Sura: Suratul An’am

Aya : 96

فَالِقُ ٱلۡإِصۡبَاحِ وَجَعَلَ ٱلَّيۡلَ سَكَنٗا وَٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَ حُسۡبَانٗاۚ ذَٰلِكَ تَقۡدِيرُ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡعَلِيمِ

(Shi ne) Mai keto da hasken safiya, kuma Ya sanya dare don nutsuwa; rana da wata kuma don qidayar lokatai. Wannan shiri ne na (Allah) Mabuwayi, Mai yawan sani



Sura: Suratul An’am

Aya : 97

وَهُوَ ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلنُّجُومَ لِتَهۡتَدُواْ بِهَا فِي ظُلُمَٰتِ ٱلۡبَرِّ وَٱلۡبَحۡرِۗ قَدۡ فَصَّلۡنَا ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يَعۡلَمُونَ

Kuma Shi ne Wanda Ya sanya muku taurari domin ku gane hanya da su a cikin duffan tudu da na ruwa. Haqiqa Mun bayyana ayoyi ga mutanen da suke da sani



Sura: Suratul An’am

Aya : 98

وَهُوَ ٱلَّذِيٓ أَنشَأَكُم مِّن نَّفۡسٖ وَٰحِدَةٖ فَمُسۡتَقَرّٞ وَمُسۡتَوۡدَعٞۗ قَدۡ فَصَّلۡنَا ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يَفۡقَهُونَ

Kuma Shi ne Wanda Ya halicce ku daga rai xaya, sannan Ya ajiye ku a wani wurin zama (tsatson namiji) da kuma wani wurin ajiya, (mahaifiyar mace). Haqiqa Mun bayyana ayoyi ga mutanen da suke fahimta



Sura: Suratul An’am

Aya : 99

وَهُوَ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَخۡرَجۡنَا بِهِۦ نَبَاتَ كُلِّ شَيۡءٖ فَأَخۡرَجۡنَا مِنۡهُ خَضِرٗا نُّخۡرِجُ مِنۡهُ حَبّٗا مُّتَرَاكِبٗا وَمِنَ ٱلنَّخۡلِ مِن طَلۡعِهَا قِنۡوَانٞ دَانِيَةٞ وَجَنَّـٰتٖ مِّنۡ أَعۡنَابٖ وَٱلزَّيۡتُونَ وَٱلرُّمَّانَ مُشۡتَبِهٗا وَغَيۡرَ مُتَشَٰبِهٍۗ ٱنظُرُوٓاْ إِلَىٰ ثَمَرِهِۦٓ إِذَآ أَثۡمَرَ وَيَنۡعِهِۦٓۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكُمۡ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ

Kuma Shi ne Wanda Ya saukar da ruwa daga sama, sai Muka fitar da kowane irin dangin tsiro da shi, sannan Muka fitar da shi (tsiron) (wasu) koraye, daga gare shi kuma Muke fitar da qwayoyi a cunkushe daga gare shi. Kuma daga hudar dabino (ake samun) nonuna waxanda suke dab da qasa; da kuma waxansu lambuna na inabi da zaitun da ruman, masu kama da juna da kuma mabambanta. Ku kalli ‘ya’yansu idan suka yi ‘ya’ya da kuma lokacin da suka nuna. Lalle game da wannan akwai ayoyi ga mutanen da suka yi imani



Sura: Suratul An’am

Aya : 100

وَجَعَلُواْ لِلَّهِ شُرَكَآءَ ٱلۡجِنَّ وَخَلَقَهُمۡۖ وَخَرَقُواْ لَهُۥ بَنِينَ وَبَنَٰتِۭ بِغَيۡرِ عِلۡمٖۚ سُبۡحَٰنَهُۥ وَتَعَٰلَىٰ عَمَّا يَصِفُونَ

Kuma sun sanya wa Allah aljannu a matsayin abokanan tarayya, alhali kuwa Shi ya halicce su; kuma suka qago masa ‘ya’ya maza da mata, ba tare da wani ilimi ba. Tsarki ya tabbata a gare Shi, kuma Ya xaukaka daga irin abin da suke siffanta (Shi da shi)



Sura: Suratul An’am

Aya : 101

بَدِيعُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ أَنَّىٰ يَكُونُ لَهُۥ وَلَدٞ وَلَمۡ تَكُن لَّهُۥ صَٰحِبَةٞۖ وَخَلَقَ كُلَّ شَيۡءٖۖ وَهُوَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٞ

(Shi ne) Maqagin sammai da qasa; ta yaya zai zama Yana da xa, ga Shi kuma ba Shi da mata? Kuma Shi ne Ya halicci komai, kuma Shi Masanin komai ne



Sura: Suratul An’am

Aya : 102

ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمۡۖ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ خَٰلِقُ كُلِّ شَيۡءٖ فَٱعۡبُدُوهُۚ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ وَكِيلٞ

Wannan Shi ne Allah Ubangijinku; ba wani abin bautawa da gaskiya sai Shi; Mahaliccin komai, don haka ku bauta masa. Kuma Shi Mai kiyayewa ne da komai



Sura: Suratul An’am

Aya : 103

لَّا تُدۡرِكُهُ ٱلۡأَبۡصَٰرُ وَهُوَ يُدۡرِكُ ٱلۡأَبۡصَٰرَۖ وَهُوَ ٱللَّطِيفُ ٱلۡخَبِيرُ

Gannai ba sa riskar Sa[1], Shi ne Yake riskar gannai, kuma Shi Mai tausasawa ne, Mai cikakken sani


1- A duniya babu wanda zai ga Allah quru-quru da idonsa. Amma a lahira muminai za su gan shi kamar yadda ya zo a Suratul Qiyama aya ta 22 zuwa 23. Hadisai masu yawa sun tabbatar da hakan.


