne kawai ake komar da al’amura
ثُمَّ خَلَقۡنَا ٱلنُّطۡفَةَ عَلَقَةٗ فَخَلَقۡنَا ٱلۡعَلَقَةَ مُضۡغَةٗ فَخَلَقۡنَا ٱلۡمُضۡغَةَ عِظَٰمٗا فَكَسَوۡنَا ٱلۡعِظَٰمَ لَحۡمٗا ثُمَّ أَنشَأۡنَٰهُ خَلۡقًا ءَاخَرَۚ فَتَبَارَكَ ٱللَّهُ أَحۡسَنُ ٱلۡخَٰلِقِينَ
Sannan Muka mayar da maniyyin ya zama gudan jini, sai gudan jinin ya zama tsoka, sai Muka mai da tsokar qasusuwa, sannan Muka lulluve qasusuwan da nama, sannan kuma Muka mai da shi wata halitta daban. To albarkatun Allah sun yawaita, Wanda Shi ne Mafi gwanintar masu halitta
وَأَنزَلۡنَا مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءَۢ بِقَدَرٖ فَأَسۡكَنَّـٰهُ فِي ٱلۡأَرۡضِۖ وَإِنَّا عَلَىٰ ذَهَابِۭ بِهِۦ لَقَٰدِرُونَ
Muka kuma saukar da ruwa daga sama daidai gwargwado, sai Muka zaunar da shi a cikin qasa, kuma lalle Mu Masu iko ne a kan kawar da shi
مَا ٱتَّخَذَ ٱللَّهُ مِن وَلَدٖ وَمَا كَانَ مَعَهُۥ مِنۡ إِلَٰهٍۚ إِذٗا لَّذَهَبَ كُلُّ إِلَٰهِۭ بِمَا خَلَقَ وَلَعَلَا بَعۡضُهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖۚ سُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ عَمَّا يَصِفُونَ
Allah bai riqi wani xa ba, kuma babu wani abin bauta tare da Shi. (Da ko haka ta faru) to da kowanne abin bauta ya kevanta da abin da ya halitta, da kuma wani ya yi rinjaye a kan wani. Allah Ya tsarkaka daga abin da suke sifanta (Shi da shi)
وَإِنَّا عَلَىٰٓ أَن نُّرِيَكَ مَا نَعِدُهُمۡ لَقَٰدِرُونَ
Mu kuma lalle Masu iko ne a kan Mu nuna maka abin da Muke musu alkawari
ٱدۡفَعۡ بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُ ٱلسَّيِّئَةَۚ نَحۡنُ أَعۡلَمُ بِمَا يَصِفُونَ
Ka ingije mummunan abu da wanda ya fi kyau. Mu ne Muka fi sanin abin da suke siffata (ka da shi)
فَتَعَٰلَى ٱللَّهُ ٱلۡمَلِكُ ٱلۡحَقُّۖ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ رَبُّ ٱلۡعَرۡشِ ٱلۡكَرِيمِ
To Allah Sarki na gaskiya Ya xaukaka; babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi, (Shi ne) Ubangijin Al’arshi mai girma
وَمَن يَدۡعُ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ لَا بُرۡهَٰنَ لَهُۥ بِهِۦ فَإِنَّمَا حِسَابُهُۥ عِندَ رَبِّهِۦٓۚ إِنَّهُۥ لَا يُفۡلِحُ ٱلۡكَٰفِرُونَ
Duk wanda ya bauta wa wani abin bauta tare da Allah ba da wata hujja ba game da (wannan bautar), to sakamakonsa wajen Ubangijinsa kawai yake. Lalle su dai kafirai ba za su rabauta ba
ٱلزَّانِيَةُ وَٱلزَّانِي فَٱجۡلِدُواْ كُلَّ وَٰحِدٖ مِّنۡهُمَا مِاْئَةَ جَلۡدَةٖۖ وَلَا تَأۡخُذۡكُم بِهِمَا رَأۡفَةٞ فِي دِينِ ٱللَّهِ إِن كُنتُمۡ تُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۖ وَلۡيَشۡهَدۡ عَذَابَهُمَا طَآئِفَةٞ مِّنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Mazinaciya da mazinaci (idan suka yi zina) sai ku yi wa kowanne xaya daga cikinsu bulala xari[1], kada kuwa wani tausayi ya kama ku game da (tabbatar da hukuncin) addinin Allah idan kun kasance kuna imani da Allah da ranar lahira; kuma lalle ne wata qungiya daga cikin muminai su halarci (wurin) yi musu haddin
1- Ga waxanda ba su yi aure ba, bayan an samu shaidun gani da ido maza huxu; ko sun yi iqirari; ko ta zo da ciki ba tare da aure ba kuma ba sa-xaka ba.
