وَكَذَّبَ بِهِۦ قَوۡمُكَ وَهُوَ ٱلۡحَقُّۚ قُل لَّسۡتُ عَلَيۡكُم بِوَكِيلٖ
Kuma mutanenka sun qaryata shi (Alqur’ani) alhali shi ne gaskiya. Ka ce: “Ni ba wakili ne a kanku ba
لِّكُلِّ نَبَإٖ مُّسۡتَقَرّٞۚ وَسَوۡفَ تَعۡلَمُونَ
“Kowane labari yana da lokaci ne na musamman. Kuma da sannu za ku sani.”
وَإِذَا رَأَيۡتَ ٱلَّذِينَ يَخُوضُونَ فِيٓ ءَايَٰتِنَا فَأَعۡرِضۡ عَنۡهُمۡ حَتَّىٰ يَخُوضُواْ فِي حَدِيثٍ غَيۡرِهِۦۚ وَإِمَّا يُنسِيَنَّكَ ٱلشَّيۡطَٰنُ فَلَا تَقۡعُدۡ بَعۡدَ ٱلذِّكۡرَىٰ مَعَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلظَّـٰلِمِينَ
Kuma idan ka ga waxanda suke kutsawa cikin ayoyinmu (suna izgili), to ka rabu da su, har sai sun canja wani zancen da ba wancan ba. Amma in da Shaixan zai mantar da kai kuwa, to bayan ka tuna kar ka sake zama tare da azzalumai
وَمَا عَلَى ٱلَّذِينَ يَتَّقُونَ مِنۡ حِسَابِهِم مِّن شَيۡءٖ وَلَٰكِن ذِكۡرَىٰ لَعَلَّهُمۡ يَتَّقُونَ
Kuma babu wani laifi a kan waxanda suke tsoron haxuwarsu da Allah (don sun zauna da su), sai dai kuma (dole su yi) musu wa’azi don su tsorata
وَذَرِ ٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ دِينَهُمۡ لَعِبٗا وَلَهۡوٗا وَغَرَّتۡهُمُ ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَاۚ وَذَكِّرۡ بِهِۦٓ أَن تُبۡسَلَ نَفۡسُۢ بِمَا كَسَبَتۡ لَيۡسَ لَهَا مِن دُونِ ٱللَّهِ وَلِيّٞ وَلَا شَفِيعٞ وَإِن تَعۡدِلۡ كُلَّ عَدۡلٖ لَّا يُؤۡخَذۡ مِنۡهَآۗ أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ أُبۡسِلُواْ بِمَا كَسَبُواْۖ لَهُمۡ شَرَابٞ مِّنۡ حَمِيمٖ وَعَذَابٌ أَلِيمُۢ بِمَا كَانُواْ يَكۡفُرُونَ
Ka rabu da waxanda suka xauki addininsu wasa da sharholiya, rayuwarsu ta duniya kuma ta ruxe su. Ka kuma yi gargaxi da shi (Alqur’ani), saboda kada a jarrabi rai da abin da ya aikata wanda ba ya da wani mataimaki ko mai ceto ban da Allah, ko da kuwa (ran) ya ba da kowace irin fansa ba za a karva ba daga gare shi. Waxancan su ne waxanda aka kange (don yi musu azaba) saboda abin da suka aikata; suna da abin sha na tafasasshen ruwa da kuma azaba mai raxaxi saboda abin da suka zamanto suna kafircewa (da shi)
قُلۡ أَنَدۡعُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَنفَعُنَا وَلَا يَضُرُّنَا وَنُرَدُّ عَلَىٰٓ أَعۡقَابِنَا بَعۡدَ إِذۡ هَدَىٰنَا ٱللَّهُ كَٱلَّذِي ٱسۡتَهۡوَتۡهُ ٱلشَّيَٰطِينُ فِي ٱلۡأَرۡضِ حَيۡرَانَ لَهُۥٓ أَصۡحَٰبٞ يَدۡعُونَهُۥٓ إِلَى ٱلۡهُدَى ٱئۡتِنَاۗ قُلۡ إِنَّ هُدَى ٱللَّهِ هُوَ ٱلۡهُدَىٰۖ وَأُمِرۡنَا لِنُسۡلِمَ لِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Ka ce: “Shin yanzu ma riqa bauta wa wani wanda ba Allah ba, abin da ba zai amfane mu ba, kuma ba zai cutar da mu ba, mu koma gidan jiya (kafirai) bayan kuwa Allah Ya shiryar da mu, (mu koma) kamar wanda shaixanu suka vatar da shi yana ta ximuwa a bayan qasa, ga shi da wasu abokai suna kiran sa zuwa ga shiriya, (suna cewa): “Ka zo (mu bi tafarkin shiriya)[1].” Ka ce: “Lalle shiriyar Allah fa ita kaxai ce shiriya; kuma mu an umarce mu da mu miqa wuya ne kaxai ga Ubangijin talikai
1- Misali ne na wanda ya saki Musulunci ya kama shirka ko vata, ya zama kamar mutumin da aljanu suka xauke shi suka tafi da shi suka jefar da shi a qurgurmin daji. Don haka ya yi nisan da ba zai ji kira ba, balle ya gane hanyar dawowa.
