۞وَقَالَ ٱلَّذِينَ لَا يَرۡجُونَ لِقَآءَنَا لَوۡلَآ أُنزِلَ عَلَيۡنَا ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ أَوۡ نَرَىٰ رَبَّنَاۗ لَقَدِ ٱسۡتَكۡبَرُواْ فِيٓ أَنفُسِهِمۡ وَعَتَوۡ عُتُوّٗا كَبِيرٗا
Waxanda kuma ba sa tsammanin haxuwa da Mu suka ce: “Me ya hana a saukar mana da mala’iku ko kuma mu ga Ubangijinmu?” Haqiqa lalle sun yi girman kai don (suna) ji da kawunansu, suka kuma yi tsaurin kai babba qwarai da gaske
يَوۡمَ يَرَوۡنَ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةَ لَا بُشۡرَىٰ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُجۡرِمِينَ وَيَقُولُونَ حِجۡرٗا مَّحۡجُورٗا
Ranar da za su ga mala’iku[1] a wannan ranar babu wani farin ciki ga masu laifi, za kuma su riqa cewa: “(Albishir daga Allah) haramun ne abin haramtawa ne (a gare su)”
1- Watau ranar mutuwarsu ko a cikin qaburburansu da ranar da za a kora su domin yi musu hisabi.
وَقَدِمۡنَآ إِلَىٰ مَا عَمِلُواْ مِنۡ عَمَلٖ فَجَعَلۡنَٰهُ هَبَآءٗ مَّنثُورًا
Muka kuma gabato zuwa ga duk wani aiki da suka yi, sai Muka mai da shi qura abar xaixaitawa
أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَنَّةِ يَوۡمَئِذٍ خَيۡرٞ مُّسۡتَقَرّٗا وَأَحۡسَنُ مَقِيلٗا
‘Yan Aljanna a wannan ranar su suka fi kyakkyawan mazauni kuma suka fi kyawon wurin barcin qailula[1]
1- Domin za a gama hisabi gabanin lokacin azahar, har ‘yan Aljanna za su shige ta su riski lokacin qailula a cikinta.
وَيَوۡمَ تَشَقَّقُ ٱلسَّمَآءُ بِٱلۡغَمَٰمِ وَنُزِّلَ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ تَنزِيلًا
Kuma (ka tuna) ranar da sama za ta kekkece da girgije, kuma a saukar da mala’iku gungu-gungu
ٱلۡمُلۡكُ يَوۡمَئِذٍ ٱلۡحَقُّ لِلرَّحۡمَٰنِۚ وَكَانَ يَوۡمًا عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ عَسِيرٗا
Mulki tabbatacce a wannan ranar na (Allah) Mai rahama ne. Kuma ta kasance rana ce mawuyaciya ga kafurai
وَيَوۡمَ يَعَضُّ ٱلظَّالِمُ عَلَىٰ يَدَيۡهِ يَقُولُ يَٰلَيۡتَنِي ٱتَّخَذۡتُ مَعَ ٱلرَّسُولِ سَبِيلٗا
(Ka tuna) kuma ranar da azzalumi zai riqa cizon yatsunsa yana cewa: “Ina ma na bi hanya tare da Manzo!
يَٰوَيۡلَتَىٰ لَيۡتَنِي لَمۡ أَتَّخِذۡ فُلَانًا خَلِيلٗا
“Kaicona ina ma da ban riqi wane aboki ba!
لَّقَدۡ أَضَلَّنِي عَنِ ٱلذِّكۡرِ بَعۡدَ إِذۡ جَآءَنِيۗ وَكَانَ ٱلشَّيۡطَٰنُ لِلۡإِنسَٰنِ خَذُولٗا
“Haqiqa ya vatar da ni daga bin Alqur’ani, bayan ya zo mini.” Shaixan kuwa ya kasance mai tavar da mutum ne
وَقَالَ ٱلرَّسُولُ يَٰرَبِّ إِنَّ قَوۡمِي ٱتَّخَذُواْ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانَ مَهۡجُورٗا
Manzo kuma ya ce: “Ya Ubangijina, lalle mutanena sun riqi wannan Alqur’ani abin qaurace wa[1].”
1- Watau ta hanyar guje wa sauraron sa da rashin karanta shi da aiki da koyarwarsa.