ٱلزَّانِي لَا يَنكِحُ إِلَّا زَانِيَةً أَوۡ مُشۡرِكَةٗ وَٱلزَّانِيَةُ لَا يَنكِحُهَآ إِلَّا زَانٍ أَوۡ مُشۡرِكٞۚ وَحُرِّمَ ذَٰلِكَ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Mazinaci ba ya aure sai da karuwa ko mushirika, karuwa kuma ba ta aure sai da mazinaci ko mushiriki. An kuma haramta wannan ga muminai
وَٱلَّذِينَ يَرۡمُونَ ٱلۡمُحۡصَنَٰتِ ثُمَّ لَمۡ يَأۡتُواْ بِأَرۡبَعَةِ شُهَدَآءَ فَٱجۡلِدُوهُمۡ ثَمَٰنِينَ جَلۡدَةٗ وَلَا تَقۡبَلُواْ لَهُمۡ شَهَٰدَةً أَبَدٗاۚ وَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡفَٰسِقُونَ
Waxanda kuwa suke jifan mata masu kamun kai sannan ba su kawo shaidu huxu ba, sai ku yi musu bulala tamanin, kuma kada ku karvi shaidarsu har abada. Waxannan kuma su ne fasiqai
إِلَّا ٱلَّذِينَ تَابُواْ مِنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَ وَأَصۡلَحُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Sai dai waxanda suka tuba bayan wannan suka kuma gyara, to haqiqa Allah Mai gafara ne, Mai jin qai ne
وَٱلَّذِينَ يَرۡمُونَ أَزۡوَٰجَهُمۡ وَلَمۡ يَكُن لَّهُمۡ شُهَدَآءُ إِلَّآ أَنفُسُهُمۡ فَشَهَٰدَةُ أَحَدِهِمۡ أَرۡبَعُ شَهَٰدَٰتِۭ بِٱللَّهِ إِنَّهُۥ لَمِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ
Waxanda kuma suke jifan matayensu (da zina) kuma ba su da wasu shaidu sai su kansu, to shaidar xayansu ita ce ya rantsuwa da Allah sau huxu a kan cewa shi lalle yana daga masu gaskiya
وَٱلۡخَٰمِسَةُ أَنَّ لَعۡنَتَ ٱللَّهِ عَلَيۡهِ إِن كَانَ مِنَ ٱلۡكَٰذِبِينَ
(Rantsuwa) ta biyar kuwa kan cewa tsinuwar Allah ta hau kansa in ya kasance daga cikin maqaryata
وَيَدۡرَؤُاْ عَنۡهَا ٱلۡعَذَابَ أَن تَشۡهَدَ أَرۡبَعَ شَهَٰدَٰتِۭ بِٱللَّهِ إِنَّهُۥ لَمِنَ ٱلۡكَٰذِبِينَ
Kuma (abin da) zai kawar mata da azabar haddi shi ne ta yi rantsuwa da Allah sau huxu kan cewa shi lalle yana daga cikin maqaryata
وَٱلۡخَٰمِسَةَ أَنَّ غَضَبَ ٱللَّهِ عَلَيۡهَآ إِن كَانَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ
(Rantsuwa) ta biyar kuwa kan cewa lalle fushin Allah ya hau kanta idan ya kasance daga masu gaskiya
وَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَرَحۡمَتُهُۥ وَأَنَّ ٱللَّهَ تَوَّابٌ حَكِيمٌ
Ba don falalar Allah gare ku ba da rahamarsa, da kuma cewa Allah Mai karvar tuba ne, Mai hikima (to da ya kunyata maqaryaci)
لَّوۡلَا جَآءُو عَلَيۡهِ بِأَرۡبَعَةِ شُهَدَآءَۚ فَإِذۡ لَمۡ يَأۡتُواْ بِٱلشُّهَدَآءِ فَأُوْلَـٰٓئِكَ عِندَ ٱللَّهِ هُمُ ٱلۡكَٰذِبُونَ
Me ya hana su kawo shaidu huxu game da shi (qagen)? To tun da yake ba su kawo shaidun ba, to waxannan a wurin Allah su ne maqaryata
وَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَرَحۡمَتُهُۥ فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِ لَمَسَّكُمۡ فِي مَآ أَفَضۡتُمۡ فِيهِ عَذَابٌ عَظِيمٌ
Ba don kuwa falalar Allah a gare ku da rahamarsa ba a duniya da lahira, to tabbas da azaba mai girma ta shafe ku game da abin da kuka kutsa cikinsa
إِنَّ ٱلَّذِينَ يُحِبُّونَ أَن تَشِيعَ ٱلۡفَٰحِشَةُ فِي ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِۚ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ وَأَنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ
Lalle waxanda suke son yaxuwar mummunan abu a cikin waxanda suka yi imani suna da (sakamakon) azaba mai raxaxi a duniya da lahira, kuma Allah (Shi) ne Yake sane, ku ba ba ku san komai ba
وَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَرَحۡمَتُهُۥ وَأَنَّ ٱللَّهَ رَءُوفٞ رَّحِيمٞ
Ba don kuwa falalar Allah a gare ku da rahamarsa ba, da kuma cewa lalle Allah Mai tausayi ne, Mai rahama (da kun faxa cikin hallaka)
۞يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَتَّبِعُواْ خُطُوَٰتِ ٱلشَّيۡطَٰنِۚ وَمَن يَتَّبِعۡ خُطُوَٰتِ ٱلشَّيۡطَٰنِ فَإِنَّهُۥ يَأۡمُرُ بِٱلۡفَحۡشَآءِ وَٱلۡمُنكَرِۚ وَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَرَحۡمَتُهُۥ مَا زَكَىٰ مِنكُم مِّنۡ أَحَدٍ أَبَدٗا وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يُزَكِّي مَن يَشَآءُۗ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٞ
Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku bi hanyoyin Shaixan, wanda kuwa duk ya bi hanyoyin Shaixan, to lalle shi (Shaixan) umarni yake yi da aikata alfasha da abin qyama. Ba don kuma falalar Allah a gare ku da rahamarsa ba, da babu xaya daga cikinku da zai tsarkaka har abada, sai dai kuma Allah (Shi) Yake tsarkake wanda Ya ga dama, Allah kuwa Mai ji ne, Masani
وَلَا يَأۡتَلِ أُوْلُواْ ٱلۡفَضۡلِ مِنكُمۡ وَٱلسَّعَةِ أَن يُؤۡتُوٓاْ أُوْلِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينَ وَٱلۡمُهَٰجِرِينَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۖ وَلۡيَعۡفُواْ وَلۡيَصۡفَحُوٓاْۗ أَلَا تُحِبُّونَ أَن يَغۡفِرَ ٱللَّهُ لَكُمۡۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٌ
Kuma kada masu hali da wadata daga cikinku su rantse a kan qin ba da (abin hannunsu) ga makusanta da miskinai da masu hijira saboda Allah. Su kuma yi afuwa su yafe. Shin ku ba kwa so ne Allah Ya gafarta muku? Allah kuwa Mai gafara ne, Mai jin qai[1]
1- Ayar tana magana ne a kan Abubakar () lokacin da ya yi rantsuwa ba zai ci gaba da taimaka wa xan innarsa Misxahu xan Usasa ba domin ya zama cikin masu kwaza qagen da aka yi wa Nana A’isha (RAH)..
فَإِن لَّمۡ تَجِدُواْ فِيهَآ أَحَدٗا فَلَا تَدۡخُلُوهَا حَتَّىٰ يُؤۡذَنَ لَكُمۡۖ وَإِن قِيلَ لَكُمُ ٱرۡجِعُواْ فَٱرۡجِعُواْۖ هُوَ أَزۡكَىٰ لَكُمۡۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ عَلِيمٞ
To idan ba ku sami kowa a cikinsu ba to kada ku shige su har sai an yi muku izini; idan kuwa aka ce da ku ku koma sai ku koma; wannan shi ya fi tsarki a gare ku. Allah kuwa Masanin abin da kuke aikatawa ne
لَّيۡسَ عَلَيۡكُمۡ جُنَاحٌ أَن تَدۡخُلُواْ بُيُوتًا غَيۡرَ مَسۡكُونَةٖ فِيهَا مَتَٰعٞ لَّكُمۡۚ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ مَا تُبۡدُونَ وَمَا تَكۡتُمُونَ
Babu wani laifi a kanku ku shiga gidaje waxanda ba wani zaune a cikinsu, kuma akwai kayanku a cikinsu[1], kuma Allah Yana sane da abin da kuke bayyanawa da abin da kuke voyewa
1- Watau wuraren da aka tanada domin amfanin kowa da kowa, kamar xakunan karatu ko shaguna a kasuwanni.