وَأَنۡ أَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَٱتَّقُوهُۚ وَهُوَ ٱلَّذِيٓ إِلَيۡهِ تُحۡشَرُونَ
“Kuma ku tsayar da salla kuma ku kiyaye dokokinsa. Kuma Shi ne Wanda za a tara ku zuwa gare Shi
وَهُوَ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ بِٱلۡحَقِّۖ وَيَوۡمَ يَقُولُ كُن فَيَكُونُۚ قَوۡلُهُ ٱلۡحَقُّۚ وَلَهُ ٱلۡمُلۡكُ يَوۡمَ يُنفَخُ فِي ٱلصُّورِۚ عَٰلِمُ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِۚ وَهُوَ ٱلۡحَكِيمُ ٱلۡخَبِيرُ
“Kuma Shi ne Wanda ya halicci sammai da qasa da gaskiya; kuma (ku tuna) ranar da zai ce da abu: ‘Kasance!’ Nan take sai ya kasance. Maganarsa gaskiya ce. Kuma Shi ne Yake da cikakken mulki a ranar da za a busa qaho Masanin gaibu da sarari, kuma Shi ne Mai hikima, Mai cikakken sani.”
۞وَإِذۡ قَالَ إِبۡرَٰهِيمُ لِأَبِيهِ ءَازَرَ أَتَتَّخِذُ أَصۡنَامًا ءَالِهَةً إِنِّيٓ أَرَىٰكَ وَقَوۡمَكَ فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ
Kuma (ka tuna) lokacin da Ibrahimu ya ce da babansa Azaru: “Yanzu ka riqi gumaka a matsayin alloli? Lalle ni ina ganin ka kai da mutanenka, kuna cikin vata mabayyani.”
وَكَذَٰلِكَ نُرِيٓ إِبۡرَٰهِيمَ مَلَكُوتَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَلِيَكُونَ مِنَ ٱلۡمُوقِنِينَ
Kuma kamar haka ne Muke nuna wa Ibrahimu halittun sammai da qasa, domin ya kasance cikin masu sakankancewa
فَلَمَّا جَنَّ عَلَيۡهِ ٱلَّيۡلُ رَءَا كَوۡكَبٗاۖ قَالَ هَٰذَا رَبِّيۖ فَلَمَّآ أَفَلَ قَالَ لَآ أُحِبُّ ٱلۡأٓفِلِينَ
To yayin da dare ya lulluve shi, ya ga tauraro, sai ya ce; “Wannan shi ne ubangijina;”[1] sannan yayin da ya vace, sai ya ce: “Ni fa ba na son abubuwa masu gushewa.”
1- Daga wannan ayar zuwa aya ta 79 Allah () ya koya wa Annabi Ibrahim () hanyar da zai yi wa mutanensa wa’azi cikin hikima da laluma don jan hankalinsu su fahimci abubuwan da suke bauta wa ba ababen bauta ne na gaskiya ba.
فَلَمَّا رَءَا ٱلۡقَمَرَ بَازِغٗا قَالَ هَٰذَا رَبِّيۖ فَلَمَّآ أَفَلَ قَالَ لَئِن لَّمۡ يَهۡدِنِي رَبِّي لَأَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلضَّآلِّينَ
Sa’annan yayin da ya ga wata ya fito, sai ya ce; “Wannan shi ne ubangijina;” sannan yayin da ya gushe, sai ya ce: “Lalle idan Ubangijina bai shiryar da ni ba, haqiqa zan kasance daga cikin mutane vatattu.”
