Sura: Suratul An’am

Aya : 111

۞وَلَوۡ أَنَّنَا نَزَّلۡنَآ إِلَيۡهِمُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةَ وَكَلَّمَهُمُ ٱلۡمَوۡتَىٰ وَحَشَرۡنَا عَلَيۡهِمۡ كُلَّ شَيۡءٖ قُبُلٗا مَّا كَانُواْ لِيُؤۡمِنُوٓاْ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ يَجۡهَلُونَ

Kuma Mu xin nan da a ce lalle za Mu saukar musu da mala’iku, kuma matattu su yi musu magana, kuma Mu tattaro musu komai a gabansu, to da ba za su tava yin imani ba, sai dai idan Allah Ya ga dama, amma yawancinsu suna jahilta ne



Sura: Suratul An’am

Aya : 112

وَكَذَٰلِكَ جَعَلۡنَا لِكُلِّ نَبِيٍّ عَدُوّٗا شَيَٰطِينَ ٱلۡإِنسِ وَٱلۡجِنِّ يُوحِي بَعۡضُهُمۡ إِلَىٰ بَعۡضٖ زُخۡرُفَ ٱلۡقَوۡلِ غُرُورٗاۚ وَلَوۡ شَآءَ رَبُّكَ مَا فَعَلُوهُۖ فَذَرۡهُمۡ وَمَا يَفۡتَرُونَ

Kuma kamar haka ne Muka sanya wa kowane annabi maqiya daga shaixanun mutane da aljannu, sashinsu yana kimsa wa wani sashi qayataccen zance, don ruxi. Kuma da Ubangijinka Ya ga dama da ba su aikata haka ba; don haka ka qyale su da irin abin da suke qagowa



Sura: Suratul An’am

Aya : 113

وَلِتَصۡغَىٰٓ إِلَيۡهِ أَفۡـِٔدَةُ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ وَلِيَرۡضَوۡهُ وَلِيَقۡتَرِفُواْ مَا هُم مُّقۡتَرِفُونَ

Don kuma zukatan waxanda ba su yi imani da lahira ba su karkata zuwa gare shi, kuma su yarda da shi (ruxin) kuma su ci gaba da qago abin da suke qagowa



Sura: Suratul An’am

Aya : 114

أَفَغَيۡرَ ٱللَّهِ أَبۡتَغِي حَكَمٗا وَهُوَ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ إِلَيۡكُمُ ٱلۡكِتَٰبَ مُفَصَّلٗاۚ وَٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ يَعۡلَمُونَ أَنَّهُۥ مُنَزَّلٞ مِّن رَّبِّكَ بِٱلۡحَقِّۖ فَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمُمۡتَرِينَ

(Ka ce) “Shin wanin Allah zan nema a matsayin mai yi mana hukunci, alhalin Shi ne wanda Ya saukar muku da littafi mai bayani dalla-dalla?” Waxanda Muka ba su littafi kuwa suna sane da cewa, lalle shi saukakke ne daga Ubangijinka da gaskiya; don haka lalle kada ka kasance daga cikin masu kokwanto



Sura: Suratul An’am

Aya : 115

وَتَمَّتۡ كَلِمَتُ رَبِّكَ صِدۡقٗا وَعَدۡلٗاۚ لَّا مُبَدِّلَ لِكَلِمَٰتِهِۦۚ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ

Kuma kalmomin Ubangijinka cike suke da gaskiya da adalci. Babu kuma mai canza kalmominsa; kuma Shi ne Mai ji, Masani



Sura: Suratul An’am

Aya : 116

وَإِن تُطِعۡ أَكۡثَرَ مَن فِي ٱلۡأَرۡضِ يُضِلُّوكَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِۚ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّ وَإِنۡ هُمۡ إِلَّا يَخۡرُصُونَ

Kuma in da za ka yi biyayya ga mafiya yawan waxanda suke a bayan qasa to za su vatar da kai daga tafarkin Allah. Babu abin da suke bi face zato, kuma ba abin da suke yi face qarya



Sura: Suratul An’am

Aya : 117

إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعۡلَمُ مَن يَضِلُّ عَن سَبِيلِهِۦۖ وَهُوَ أَعۡلَمُ بِٱلۡمُهۡتَدِينَ

Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sanin waxanda suke vace wa tafarkinsa, kuma Shi ne Mafi sanin shiryayyu



Sura: Suratul An’am

Aya : 118

فَكُلُواْ مِمَّا ذُكِرَ ٱسۡمُ ٱللَّهِ عَلَيۡهِ إِن كُنتُم بِـَٔايَٰتِهِۦ مُؤۡمِنِينَ

