وَلَا تَلۡبِسُواْ ٱلۡحَقَّ بِٱلۡبَٰطِلِ وَتَكۡتُمُواْ ٱلۡحَقَّ وَأَنتُمۡ تَعۡلَمُونَ
Kada kuma ku gauraya gaskiya da qarya, kuma ku voye gaskiya, alhalin kuna sane
۞وَلَقَدۡ جَآءَكُم مُّوسَىٰ بِٱلۡبَيِّنَٰتِ ثُمَّ ٱتَّخَذۡتُمُ ٱلۡعِجۡلَ مِنۢ بَعۡدِهِۦ وَأَنتُمۡ ظَٰلِمُونَ
Haqiqa Musa ya zo muka da hujjoji bayyanannu, sannan kuka bauta wa xan maraqi bayansa alhalin kuna azzalumai
وَإِذۡ أَخَذۡنَا مِيثَٰقَكُمۡ وَرَفَعۡنَا فَوۡقَكُمُ ٱلطُّورَ خُذُواْ مَآ ءَاتَيۡنَٰكُم بِقُوَّةٖ وَٱسۡمَعُواْۖ قَالُواْ سَمِعۡنَا وَعَصَيۡنَا وَأُشۡرِبُواْ فِي قُلُوبِهِمُ ٱلۡعِجۡلَ بِكُفۡرِهِمۡۚ قُلۡ بِئۡسَمَا يَأۡمُرُكُم بِهِۦٓ إِيمَٰنُكُمۡ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ
Kuma ku tuna lokacin da Muka xauki alqawari da ku, Muka kuma xaga dutsen Xuri a kanku, Muka ce: “Ku riqi abin da muka ba ku da qarfi, kuma ku saurara”. Sai suka ce: “Mun ji kuma mun sava”. Kuma aka sanya musu tsananin son bautar xan maraqi a zukatansu saboda kafircinsu. Ka ce: “Tir da abin da imaninku yake umartar ku da shi, idan har kun kasance muminai.”
ٱنظُرۡ كَيۡفَ يَفۡتَرُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَۖ وَكَفَىٰ بِهِۦٓ إِثۡمٗا مُّبِينًا
Duba ka ga yadda suke qirqirar qarya su jingina wa Allah; kuma yin haka kaxai ya isa zama wani zunubi mabayyani
إِن يَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦٓ إِلَّآ إِنَٰثٗا وَإِن يَدۡعُونَ إِلَّا شَيۡطَٰنٗا مَّرِيدٗا
Ba waxanda suke bauta wa, baya ga Allah, sai wasu gumaka masu sunan mata, kuma babu wanda suke bauta wa sai Shaixan mai taurin kai
لَّعَنَهُ ٱللَّهُۘ وَقَالَ لَأَتَّخِذَنَّ مِنۡ عِبَادِكَ نَصِيبٗا مَّفۡرُوضٗا
Allah Ya la’ance shi. Sai kuma ya ce: “Tabbas sai na samu wani kaso qayyadajje daga bayinka
مَا جَعَلَ ٱللَّهُ مِنۢ بَحِيرَةٖ وَلَا سَآئِبَةٖ وَلَا وَصِيلَةٖ وَلَا حَامٖ وَلَٰكِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ يَفۡتَرُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَۖ وَأَكۡثَرُهُمۡ لَا يَعۡقِلُونَ
Allah bai sanya wata dabba bahîra ba ko sá’iba ko wasîla ko hám[1] ba, sai dai waxanda suka kafirta suna qirqirar qarya su jingina wa Allah; kuma yawancinsu ba sa hankalta
1- Bahîra da sá’iba da wasîla da hám duk waxannan dabbobi ne da mushirikan Larabawa suke ‘yanta su ga gumakansu, ba a hawan su, ba a xora musu kaya, ba a cin namansu.
وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا أَوۡ كَذَّبَ بِـَٔايَٰتِهِۦٓۚ إِنَّهُۥ لَا يُفۡلِحُ ٱلظَّـٰلِمُونَ
Kuma ba mafi zalunci fiye da wanda ya qirqiri qarya ya jingina wa Allah, ko kuma ya qaryata ayoyinsa. Haqiqar lamarin dai su azzalumai ba za su tava rabauta ba
۞وَإِذۡ قَالَ إِبۡرَٰهِيمُ لِأَبِيهِ ءَازَرَ أَتَتَّخِذُ أَصۡنَامًا ءَالِهَةً إِنِّيٓ أَرَىٰكَ وَقَوۡمَكَ فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ
Kuma (ka tuna) lokacin da Ibrahimu ya ce da babansa Azaru: “Yanzu ka riqi gumaka a matsayin alloli? Lalle ni ina ganin ka kai da mutanenka, kuna cikin vata mabayyani.”
وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا أَوۡ قَالَ أُوحِيَ إِلَيَّ وَلَمۡ يُوحَ إِلَيۡهِ شَيۡءٞ وَمَن قَالَ سَأُنزِلُ مِثۡلَ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُۗ وَلَوۡ تَرَىٰٓ إِذِ ٱلظَّـٰلِمُونَ فِي غَمَرَٰتِ ٱلۡمَوۡتِ وَٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ بَاسِطُوٓاْ أَيۡدِيهِمۡ أَخۡرِجُوٓاْ أَنفُسَكُمُۖ ٱلۡيَوۡمَ تُجۡزَوۡنَ عَذَابَ ٱلۡهُونِ بِمَا كُنتُمۡ تَقُولُونَ عَلَى ٱللَّهِ غَيۡرَ ٱلۡحَقِّ وَكُنتُمۡ عَنۡ ءَايَٰتِهِۦ تَسۡتَكۡبِرُونَ
Kuma wane ne ya fi zalunci kamar wanda ya qagi qarya ya jingina wa Allah, ko kuma ya ce: “An yiwo mini wahayi,” alhalin kuma ba a yi masa wahayin komai ba, da kuma wanda ya ce: “Zan saukar da irin abin da Allah Ya saukar?” Kuma da za ka ga lokacin da kafirai suke cikin magagin mutuwa, mala’iku kuma suna miqa hannayensu suna cewa: “Ku fito da rayukanku (da kanku), a yau ne za a saka muku da azabar wulaqanci, saboda irin abin da kuke faxa game da Allah wanda ba gaskiya ba, kuma kun kasance kuna girman kai game da ayoyinsa.”
وَلَقَدۡ جِئۡتُمُونَا فُرَٰدَىٰ كَمَا خَلَقۡنَٰكُمۡ أَوَّلَ مَرَّةٖ وَتَرَكۡتُم مَّا خَوَّلۡنَٰكُمۡ وَرَآءَ ظُهُورِكُمۡۖ وَمَا نَرَىٰ مَعَكُمۡ شُفَعَآءَكُمُ ٱلَّذِينَ زَعَمۡتُمۡ أَنَّهُمۡ فِيكُمۡ شُرَكَـٰٓؤُاْۚ لَقَد تَّقَطَّعَ بَيۡنَكُمۡ وَضَلَّ عَنكُم مَّا كُنتُمۡ تَزۡعُمُونَ
Kuma lalle haqiqa kun zo Mana xaixai kamar yadda Muka halicce ku a karon fari, kuma kun baro abin da Muka ba ku a bayanku (a duniya), kuma har yanzu ba Ma ganin masu ceton ku waxanda kuka riya cewa su ne abokanan tarayyarku. Lalle haqiqa dangantakar da take tsakaninku ta yanke, kuma abin da kuke riyawa ya vace muku