فَلَمَّا رَءَا ٱلشَّمۡسَ بَازِغَةٗ قَالَ هَٰذَا رَبِّي هَٰذَآ أَكۡبَرُۖ فَلَمَّآ أَفَلَتۡ قَالَ يَٰقَوۡمِ إِنِّي بَرِيٓءٞ مِّمَّا تُشۡرِكُونَ
Sannan yayin da ya ga rana ta hudo, sai ya ce: “Wannan shi ne ubangijina, wannan shi ya fi girma;” sannan yayin da ta vace, sai ya ce: “Ya ku mutanena, haqiqa ni ba ruwana da abin da kuke haxa Allah da shi
إِنِّي وَجَّهۡتُ وَجۡهِيَ لِلَّذِي فَطَرَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ حَنِيفٗاۖ وَمَآ أَنَا۠ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ
“Lalle ni kam na juyar da fuskata ga Wanda Ya halicci sammai da qasa, ina mai kauce wa varna kuma ni ba na cikin masu yin shirka.”
وَحَآجَّهُۥ قَوۡمُهُۥۚ قَالَ أَتُحَـٰٓجُّوٓنِّي فِي ٱللَّهِ وَقَدۡ هَدَىٰنِۚ وَلَآ أَخَافُ مَا تُشۡرِكُونَ بِهِۦٓ إِلَّآ أَن يَشَآءَ رَبِّي شَيۡـٔٗاۚ وَسِعَ رَبِّي كُلَّ شَيۡءٍ عِلۡمًاۚ أَفَلَا تَتَذَكَّرُونَ
Kuma mutanensa sun yi jayayya da shi; (sai) ya ce: “Shin yanzu kwa riqa jayayya da ni game da (kaxaitakar) Allah, alhalin kuwa Ya shiryar da ni? Kuma ba na jin tsoron abin da kuke sanya wa Allah kishiya da shi, sai abin da Ubangijina Ya ga dama. Kuma ilimin Ubangijina ya yalwaci komai. Shin ba za ku wa’azantu ba?
وَكَيۡفَ أَخَافُ مَآ أَشۡرَكۡتُمۡ وَلَا تَخَافُونَ أَنَّكُمۡ أَشۡرَكۡتُم بِٱللَّهِ مَا لَمۡ يُنَزِّلۡ بِهِۦ عَلَيۡكُمۡ سُلۡطَٰنٗاۚ فَأَيُّ ٱلۡفَرِيقَيۡنِ أَحَقُّ بِٱلۡأَمۡنِۖ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ
“To ta qaqa kuwa zan ji tsoron abin da kuka tara da (Allah), alhali ku kuma ba kwa jin tsoron kun sanya wa Allah kishiya, abin da kuwa bai saukar muku da wata hujja a kai ba? To wane vangare ne cikin vangarori biyu, ya fi dacewa da samun aminci; in har kun kasance kun sani?
ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَلَمۡ يَلۡبِسُوٓاْ إِيمَٰنَهُم بِظُلۡمٍ أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمُ ٱلۡأَمۡنُ وَهُم مُّهۡتَدُونَ
“Waxanda suka yi imani, kuma ba su garwaya imaninsu da zalunci ba, waxannan su suke da aminci, kuma su ne shiryayyu.”
وَتِلۡكَ حُجَّتُنَآ ءَاتَيۡنَٰهَآ إِبۡرَٰهِيمَ عَلَىٰ قَوۡمِهِۦۚ نَرۡفَعُ دَرَجَٰتٖ مَّن نَّشَآءُۗ إِنَّ رَبَّكَ حَكِيمٌ عَلِيمٞ
Kuma waxancan su ne hujjojinmu da Muka ba wa Ibrahimu su a kan mutanensa. Muna xaukaka darajojin waxanda Muka ga dama. Lalle Ubangijinka Mai hikima ne, Mai yawan sani
وَوَهَبۡنَا لَهُۥٓ إِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَۚ كُلًّا هَدَيۡنَاۚ وَنُوحًا هَدَيۡنَا مِن قَبۡلُۖ وَمِن ذُرِّيَّتِهِۦ دَاوُۥدَ وَسُلَيۡمَٰنَ وَأَيُّوبَ وَيُوسُفَ وَمُوسَىٰ وَهَٰرُونَۚ وَكَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Kuma Muka ba shi Ishaqa da Ya’aqubu. Kowanne daga cikinsu Mun shiryar da shi, kuma Mun shiryar da Nuhu tun gabaninsu. Kuma daga cikin zurriyarsa akwai Dawudu da Sulaimanu da Ayyuba da Yusufu da Musa da Haruna. Kuma kamar haka ne Muke saka wa masu kyautata (ayyukansu)