To ku ci abin da aka ambaci sunan Allah a kansa (lokacin yankansa), in har kun kasance masu imani da ayoyinsa



Sura: Suratul An’am

Aya : 119

وَمَا لَكُمۡ أَلَّا تَأۡكُلُواْ مِمَّا ذُكِرَ ٱسۡمُ ٱللَّهِ عَلَيۡهِ وَقَدۡ فَصَّلَ لَكُم مَّا حَرَّمَ عَلَيۡكُمۡ إِلَّا مَا ٱضۡطُرِرۡتُمۡ إِلَيۡهِۗ وَإِنَّ كَثِيرٗا لَّيُضِلُّونَ بِأَهۡوَآئِهِم بِغَيۡرِ عِلۡمٍۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعۡلَمُ بِٱلۡمُعۡتَدِينَ

Kuma me ya sa ba za ku ci abin da aka ambaci sunan Allah a kansa ba, alhali Ya bayyana muku abin da Ya haramta muku, sai fa abin da kuka matsu game da shi[1]? Kuma lalle yawancinsu ba shakka suna vatar da waxansu ne ta hanyar bin son zuciyarsu, ba tare da ilimi ba. Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sanin masu qetare iyaka


1- A halin larura an halatta wa Musulmi ya ci abin da aka haramta masa gwargwadon wannan larurar kaxai.


Sura: Suratul An’am

Aya : 120

وَذَرُواْ ظَٰهِرَ ٱلۡإِثۡمِ وَبَاطِنَهُۥٓۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ يَكۡسِبُونَ ٱلۡإِثۡمَ سَيُجۡزَوۡنَ بِمَا كَانُواْ يَقۡتَرِفُونَ

Kuma ku bar (aikata) laifuka na sarari da na voye. Haqiqa waxanda suke aikata savo, za a saka musu da irin abin da suke aikatawa



Sura: Suratul An’am

Aya : 121

وَلَا تَأۡكُلُواْ مِمَّا لَمۡ يُذۡكَرِ ٱسۡمُ ٱللَّهِ عَلَيۡهِ وَإِنَّهُۥ لَفِسۡقٞۗ وَإِنَّ ٱلشَّيَٰطِينَ لَيُوحُونَ إِلَىٰٓ أَوۡلِيَآئِهِمۡ لِيُجَٰدِلُوكُمۡۖ وَإِنۡ أَطَعۡتُمُوهُمۡ إِنَّكُمۡ لَمُشۡرِكُونَ

Kuma kada ku ci daga abin da ba a ambaci sunan Allah a kansa ba, kuma lalle shi tabbas fasiqanci ne. Haqiqa shaixanu tabbas suna kimsa wa masoyansu, don su yi jayayya da ku; idan kuwa kuka bi su to lalle tabbas ku mushirikai ne



Sura: Suratul An’am

Aya : 122

أَوَمَن كَانَ مَيۡتٗا فَأَحۡيَيۡنَٰهُ وَجَعَلۡنَا لَهُۥ نُورٗا يَمۡشِي بِهِۦ فِي ٱلنَّاسِ كَمَن مَّثَلُهُۥ فِي ٱلظُّلُمَٰتِ لَيۡسَ بِخَارِجٖ مِّنۡهَاۚ كَذَٰلِكَ زُيِّنَ لِلۡكَٰفِرِينَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Shin yanzu wanda ya kasance matacce (kafiri), sai Muka rayar da shi, kuma Muka sanya masa haske (na shiriya), yana tafiya da shi cikin mutane, (yanzu) zai zama kamar wanda yake cikin duhu (na kafirci), ta yadda ba zai iya fita daga cikinsa ba? Kamar haka ne aka qawata wa kafirai abin da suka kasance suna aikatawa



Sura: Suratul An’am

Aya : 123

وَكَذَٰلِكَ جَعَلۡنَا فِي كُلِّ قَرۡيَةٍ أَكَٰبِرَ مُجۡرِمِيهَا لِيَمۡكُرُواْ فِيهَاۖ وَمَا يَمۡكُرُونَ إِلَّا بِأَنفُسِهِمۡ وَمَا يَشۡعُرُونَ

Kuma kamar haka ne a cikin kowace qasa Muka sanya manyan masu laifinta, don su yi makirci a cikinta; kuma ba wanda suke qulla wa makirci sai kawunansu, amma su ba sa jin (haka)



