Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 110

وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَۚ وَمَا تُقَدِّمُواْ لِأَنفُسِكُم مِّنۡ خَيۡرٖ تَجِدُوهُ عِندَ ٱللَّهِۗ إِنَّ ٱللَّهَ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ

Kuma ku tsayar da salla ku kuma ba da zakka; kuma duk abin da kuka aikata na alheri domin kawunanku za ku same shi a wajen Allah. Lalle Allah Mai ganin abin da kuke aikatawa ne



Capítulo: Suratu Yunus

Verso : 26

۞لِّلَّذِينَ أَحۡسَنُواْ ٱلۡحُسۡنَىٰ وَزِيَادَةٞۖ وَلَا يَرۡهَقُ وُجُوهَهُمۡ قَتَرٞ وَلَا ذِلَّةٌۚ أُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَنَّةِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ

Waxanda suka kyautata aiki suna da sakamako mafi kyau (watau Aljanna) da kuma qari[1]. Wani qunci da qasqanci kuma ba za su same su ba. Waxannan su ne ‘yan Aljanna; su masu dawwama ne a cikinta


1- Watau shi ne ganin Fuskar Allah () bayan shigarsu Aljanna. Duba Muslim #181.


Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 30

۞وَقِيلَ لِلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْ مَاذَآ أَنزَلَ رَبُّكُمۡۚ قَالُواْ خَيۡرٗاۗ لِّلَّذِينَ أَحۡسَنُواْ فِي هَٰذِهِ ٱلدُّنۡيَا حَسَنَةٞۚ وَلَدَارُ ٱلۡأٓخِرَةِ خَيۡرٞۚ وَلَنِعۡمَ دَارُ ٱلۡمُتَّقِينَ

Aka kuma ce da waxanda suka kiyaye dokokin (Allah): “Me Ubangijinku Ya sauqar?” Suka ce: “Alheri.” Waxanda suka kyautata a wannan duniya suna da kyakkyawar (rayuwa). Lalle kuma gidan lahira shi ya fi alheri. Madalla da gidan masu taqawa



Capítulo: Suratul Kahf 

Verso : 30

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ إِنَّا لَا نُضِيعُ أَجۡرَ مَنۡ أَحۡسَنَ عَمَلًا

Lalle waxanda suka yi imani suka kuma yi aiki nagari tabbas Mu ba ma tozarta ladan wanda ya kyautata aiki



Capítulo: Suratul Kahf 

Verso : 31

أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ جَنَّـٰتُ عَدۡنٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهِمُ ٱلۡأَنۡهَٰرُ يُحَلَّوۡنَ فِيهَا مِنۡ أَسَاوِرَ مِن ذَهَبٖ وَيَلۡبَسُونَ ثِيَابًا خُضۡرٗا مِّن سُندُسٖ وَإِسۡتَبۡرَقٖ مُّتَّكِـِٔينَ فِيهَا عَلَى ٱلۡأَرَآئِكِۚ نِعۡمَ ٱلثَّوَابُ وَحَسُنَتۡ مُرۡتَفَقٗا

Waxannan suna da gidajen Aljanna na dawwama waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, ana yi musu ado a cikinsu (watau gidajen) da awarwaro na zinare, suna kuma sanya tufafi koraye na alharini mai shara-shara da mai kauri, suna kwance a kan gadaje. Madalla (da wannan) lada, wurin hutu kuma ya kyautata



Capítulo: Suratun Namli

Verso : 89

مَن جَآءَ بِٱلۡحَسَنَةِ فَلَهُۥ خَيۡرٞ مِّنۡهَا وَهُم مِّن فَزَعٖ يَوۡمَئِذٍ ءَامِنُونَ

Duk waxanda suka zo da kyakkyawan (aiki), to suna da (lada) fiye da shi, kuma su amintattu ne daga firgitar wannan ranar