وَكَذَٰلِكَ جَعَلۡنَا لِكُلِّ نَبِيٍّ عَدُوّٗا مِّنَ ٱلۡمُجۡرِمِينَۗ وَكَفَىٰ بِرَبِّكَ هَادِيٗا وَنَصِيرٗا
Kamar haka Muka sanya wa kowanne annabi abokan gaba daga masu laifi, kuma Ubangijinka Ya ishe ka Mai shiryarwa Mai taimako
وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَوۡلَا نُزِّلَ عَلَيۡهِ ٱلۡقُرۡءَانُ جُمۡلَةٗ وَٰحِدَةٗۚ كَذَٰلِكَ لِنُثَبِّتَ بِهِۦ فُؤَادَكَۖ وَرَتَّلۡنَٰهُ تَرۡتِيلٗا
Waxanda kuma suka kafirta suka ce: “Me ya hana a saukar masa da Alqur’ani gaba xaya, a lokaci guda[1]?” Kamar haka ne (Muke saukar da shi kaxan-kaxan) don Mu tabbatar da zuciyarka da shi, Muka kuma karantar (da kai) shi daki-daki
1- Watau kamar yadda aka saukar da littafin Attaura ko Linjila.
وَلَا يَأۡتُونَكَ بِمَثَلٍ إِلَّا جِئۡنَٰكَ بِٱلۡحَقِّ وَأَحۡسَنَ تَفۡسِيرًا
Kuma ba za su zo maka da wani misali ba (na qalu-bale) sai Mun zo maka da gaskiya, kuma da mafi kyan bayani
ٱلَّذِينَ يُحۡشَرُونَ عَلَىٰ وُجُوهِهِمۡ إِلَىٰ جَهَنَّمَ أُوْلَـٰٓئِكَ شَرّٞ مَّكَانٗا وَأَضَلُّ سَبِيلٗا
Waxanda za a tashe su zuwa wutar Jahannama a kan fuskokinsu, waxannan su suka fi mummunan matsayi kuma mafiya vatacciyar hanya
وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ وَجَعَلۡنَا مَعَهُۥٓ أَخَاهُ هَٰرُونَ وَزِيرٗا
Haqiqa kuma Mun bai wa Musa Littafi muka kuma sanya xan’uwansa Haruna tare da shi a matsayin Waziri
فَقُلۡنَا ٱذۡهَبَآ إِلَى ٱلۡقَوۡمِ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا فَدَمَّرۡنَٰهُمۡ تَدۡمِيرٗا
Sai Muka ce: “Ku tafi zuwa ga mutanen da suka qaryata ayoyinmu, sai Muka hallaka su hallakarwa mai tsanani!”
وَقَوۡمَ نُوحٖ لَّمَّا كَذَّبُواْ ٱلرُّسُلَ أَغۡرَقۡنَٰهُمۡ وَجَعَلۡنَٰهُمۡ لِلنَّاسِ ءَايَةٗۖ وَأَعۡتَدۡنَا لِلظَّـٰلِمِينَ عَذَابًا أَلِيمٗا
Mutanen Nuhu kuma lokacin da suka qaryata manzanni[1] sai Muka nutsar da su, Muka kuma sanya su wa’azi ga mutane, kuma Muka tanadi azaba mai raxaxi ga azzalumai
1- Watau ta hanyar qaryata Annabi Nuhu(), domin saqon duk manzanni guda xaya ne, shi ne kaxaita Allah da bauta.
وَعَادٗا وَثَمُودَاْ وَأَصۡحَٰبَ ٱلرَّسِّ وَقُرُونَۢا بَيۡنَ ذَٰلِكَ كَثِيرٗا
Kuma (Muka hallakar da) Adawa da Samudawa da kuma mutanen (rijiyar) Rassu, da kuma wasu al’ummu masu yawa tsakanin hakan
وَكُلّٗا ضَرَبۡنَا لَهُ ٱلۡأَمۡثَٰلَۖ وَكُلّٗا تَبَّرۡنَا تَتۡبِيرٗا
Kowannensu kuwa Mun ba shi misalai; kuma kowannensu Mun hallaka shi mummunar hallakawa
وَلَقَدۡ أَتَوۡاْ عَلَى ٱلۡقَرۡيَةِ ٱلَّتِيٓ أُمۡطِرَتۡ مَطَرَ ٱلسَّوۡءِۚ أَفَلَمۡ يَكُونُواْ يَرَوۡنَهَاۚ بَلۡ كَانُواْ لَا يَرۡجُونَ نُشُورٗا
Haqiqa kuma (su mutanen Makka) sun bi ta alqaryar nan wadda aka yi wa ruwan azaba. Shin ba su kasance suna ganin ta ba ne? Ba haka ba ne, sun dai kasance ne ba sa tsammanin tashin alqiyama
وَإِذَا رَأَوۡكَ إِن يَتَّخِذُونَكَ إِلَّا هُزُوًا أَهَٰذَا ٱلَّذِي بَعَثَ ٱللَّهُ رَسُولًا
Idan kuma suka gan ka ba sa riqon ka sai abin yi wa izgili, (suna cewa): “Yanzu wannan ne wanda Allah ya aiko Manzo?