Sura: Suratul An’am

Aya : 124

وَإِذَا جَآءَتۡهُمۡ ءَايَةٞ قَالُواْ لَن نُّؤۡمِنَ حَتَّىٰ نُؤۡتَىٰ مِثۡلَ مَآ أُوتِيَ رُسُلُ ٱللَّهِۘ ٱللَّهُ أَعۡلَمُ حَيۡثُ يَجۡعَلُ رِسَالَتَهُۥۗ سَيُصِيبُ ٱلَّذِينَ أَجۡرَمُواْ صَغَارٌ عِندَ ٱللَّهِ وَعَذَابٞ شَدِيدُۢ بِمَا كَانُواْ يَمۡكُرُونَ

Kuma idan wata aya ta zo musu, sai su ce: “Ba za mu yi imani ba, har sai an ba mu kwatankwacin abin da aka ba wa manzannin Allah.” Ai Allah Shi ne Mafi sanin inda ya dace Ya sanya manzancinsa. Da sannu qasqanci daga Allah zai auka wa waxanda suka aikata manyan laifuka da kuma azaba mai tsanani, saboda abin da suka kasance suna shiryawa na makirci



Sura: Suratul An’am

Aya : 125

فَمَن يُرِدِ ٱللَّهُ أَن يَهۡدِيَهُۥ يَشۡرَحۡ صَدۡرَهُۥ لِلۡإِسۡلَٰمِۖ وَمَن يُرِدۡ أَن يُضِلَّهُۥ يَجۡعَلۡ صَدۡرَهُۥ ضَيِّقًا حَرَجٗا كَأَنَّمَا يَصَّعَّدُ فِي ٱلسَّمَآءِۚ كَذَٰلِكَ يَجۡعَلُ ٱللَّهُ ٱلرِّجۡسَ عَلَى ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ

Sannan duk wanda Allah Ya yi nufin shiryar da shi, sai Ya yalwata qirjinsa ga karvar Musulunci. Duk wanda kuwa Ya yi nufin Ya vatar da shi, sai Ya sanya qirjinsa a quntace ainun kamar wanda yake yunqurin hawa sama. Kamar haka ne Allah Yake sanya vata a kan waxanda ba sa yin imani



Sura: Suratul An’am

Aya : 126

وَهَٰذَا صِرَٰطُ رَبِّكَ مُسۡتَقِيمٗاۗ قَدۡ فَصَّلۡنَا ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يَذَّكَّرُونَ

Kuma wannan shi ne tafarkin Ubangijinka miqaqqe. Haqiqa Mun bayyana ayoyi ga mutanen da suke tuntuntuni



Sura: Suratul An’am

Aya : 127

۞لَهُمۡ دَارُ ٱلسَّلَٰمِ عِندَ رَبِّهِمۡۖ وَهُوَ وَلِيُّهُم بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Suna da gida na aminci a wurin Ubangijinsu, kuma Shi ne Majivincinsu, saboda abin da suka kasance suna aikatawa



Sura: Suratul An’am

Aya : 128

وَيَوۡمَ يَحۡشُرُهُمۡ جَمِيعٗا يَٰمَعۡشَرَ ٱلۡجِنِّ قَدِ ٱسۡتَكۡثَرۡتُم مِّنَ ٱلۡإِنسِۖ وَقَالَ أَوۡلِيَآؤُهُم مِّنَ ٱلۡإِنسِ رَبَّنَا ٱسۡتَمۡتَعَ بَعۡضُنَا بِبَعۡضٖ وَبَلَغۡنَآ أَجَلَنَا ٱلَّذِيٓ أَجَّلۡتَ لَنَاۚ قَالَ ٱلنَّارُ مَثۡوَىٰكُمۡ خَٰلِدِينَ فِيهَآ إِلَّا مَا شَآءَ ٱللَّهُۚ إِنَّ رَبَّكَ حَكِيمٌ عَلِيمٞ

Kuma (ka tuna) ranar da zai tara su gaba xaya (Ya ce): “Ya ku jama’ar aljannu, haqiqa kun samu mabiya da yawa daga cikin mutane.” Sai majivinta lamarinsu cikin mutane su ce: “Ya Ubangijinmu; mun dai daxaxa wa junanmu kuma mun kawo qarshen lokacin da Ka yanka mana.” Sai Ya ce: “Wuta ita ce makomarku, za ku dawwama a cikinta, sai dai abin da Allah Ya ga dama.” Lalle Ubangijinka Mai hikima ne, Mai yawan sani



Sura: Suratul An’am

Aya : 129

وَكَذَٰلِكَ نُوَلِّي بَعۡضَ ٱلظَّـٰلِمِينَ بَعۡضَۢا بِمَا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ

Kuma kamar haka ne Muke xora wani sashi na azzalumai a kan wani sashi, saboda abin da suka kasance suna aikatawa