Capítulo: Suratul Qasas

Verso : 84

مَن جَآءَ بِٱلۡحَسَنَةِ فَلَهُۥ خَيۡرٞ مِّنۡهَاۖ وَمَن جَآءَ بِٱلسَّيِّئَةِ فَلَا يُجۡزَى ٱلَّذِينَ عَمِلُواْ ٱلسَّيِّـَٔاتِ إِلَّا مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Duk wanda ya zo da kyakkyawan aiki, to yana da (lada) fiye da aikinsa; wanda kuma ya zo da mummunan aiki, to ba za a saka wa waxanda suka aikata munanan ayyuka ba face daidai da abin da suka kasance suna aikatawa



Capítulo: Suratur Rahman

Verso : 60

هَلۡ جَزَآءُ ٱلۡإِحۡسَٰنِ إِلَّا ٱلۡإِحۡسَٰنُ

Shin akwai wani sakamako na kyautatawa in ba kyautatawa ba?



Capítulo: Suratul Muzzammil

Verso : 20

۞إِنَّ رَبَّكَ يَعۡلَمُ أَنَّكَ تَقُومُ أَدۡنَىٰ مِن ثُلُثَيِ ٱلَّيۡلِ وَنِصۡفَهُۥ وَثُلُثَهُۥ وَطَآئِفَةٞ مِّنَ ٱلَّذِينَ مَعَكَۚ وَٱللَّهُ يُقَدِّرُ ٱلَّيۡلَ وَٱلنَّهَارَۚ عَلِمَ أَن لَّن تُحۡصُوهُ فَتَابَ عَلَيۡكُمۡۖ فَٱقۡرَءُواْ مَا تَيَسَّرَ مِنَ ٱلۡقُرۡءَانِۚ عَلِمَ أَن سَيَكُونُ مِنكُم مَّرۡضَىٰ وَءَاخَرُونَ يَضۡرِبُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ يَبۡتَغُونَ مِن فَضۡلِ ٱللَّهِ وَءَاخَرُونَ يُقَٰتِلُونَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۖ فَٱقۡرَءُواْ مَا تَيَسَّرَ مِنۡهُۚ وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ وَأَقۡرِضُواْ ٱللَّهَ قَرۡضًا حَسَنٗاۚ وَمَا تُقَدِّمُواْ لِأَنفُسِكُم مِّنۡ خَيۡرٖ تَجِدُوهُ عِندَ ٱللَّهِ هُوَ خَيۡرٗا وَأَعۡظَمَ أَجۡرٗاۚ وَٱسۡتَغۡفِرُواْ ٱللَّهَۖ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمُۢ

Lalle Ubangijinka Yana sane da cewa kai kana tsayawa qasa da kashi biyu cikin uku na dare, da kuma rabinsa, da kuma xaya bisa ukunsa, kai da wata jama’ar da take tare da kai. Allah ne kuma Yake qaddara dare da rana. Ya san kuma cewa, ba za ku iya qididdige (sa’o’insa) ba, don haka sai Ya yafe muku; to sai ku karanta abin da ya sauqaqa daga Alqur’ani. Ya san cewa daga cikinku akwai waxanda za su kasance marasa lafiya, waxansu kuma suna tafiya a bayan qasa don fatauci suna neman falala daga Allah, waxansu kuma suna yin yaqi saboda Allah; to sai ku karanta abin da ya sauqaqa daga gare shi (Alqur’ani). Ku kuma tsayar da salla, ku kuma ba da zakka, kuma ku bai wa Allah rance kyakkyawa[1]. Kuma abin da kuka gabatar wa kanku na wani alheri, to za ku same shi wurin Allah, shi ya fi alheri ya kuma fi girman lada. Ku kuma nemi gafarar Allah; lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai


1- Watau su ciyar da dukiyoyinsu don Allah wuraren da suka dace.


Capítulo: Suratuz Zalzala

Verso : 7

فَمَن يَعۡمَلۡ مِثۡقَالَ ذَرَّةٍ خَيۡرٗا يَرَهُۥ

To duk wanda ya yi aikin alheri daidai da zarra zai gan shi