Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 249

فَلَمَّا فَصَلَ طَالُوتُ بِٱلۡجُنُودِ قَالَ إِنَّ ٱللَّهَ مُبۡتَلِيكُم بِنَهَرٖ فَمَن شَرِبَ مِنۡهُ فَلَيۡسَ مِنِّي وَمَن لَّمۡ يَطۡعَمۡهُ فَإِنَّهُۥ مِنِّيٓ إِلَّا مَنِ ٱغۡتَرَفَ غُرۡفَةَۢ بِيَدِهِۦۚ فَشَرِبُواْ مِنۡهُ إِلَّا قَلِيلٗا مِّنۡهُمۡۚ فَلَمَّا جَاوَزَهُۥ هُوَ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَهُۥ قَالُواْ لَا طَاقَةَ لَنَا ٱلۡيَوۡمَ بِجَالُوتَ وَجُنُودِهِۦۚ قَالَ ٱلَّذِينَ يَظُنُّونَ أَنَّهُم مُّلَٰقُواْ ٱللَّهِ كَم مِّن فِئَةٖ قَلِيلَةٍ غَلَبَتۡ فِئَةٗ كَثِيرَةَۢ بِإِذۡنِ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ مَعَ ٱلصَّـٰبِرِينَ

To yayin da Xalutu ya fita (bayan gari) da rundunarsa, sai ya ce: “Lalle Allah zai jarrabe ku da wata qorama, to duk wanda ya sha daga gare ta, to ba ya tare da ni, duk wanda kuwa bai sha ba, to wannan yana tare da ni, sai dai wanda ya kamfata sau xaya da (tafin) hannunsa.” Gaba xayansu sai suka sha daga cikinta sai ‘yan kaxan daga cikinsu (su ne ba su sha ba). To yayin da ya qetare shi, shi da waxanda suka yi imani tare da shi, sai suka ce: “A yau kam ba mu da iko wajen fuskantar Jalutu da rundunarsa.” Sai waxanda suke da yaqinin cewa za su haxu da Allah suka ce: “Sau da yawa wata runduna ‘yan kaxan takan yi rinjaye a kan wata runduna mai yawa da izinin Allah. Kuma Allah Yana tare da masu haquri.”



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 250

وَلَمَّا بَرَزُواْ لِجَالُوتَ وَجُنُودِهِۦ قَالُواْ رَبَّنَآ أَفۡرِغۡ عَلَيۡنَا صَبۡرٗا وَثَبِّتۡ أَقۡدَامَنَا وَٱنصُرۡنَا عَلَى ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Kuma yayin da suka yi fito-na-fito da Jalutu da rundunarsa, sai suka ce: “Ya Ubangijinmu, Ka zubo mana haquri na musamman, kuma Ka tabbatar da dugaduganmu, kuma Ka taimake mu a kan mutane kafirai.”



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 251

فَهَزَمُوهُم بِإِذۡنِ ٱللَّهِ وَقَتَلَ دَاوُۥدُ جَالُوتَ وَءَاتَىٰهُ ٱللَّهُ ٱلۡمُلۡكَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَعَلَّمَهُۥ مِمَّا يَشَآءُۗ وَلَوۡلَا دَفۡعُ ٱللَّهِ ٱلنَّاسَ بَعۡضَهُم بِبَعۡضٖ لَّفَسَدَتِ ٱلۡأَرۡضُ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ ذُو فَضۡلٍ عَلَى ٱلۡعَٰلَمِينَ

Sai suka murqushe su da izinin Allah, kuma Dawudu ya kashe Jalutu, sai Allah Ya ba shi mulki da hikima, kuma Ya sanar da shi irin abin da Ya ga dama. Ba don yadda Allah Yake kare wani sashin mutane da wani sashi ba, to lalle da qasa ta lalace, sai dai kuma Allah Ma’abocin falala ne ga talikai