Sura: Suratul An’am

Aya : 130

يَٰمَعۡشَرَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِ أَلَمۡ يَأۡتِكُمۡ رُسُلٞ مِّنكُمۡ يَقُصُّونَ عَلَيۡكُمۡ ءَايَٰتِي وَيُنذِرُونَكُمۡ لِقَآءَ يَوۡمِكُمۡ هَٰذَاۚ قَالُواْ شَهِدۡنَا عَلَىٰٓ أَنفُسِنَاۖ وَغَرَّتۡهُمُ ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَا وَشَهِدُواْ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِمۡ أَنَّهُمۡ كَانُواْ كَٰفِرِينَ

Ya ku jama’ar aljannu da mutane, shin manzanni daga cikinku ba su zo muku ba, suna karanta muku ayoyina, kuma suna gargaxin ku game da saduwarku da wannan yini?” Sai su ce: “Mun ba da shaida a kan kawunanmu;” rayuwar duniya kuma ta ruxe su, kuma suka yi wa kansu shaidar cewa lalle su sun kasance kafirai



Sura: Suratul An’am

Aya : 131

ذَٰلِكَ أَن لَّمۡ يَكُن رَّبُّكَ مُهۡلِكَ ٱلۡقُرَىٰ بِظُلۡمٖ وَأَهۡلُهَا غَٰفِلُونَ

Haka ta faru ne, saboda Ubangijinka bai zamanto Mai hallakar da wata alqarya saboda kafircewarta ba, alhali mutanenta suna cikin gafala



Sura: Suratul An’am

Aya : 132

وَلِكُلّٖ دَرَجَٰتٞ مِّمَّا عَمِلُواْۚ وَمَا رَبُّكَ بِغَٰفِلٍ عَمَّا يَعۡمَلُونَ

Kuma kowanne yana da nasa matsayi game da abin da suka aikata, kuma Ubangijinka bai zama Mai rafkana ba dangane da abin da suke aikatawa



Sura: Suratul An’am

Aya : 133

وَرَبُّكَ ٱلۡغَنِيُّ ذُو ٱلرَّحۡمَةِۚ إِن يَشَأۡ يُذۡهِبۡكُمۡ وَيَسۡتَخۡلِفۡ مِنۢ بَعۡدِكُم مَّا يَشَآءُ كَمَآ أَنشَأَكُم مِّن ذُرِّيَّةِ قَوۡمٍ ءَاخَرِينَ

Kuma Ubangijinka Shi ne Mawadaci, Mai rahama. Idan Ya ga dama sai Ya tafiyar da ku, kuma Ya maye gurbinku da waxanda Ya ga dama, kamar yadda Ya fare ku daga zurriyar waxansu mutanen daban



Sura: Suratul An’am

Aya : 134

إِنَّ مَا تُوعَدُونَ لَأٓتٖۖ وَمَآ أَنتُم بِمُعۡجِزِينَ

Lalle abin da ake yi Muku alqawarinsa mai zuwa ne; kuma ku ba za ku iya kuvucewa (daga azabarmu) ba



Sura: Suratul An’am

Aya : 135

قُلۡ يَٰقَوۡمِ ٱعۡمَلُواْ عَلَىٰ مَكَانَتِكُمۡ إِنِّي عَامِلٞۖ فَسَوۡفَ تَعۡلَمُونَ مَن تَكُونُ لَهُۥ عَٰقِبَةُ ٱلدَّارِۚ إِنَّهُۥ لَا يُفۡلِحُ ٱلظَّـٰلِمُونَ

Ka ce: “Ya ku mutanena, ku yi aiki a kan irin hanyarku, lalle ni ma mai yin aiki ne (kan hanyata); don haka da sannu za ku san wanda zai yi kyakkyawan qarshe. Lalle su dai azzalumai ba za su rabauta ba



Sura: Suratul An’am

Aya : 136

وَجَعَلُواْ لِلَّهِ مِمَّا ذَرَأَ مِنَ ٱلۡحَرۡثِ وَٱلۡأَنۡعَٰمِ نَصِيبٗا فَقَالُواْ هَٰذَا لِلَّهِ بِزَعۡمِهِمۡ وَهَٰذَا لِشُرَكَآئِنَاۖ فَمَا كَانَ لِشُرَكَآئِهِمۡ فَلَا يَصِلُ إِلَى ٱللَّهِۖ وَمَا كَانَ لِلَّهِ فَهُوَ يَصِلُ إِلَىٰ شُرَكَآئِهِمۡۗ سَآءَ مَا يَحۡكُمُونَ