وَزَكَرِيَّا وَيَحۡيَىٰ وَعِيسَىٰ وَإِلۡيَاسَۖ كُلّٞ مِّنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ
Da Zakariyya da Yahaya da Isa da Iliyasu; kowanne daga cikinsu yana cikin salihan bayi
وَإِسۡمَٰعِيلَ وَٱلۡيَسَعَ وَيُونُسَ وَلُوطٗاۚ وَكُلّٗا فَضَّلۡنَا عَلَى ٱلۡعَٰلَمِينَ
Da Isma’ilu da Alyasa’u da Yunusu da Luxu. Kowanne daga cikinsu kuma Mun fifita shi a kan (sauran) talikai
وَمِنۡ ءَابَآئِهِمۡ وَذُرِّيَّـٰتِهِمۡ وَإِخۡوَٰنِهِمۡۖ وَٱجۡتَبَيۡنَٰهُمۡ وَهَدَيۡنَٰهُمۡ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ
Kuma daga cikin iyayensu da zurriyarsu da ‘yan’uwansu; duka Mun zave su, kuma Mun shiryar da su zuwa ga tafarki madaidaici
ذَٰلِكَ هُدَى ٱللَّهِ يَهۡدِي بِهِۦ مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦۚ وَلَوۡ أَشۡرَكُواْ لَحَبِطَ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Wannan ita ce shiriyar Allah wadda da ita ne Yake shiryar da wanda Ya ga dama cikin bayinsa. Kuma da a ce sun yi shirka, to lalle da duk abin da suka kasance suna aikatawa ya rushe
أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحُكۡمَ وَٱلنُّبُوَّةَۚ فَإِن يَكۡفُرۡ بِهَا هَـٰٓؤُلَآءِ فَقَدۡ وَكَّلۡنَا بِهَا قَوۡمٗا لَّيۡسُواْ بِهَا بِكَٰفِرِينَ
Waxannan su ne waxanda Muka bai wa littattafai da hukunci da annabta. To idan waxancan (mutanen Makka) suka kafirce mata (shiriya), to haqiqa Mun shirya musu waxansu mutane waxanda ba za su kafirce mata ba
أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ هَدَى ٱللَّهُۖ فَبِهُدَىٰهُمُ ٱقۡتَدِهۡۗ قُل لَّآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ أَجۡرًاۖ إِنۡ هُوَ إِلَّا ذِكۡرَىٰ لِلۡعَٰلَمِينَ
Waxannan su ne waxanda Allah Ya shiryar; don haka ka yi koyi da irin shiriyarsu. Ka ce: “Ba na roqon ku wani lada game da shi (Alqur’ani); shi ba komai ba ne face tunatarwa ga talikai.”
وَمَا قَدَرُواْ ٱللَّهَ حَقَّ قَدۡرِهِۦٓ إِذۡ قَالُواْ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ عَلَىٰ بَشَرٖ مِّن شَيۡءٖۗ قُلۡ مَنۡ أَنزَلَ ٱلۡكِتَٰبَ ٱلَّذِي جَآءَ بِهِۦ مُوسَىٰ نُورٗا وَهُدٗى لِّلنَّاسِۖ تَجۡعَلُونَهُۥ قَرَاطِيسَ تُبۡدُونَهَا وَتُخۡفُونَ كَثِيرٗاۖ وَعُلِّمۡتُم مَّا لَمۡ تَعۡلَمُوٓاْ أَنتُمۡ وَلَآ ءَابَآؤُكُمۡۖ قُلِ ٱللَّهُۖ ثُمَّ ذَرۡهُمۡ فِي خَوۡضِهِمۡ يَلۡعَبُونَ
Kuma ba su girmama Allah haqiqanin girman da ya kamace shi ba, yayin da suka ce: “Allah bai saukar wa wani mutum da komai ba.” Ka ce: “Wane ne ya saukar da littafin da Musa ya zo da shi, mai haske, kuma mai shiryar da mutane; kuka riqa mayar da takardunsa falle-falle, kuna bayyana (waxanda kuke so), kuma kuna voye wani kaso mai yawa; kuma aka sanar da ku abin da ba ku sani ba, ku da ma iyayenku?” Ka ce: “Allah ne (Ya saukar da shi)” Sannan sai ka qyale su su yi ta kutsawa cikin varnarsu, suna wasa