إِن كَادَ لَيُضِلُّنَا عَنۡ ءَالِهَتِنَا لَوۡلَآ أَن صَبَرۡنَا عَلَيۡهَاۚ وَسَوۡفَ يَعۡلَمُونَ حِينَ يَرَوۡنَ ٱلۡعَذَابَ مَنۡ أَضَلُّ سَبِيلًا
“Lalle saura qiris ya vatar da mu daga ababen bautarmu, ba don mun yi haquri a kansu ba.” Ba da daxewa ba kuwa za su san wanda ya fi vatan hanya yayin da za su ga azaba
أَرَءَيۡتَ مَنِ ٱتَّخَذَ إِلَٰهَهُۥ هَوَىٰهُ أَفَأَنتَ تَكُونُ عَلَيۡهِ وَكِيلًا
Shin ka ga wanda ya mayar da son zuciyarsa (shi ne) abin bautarsa, to yanzu kai za ka zama mai kiyaye shi (daga bin son zuciyarsa)?
أَمۡ تَحۡسَبُ أَنَّ أَكۡثَرَهُمۡ يَسۡمَعُونَ أَوۡ يَعۡقِلُونَۚ إِنۡ هُمۡ إِلَّا كَٱلۡأَنۡعَٰمِ بَلۡ هُمۡ أَضَلُّ سَبِيلًا
Ko kuwa kana tsammanin cewa yawancinsu suna ji ne (na fahimta) ko suna hankalta? Ai su ba wasu ba ne illa kamar dabbobi; a’a su ne ma suka fi (dabbobi) vace hanya
أَلَمۡ تَرَ إِلَىٰ رَبِّكَ كَيۡفَ مَدَّ ٱلظِّلَّ وَلَوۡ شَآءَ لَجَعَلَهُۥ سَاكِنٗا ثُمَّ جَعَلۡنَا ٱلشَّمۡسَ عَلَيۡهِ دَلِيلٗا
Shin ba ka ganin (irin aikin) Ubangijinka yadda ya shimfixa inuwa, da kuwa ya ga dama da sai ya sanya ta a tsaye cak, sannan Muka sanya rana dalilin samuwarta (inuwar)
ثُمَّ قَبَضۡنَٰهُ إِلَيۡنَا قَبۡضٗا يَسِيرٗا
Sannan Muka riqa janye ta da kaxan-kaxan[1]
1- Watau tana raguwa gwargwadon xagawar rana, har ya zamanto ta gushe gaba xaya.
وَهُوَ ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلَّيۡلَ لِبَاسٗا وَٱلنَّوۡمَ سُبَاتٗا وَجَعَلَ ٱلنَّهَارَ نُشُورٗا
Kuma shi ne wanda ya sanya muku dare ya zama sutura, bacci kuma don hutawa kuma ya sanya rana don watsuwa (wajen neman abinci)
وَهُوَ ٱلَّذِيٓ أَرۡسَلَ ٱلرِّيَٰحَ بُشۡرَۢا بَيۡنَ يَدَيۡ رَحۡمَتِهِۦۚ وَأَنزَلۡنَا مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ طَهُورٗا
Kuma shi ne wanda ya aiko iska don albishir a gabanin (saukar) rahamarsa. Muka kuma saukar da ruwa mai tsarkakewa daga sama
لِّنُحۡـِۧيَ بِهِۦ بَلۡدَةٗ مَّيۡتٗا وَنُسۡقِيَهُۥ مِمَّا خَلَقۡنَآ أَنۡعَٰمٗا وَأَنَاسِيَّ كَثِيرٗا
Don Mu raya busasshiyar qasa da shi, kuma Mu shayar da dabbobi da mutane masu yawa daga abubuwan da Muka halitta
وَلَقَدۡ صَرَّفۡنَٰهُ بَيۡنَهُمۡ لِيَذَّكَّرُواْ فَأَبَىٰٓ أَكۡثَرُ ٱلنَّاسِ إِلَّا كُفُورٗا
Haqiqa kuma Mun sarrafa shi a tsakaninsu don su wa’azantu[1], sai mafi yawan mutane suka qi (wa’azantuwa) sai kafirci
1- Watau Allah () ya sarrafa hujjoji da dalilai daban-daban a cikin Alqur’ani domin mutane su wa’azantu.