وَلَا تَسُبُّواْ ٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ فَيَسُبُّواْ ٱللَّهَ عَدۡوَۢا بِغَيۡرِ عِلۡمٖۗ كَذَٰلِكَ زَيَّنَّا لِكُلِّ أُمَّةٍ عَمَلَهُمۡ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّهِم مَّرۡجِعُهُمۡ فَيُنَبِّئُهُم بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Kuma kada ku zagi waxanda suke bauta wa ba Allah ba, sai su zagi Allah saboda zalunci, ba tare da sanin (girmansa) ba. Kamar haka ne Muka qawata wa kowace al’umma ayyukansu (nagari da munana), sannan zuwa ga Ubangijinsu ne makomarsu take, sai Ya ba su labarin abin da suka kasance suna aikatawa
وَجَٰوَزۡنَا بِبَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ ٱلۡبَحۡرَ فَأَتَوۡاْ عَلَىٰ قَوۡمٖ يَعۡكُفُونَ عَلَىٰٓ أَصۡنَامٖ لَّهُمۡۚ قَالُواْ يَٰمُوسَى ٱجۡعَل لَّنَآ إِلَٰهٗا كَمَا لَهُمۡ ءَالِهَةٞۚ قَالَ إِنَّكُمۡ قَوۡمٞ تَجۡهَلُونَ
Kuma sai Muka tsallakar da Banu Isra’ila kogi, sai suka tarar da waxansu mutane da suka duqufa a kan (bautar) gumakansu, suka ce: “Ya kai Musa, ka sa mana wani abin bauta, irin yadda waxannan suke da abubuwan bauta.” Sai ya ce: “Lalle ku mutane ne da kuke da jahilci
إِنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ مُتَبَّرٞ مَّا هُمۡ فِيهِ وَبَٰطِلٞ مَّا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
“Lalle waxannan abin da suke cikinsa halaka ne, kuma abin da suke aikatawa varna ce.”
وَٱتَّخَذَ قَوۡمُ مُوسَىٰ مِنۢ بَعۡدِهِۦ مِنۡ حُلِيِّهِمۡ عِجۡلٗا جَسَدٗا لَّهُۥ خُوَارٌۚ أَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّهُۥ لَا يُكَلِّمُهُمۡ وَلَا يَهۡدِيهِمۡ سَبِيلًاۘ ٱتَّخَذُوهُ وَكَانُواْ ظَٰلِمِينَ
Mutanen Musa kuma a bayansa sun qera wani xan maraqi daga kayan adonsu mai surar jiki yana wata qara (don su bauta masa). Shin ba su ga cewa ba ya yi musu Magana, kuma ba ya iya shiryar da su wani tafarki? Sun riqe shi (a matsayin abin bauta), kuma sun tabbata azzalumai
وَلَمَّا سُقِطَ فِيٓ أَيۡدِيهِمۡ وَرَأَوۡاْ أَنَّهُمۡ قَدۡ ضَلُّواْ قَالُواْ لَئِن لَّمۡ يَرۡحَمۡنَا رَبُّنَا وَيَغۡفِرۡ لَنَا لَنَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ
Kuma lokacin da suka yi nadama, suka gane cewa sun vata, sai suka ce: “Matuqar Ubangijinmu bai ji qan mu ba, kuma bai gafarta mana ba, lalle za mu kasance cikin hasararru.”