وَهَٰذَا كِتَٰبٌ أَنزَلۡنَٰهُ مُبَارَكٞ مُّصَدِّقُ ٱلَّذِي بَيۡنَ يَدَيۡهِ وَلِتُنذِرَ أُمَّ ٱلۡقُرَىٰ وَمَنۡ حَوۡلَهَاۚ وَٱلَّذِينَ يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ يُؤۡمِنُونَ بِهِۦۖ وَهُمۡ عَلَىٰ صَلَاتِهِمۡ يُحَافِظُونَ
Kuma wannan (Alqur’ani) littafi ne mai albarka, wanda Muka saukar da shi mai gaskata abin da ya gabace shi (na littattafai), kuma don ka gargaxi uwar alqaryu (mutanen Makka) da waxanda suke kewaye da ita. Waxanda kuwa suke yin imani da ranar lahira, suna yin imani da shi ne (Alqur’ani), kuma su suna kiyaye sallolinsu
وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا أَوۡ قَالَ أُوحِيَ إِلَيَّ وَلَمۡ يُوحَ إِلَيۡهِ شَيۡءٞ وَمَن قَالَ سَأُنزِلُ مِثۡلَ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُۗ وَلَوۡ تَرَىٰٓ إِذِ ٱلظَّـٰلِمُونَ فِي غَمَرَٰتِ ٱلۡمَوۡتِ وَٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ بَاسِطُوٓاْ أَيۡدِيهِمۡ أَخۡرِجُوٓاْ أَنفُسَكُمُۖ ٱلۡيَوۡمَ تُجۡزَوۡنَ عَذَابَ ٱلۡهُونِ بِمَا كُنتُمۡ تَقُولُونَ عَلَى ٱللَّهِ غَيۡرَ ٱلۡحَقِّ وَكُنتُمۡ عَنۡ ءَايَٰتِهِۦ تَسۡتَكۡبِرُونَ
Kuma wane ne ya fi zalunci kamar wanda ya qagi qarya ya jingina wa Allah, ko kuma ya ce: “An yiwo mini wahayi,” alhalin kuma ba a yi masa wahayin komai ba, da kuma wanda ya ce: “Zan saukar da irin abin da Allah Ya saukar?” Kuma da za ka ga lokacin da kafirai suke cikin magagin mutuwa, mala’iku kuma suna miqa hannayensu suna cewa: “Ku fito da rayukanku (da kanku), a yau ne za a saka muku da azabar wulaqanci, saboda irin abin da kuke faxa game da Allah wanda ba gaskiya ba, kuma kun kasance kuna girman kai game da ayoyinsa.”
وَلَقَدۡ جِئۡتُمُونَا فُرَٰدَىٰ كَمَا خَلَقۡنَٰكُمۡ أَوَّلَ مَرَّةٖ وَتَرَكۡتُم مَّا خَوَّلۡنَٰكُمۡ وَرَآءَ ظُهُورِكُمۡۖ وَمَا نَرَىٰ مَعَكُمۡ شُفَعَآءَكُمُ ٱلَّذِينَ زَعَمۡتُمۡ أَنَّهُمۡ فِيكُمۡ شُرَكَـٰٓؤُاْۚ لَقَد تَّقَطَّعَ بَيۡنَكُمۡ وَضَلَّ عَنكُم مَّا كُنتُمۡ تَزۡعُمُونَ
Kuma lalle haqiqa kun zo Mana xaixai kamar yadda Muka halicce ku a karon fari, kuma kun baro abin da Muka ba ku a bayanku (a duniya), kuma har yanzu ba Ma ganin masu ceton ku waxanda kuka riya cewa su ne abokanan tarayyarku. Lalle haqiqa dangantakar da take tsakaninku ta yanke, kuma abin da kuke riyawa ya vace muku
۞إِنَّ ٱللَّهَ فَالِقُ ٱلۡحَبِّ وَٱلنَّوَىٰۖ يُخۡرِجُ ٱلۡحَيَّ مِنَ ٱلۡمَيِّتِ وَمُخۡرِجُ ٱلۡمَيِّتِ مِنَ ٱلۡحَيِّۚ ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُۖ فَأَنَّىٰ تُؤۡفَكُونَ
Lalle Allah ne Yake tsaga qwaya da qwallon dabino (lokacin tsirowarsa) shi Yake fitar da rayayye daga matacce, kuma Mai fitar da matacce daga rayayye. Mai yin wannan aiki Shi ne Allah; to ta yaya ake kautar da ku?