Sura: Suratul An’am

Aya : 104

قَدۡ جَآءَكُم بَصَآئِرُ مِن رَّبِّكُمۡۖ فَمَنۡ أَبۡصَرَ فَلِنَفۡسِهِۦۖ وَمَنۡ عَمِيَ فَعَلَيۡهَاۚ وَمَآ أَنَا۠ عَلَيۡكُم بِحَفِيظٖ

Haqiqa hujjoji sun zo muku daga Ubangijinku; don haka duk wanda ya gan su (ya bi su), to ya yi don amfanin kansa ne; duk kuwa wanda ya makance, to kansa ya cuta. Kuma ni ba mai tsaron ku ba ne



Sura: Suratul An’am

Aya : 105

وَكَذَٰلِكَ نُصَرِّفُ ٱلۡأٓيَٰتِ وَلِيَقُولُواْ دَرَسۡتَ وَلِنُبَيِّنَهُۥ لِقَوۡمٖ يَعۡلَمُونَ

Kuma kamar haka ne Muke bayyana ayoyi, don (kafirai) su ce: “Ka koya ne (daga wasu littattafai)”, kuma don Mu bayyana shi (Alqur’ani) ga mutanen da suke ganewa



Sura: Suratul An’am

Aya : 106

ٱتَّبِعۡ مَآ أُوحِيَ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَۖ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ وَأَعۡرِضۡ عَنِ ٱلۡمُشۡرِكِينَ

Ka bi abin da aka yi maka wahayi daga Ubangijinka; ba abin bautawa da gaskiya sai Shi; kuma ka kawar da kai daga mushrikai



Sura: Suratul An’am

Aya : 107

وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ مَآ أَشۡرَكُواْۗ وَمَا جَعَلۡنَٰكَ عَلَيۡهِمۡ حَفِيظٗاۖ وَمَآ أَنتَ عَلَيۡهِم بِوَكِيلٖ

Kuma da Allah Ya ga dama, da ba su yi shirka ba. Ba Mu kuma sanya ka mai tsaro a kansu ba; kuma kai ba wakili ne a gare su ba



Sura: Suratul An’am

Aya : 108

وَلَا تَسُبُّواْ ٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ فَيَسُبُّواْ ٱللَّهَ عَدۡوَۢا بِغَيۡرِ عِلۡمٖۗ كَذَٰلِكَ زَيَّنَّا لِكُلِّ أُمَّةٍ عَمَلَهُمۡ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّهِم مَّرۡجِعُهُمۡ فَيُنَبِّئُهُم بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Kuma kada ku zagi waxanda suke bauta wa ba Allah ba, sai su zagi Allah saboda zalunci, ba tare da sanin (girmansa) ba. Kamar haka ne Muka qawata wa kowace al’umma ayyukansu (nagari da munana), sannan zuwa ga Ubangijinsu ne makomarsu take, sai Ya ba su labarin abin da suka kasance suna aikatawa



Sura: Suratul An’am

Aya : 109

وَأَقۡسَمُواْ بِٱللَّهِ جَهۡدَ أَيۡمَٰنِهِمۡ لَئِن جَآءَتۡهُمۡ ءَايَةٞ لَّيُؤۡمِنُنَّ بِهَاۚ قُلۡ إِنَّمَا ٱلۡأٓيَٰتُ عِندَ ٱللَّهِۖ وَمَا يُشۡعِرُكُمۡ أَنَّهَآ إِذَا جَآءَتۡ لَا يُؤۡمِنُونَ

Kuma sun rantse da Allah iyakar gaskiyarsu cewa, lalle idan har aya ta zo musu, tabbas za su yi imani da ita. Ka ce: “Ai ayoyi daga wajen Allah suke.” Kuma wa ya sanar da ku cewa, idan (ayoyin) sun zo ba za su yi imani ba?



Sura: Suratul An’am

Aya : 110

وَنُقَلِّبُ أَفۡـِٔدَتَهُمۡ وَأَبۡصَٰرَهُمۡ كَمَا لَمۡ يُؤۡمِنُواْ بِهِۦٓ أَوَّلَ مَرَّةٖ وَنَذَرُهُمۡ فِي طُغۡيَٰنِهِمۡ يَعۡمَهُونَ

Kuma za Mu riqa jujjuya zukatansu da gannansu, (daga fahimta da ganin gaskiya) kamar yadda ba su yi imani da shi ba da farko, Mu kuma bar su cikin shisshiginsu suna ximuwa