إِنَّ ٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ ٱلۡعِجۡلَ سَيَنَالُهُمۡ غَضَبٞ مِّن رَّبِّهِمۡ وَذِلَّةٞ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۚ وَكَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُفۡتَرِينَ
Lalle waxannan da suka riqi xan maraqi (abin bauta) fushin Ubangijinsu zai same su da qasqanci a cikin rayuwar duniya. Kuma kamar haka ne Muke saka wa masu qage
إِنَّ ٱلَّذِينَ تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ عِبَادٌ أَمۡثَالُكُمۡۖ فَٱدۡعُوهُمۡ فَلۡيَسۡتَجِيبُواْ لَكُمۡ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Lalle waxanda kuke kira ba Allah ba bayi ne kamarku, to ku kirawo su mana, sai su kuma su amsa muku idan kun kasance masu gaskiya ne
وَٱلَّذِينَ تَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦ لَا يَسۡتَطِيعُونَ نَصۡرَكُمۡ وَلَآ أَنفُسَهُمۡ يَنصُرُونَ
Waxanda kuke kira ba Shi ba kuwa, ba za su iya taimakon ku ba, kuma ba za su iya taimaka wa kawunansu ba
وَإِن تَدۡعُوهُمۡ إِلَى ٱلۡهُدَىٰ لَا يَسۡمَعُواْۖ وَتَرَىٰهُمۡ يَنظُرُونَ إِلَيۡكَ وَهُمۡ لَا يُبۡصِرُونَ
Kuma idan da za ku yi kiran su zuwa ga shiriya, to fa ba za su ji ba; kuma za ka gan su suna kallon ka, alhali kuwa ba sa gani
وَيَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَضُرُّهُمۡ وَلَا يَنفَعُهُمۡ وَيَقُولُونَ هَـٰٓؤُلَآءِ شُفَعَـٰٓؤُنَا عِندَ ٱللَّهِۚ قُلۡ أَتُنَبِّـُٔونَ ٱللَّهَ بِمَا لَا يَعۡلَمُ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَلَا فِي ٱلۡأَرۡضِۚ سُبۡحَٰنَهُۥ وَتَعَٰلَىٰ عَمَّا يُشۡرِكُونَ
Suna kuma bauta wa wani ba Allah ba, abin da ba zai cutar da su ba ba kuma zai amfane su ba, suna kuma cewa: “Waxannan su ne masu ceton mu a wurin Allah.” Ka ce: “Shin yanzu za ku ba Allah labarin abin da bai sani ba ne a cikin sammai ko kuma a bayan qasa? Tsarki ya tabbata a gare Shi Ya kuma xaukaka daga abin da suke shirka da Shi.”
قُلۡ إِنَّ ٱلَّذِينَ يَفۡتَرُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَ لَا يُفۡلِحُونَ
Ka ce: “Lalle waxanda suke qaga wa Allah qarya ba za su rabauta ba.”
مَتَٰعٞ فِي ٱلدُّنۡيَا ثُمَّ إِلَيۡنَا مَرۡجِعُهُمۡ ثُمَّ نُذِيقُهُمُ ٱلۡعَذَابَ ٱلشَّدِيدَ بِمَا كَانُواْ يَكۡفُرُونَ
Jin daxi ne kawai a cikin duniya, sannan kuma gare Mu ne makomarsu take, sannan Mu xanxana musu azaba mai tsanani saboda abin da suka zamanto suna yi na kafirci
وَمَا ظَلَمۡنَٰهُمۡ وَلَٰكِن ظَلَمُوٓاْ أَنفُسَهُمۡۖ فَمَآ أَغۡنَتۡ عَنۡهُمۡ ءَالِهَتُهُمُ ٱلَّتِي يَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ مِن شَيۡءٖ لَّمَّا جَآءَ أَمۡرُ رَبِّكَۖ وَمَا زَادُوهُمۡ غَيۡرَ تَتۡبِيبٖ
Ba Mu kuwa zalunce su ba, sai dai su ne suka zalunci kansu; allolinsu da suke bauta wa ba Allah ba, ba su maganta musu komai ba, lokacin da umarnin Ubangijinka ya zo; ba su kuwa qara musu komai ba in ban da halaka
أَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَسَالَتۡ أَوۡدِيَةُۢ بِقَدَرِهَا فَٱحۡتَمَلَ ٱلسَّيۡلُ زَبَدٗا رَّابِيٗاۖ وَمِمَّا يُوقِدُونَ عَلَيۡهِ فِي ٱلنَّارِ ٱبۡتِغَآءَ حِلۡيَةٍ أَوۡ مَتَٰعٖ زَبَدٞ مِّثۡلُهُۥۚ كَذَٰلِكَ يَضۡرِبُ ٱللَّهُ ٱلۡحَقَّ وَٱلۡبَٰطِلَۚ فَأَمَّا ٱلزَّبَدُ فَيَذۡهَبُ جُفَآءٗۖ وَأَمَّا مَا يَنفَعُ ٱلنَّاسَ فَيَمۡكُثُ فِي ٱلۡأَرۡضِۚ كَذَٰلِكَ يَضۡرِبُ ٱللَّهُ ٱلۡأَمۡثَالَ
Ya saukar da ruwa daga sama, sai magudanai suka kwarara daidai gwargwadon abin da za su iya xauka, sai (shi ruwan) mai kwarara ya xauko kumfa a samansa. Akwai kuma wata kumfar kamarta daga abin da kuke narkawa a wuta don samun abin ado ko kuwa (qera) abin jin daxi. Kamar haka ne Allah Yake ba da misalin gaskiya da varna. To amma kumfar sai ta tafi ta bi iska; amma kuma abin da zai amfani mutane sai ya zauna a qasa. Kamar haka ne Allah Yake ba da misali
إِنَّمَا يَفۡتَرِي ٱلۡكَذِبَ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِۖ وَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡكَٰذِبُونَ
Waxanda ba sa yin imani da ayoyin Allah su ne kawai suke qirqirar qarya; kuma waxannan su ne maqaryata
وَلَا تَقُولُواْ لِمَا تَصِفُ أَلۡسِنَتُكُمُ ٱلۡكَذِبَ هَٰذَا حَلَٰلٞ وَهَٰذَا حَرَامٞ لِّتَفۡتَرُواْ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ يَفۡتَرُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَ لَا يُفۡلِحُونَ
Kuma saboda abin da harsunanku suke bayyanawa na qarya kada ku riqa cewa, wannan halal ne, wannan kuma haram ne, don ku yi wa Allah qarya. Lalle waxanda suke qirqira wa Allah qarya ba sa rabauta
قُلِ ٱدۡعُواْ ٱلَّذِينَ زَعَمۡتُم مِّن دُونِهِۦ فَلَا يَمۡلِكُونَ كَشۡفَ ٱلضُّرِّ عَنكُمۡ وَلَا تَحۡوِيلًا
Ka ce (da su): “Ku kirawo waxanda kuka riya (cewa su ne iyayen gijinku) ba Shi ba, to ba su da ikon yaye muku cuta ko juyar da ita.”
أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ يَبۡتَغُونَ إِلَىٰ رَبِّهِمُ ٱلۡوَسِيلَةَ أَيُّهُمۡ أَقۡرَبُ وَيَرۡجُونَ رَحۡمَتَهُۥ وَيَخَافُونَ عَذَابَهُۥٓۚ إِنَّ عَذَابَ رَبِّكَ كَانَ مَحۡذُورٗا
Waxancan da suke bauta wa[1], su ma suna neman hanya ne zuwa ga Ubangijinsu, a cikinsu wa zai fi kusanci? Suna kuma qaunar rahamarsa, kuma suna tsoron azabarsa. Lalle azabar Ubangijinka ta kasance abar tsoro ce
1- Watau kamar mala’iku ko annabawa ko salihan bayi.
وَإِذَا مَسَّكُمُ ٱلضُّرُّ فِي ٱلۡبَحۡرِ ضَلَّ مَن تَدۡعُونَ إِلَّآ إِيَّاهُۖ فَلَمَّا نَجَّىٰكُمۡ إِلَى ٱلۡبَرِّ أَعۡرَضۡتُمۡۚ وَكَانَ ٱلۡإِنسَٰنُ كَفُورًا
Idan kuma bala’i ya same ku a cikin kogi sai duk waxanda kuke kira su vace (muku) sai Shi kawai; sannan lokacin da Ya tserar da ku zuwa sarari sai kuka bijire. Kai mutum ya tabbata butulu!