Kuma sun sanya wa Allah wani kaso cikin abin da Ya halitta na amfanin gona da dabbobin gida, sai suka riqa cewa: “Wannan kaso na Allah ne”, a riyawarsu, “Wannan kuma na gumakanmu ne;” sannan abin da ya kasance na gumakansu ba zai isa ga Allah ba; abin da kuwa ya kasance na Allah, to shi zai isa ga gumakansu. Abin da suke hukuntawa ya munana[1]


1- Mushirikan Larabawa sukan kasa amfanin gonarsu da dabbobinsu kaso biyu, kaso xaya su ce na Allah ne, kaso na biyun kuma su ce na gumakansu ne. To idan kason gumakansu ya shiga cikin kason Allah sai su dawo da shi wurinsu, amma idan kason da suka ware wa Allah ya shiga na gumakansu ba za su dawo da shi ba.


Sura: Suratul An’am

Aya : 137

وَكَذَٰلِكَ زَيَّنَ لِكَثِيرٖ مِّنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ قَتۡلَ أَوۡلَٰدِهِمۡ شُرَكَآؤُهُمۡ لِيُرۡدُوهُمۡ وَلِيَلۡبِسُواْ عَلَيۡهِمۡ دِينَهُمۡۖ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ مَا فَعَلُوهُۖ فَذَرۡهُمۡ وَمَا يَفۡتَرُونَ

Kuma kamar haka ne abokan tarayyarsu suka qawata wa yawancin mushirikai su dinga kashe ‘ya’yansu, don su hallakar da su, kuma don su rikita musu addininsu. Kuma da Allah Ya ga dama da ba su aikata haka ba. To ka qyale su da irin abin da suke qagawa



Sura: Suratul An’am

Aya : 138

وَقَالُواْ هَٰذِهِۦٓ أَنۡعَٰمٞ وَحَرۡثٌ حِجۡرٞ لَّا يَطۡعَمُهَآ إِلَّا مَن نَّشَآءُ بِزَعۡمِهِمۡ وَأَنۡعَٰمٌ حُرِّمَتۡ ظُهُورُهَا وَأَنۡعَٰمٞ لَّا يَذۡكُرُونَ ٱسۡمَ ٱللَّهِ عَلَيۡهَا ٱفۡتِرَآءً عَلَيۡهِۚ سَيَجۡزِيهِم بِمَا كَانُواْ يَفۡتَرُونَ

Kuma suka ce: “Waxannan dabbobi na gida da kuma amfanin gona haramtattu ne, ba wanda zai ci su sai wanda muka ga dama,” a riyawarsu. Waxansu dabbobin kuma an haramta hawansu, waxansu dabbobin kuma ba sa ambaton sunan Allah a kansu (yayin yankan su), don kawai su yi masa qage. Da sannu zai yi musu sakamakon abin da suka kasance suna qagawa



Sura: Suratul An’am

Aya : 139

وَقَالُواْ مَا فِي بُطُونِ هَٰذِهِ ٱلۡأَنۡعَٰمِ خَالِصَةٞ لِّذُكُورِنَا وَمُحَرَّمٌ عَلَىٰٓ أَزۡوَٰجِنَاۖ وَإِن يَكُن مَّيۡتَةٗ فَهُمۡ فِيهِ شُرَكَآءُۚ سَيَجۡزِيهِمۡ وَصۡفَهُمۡۚ إِنَّهُۥ حَكِيمٌ عَلِيمٞ

Kuma suka ce: “Abin da yake cikin waxannan dabbobi, a kevance yake ga mazajenmu, amma haramun ne ga matayenmu.” Idan kuma ya zamo mushe, to su duka sai su yi tarayya a kansa. Da sannu (Allah) zai yi musu sakayyar wannan abin da suka siffanta. Lalle Shi Mai hikima ne, Mai yawan sani



Sura: Suratul An’am

Aya : 140

قَدۡ خَسِرَ ٱلَّذِينَ قَتَلُوٓاْ أَوۡلَٰدَهُمۡ سَفَهَۢا بِغَيۡرِ عِلۡمٖ وَحَرَّمُواْ مَا رَزَقَهُمُ ٱللَّهُ ٱفۡتِرَآءً عَلَى ٱللَّهِۚ قَدۡ ضَلُّواْ وَمَا كَانُواْ مُهۡتَدِينَ

Haqiqa waxannan da suka kashe ‘ya’yansu don wauta, ba tare da ilimi ba sun tave, kuma suka haramta wa kansu abin da Allah Ya arzuta su da shi, don qage ga Allah. Haqiqa sun vata, kuma ba su kasance shiryayyu ba