Sura: Suratu Yunus

Aya : 24

إِنَّمَا مَثَلُ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا كَمَآءٍ أَنزَلۡنَٰهُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ فَٱخۡتَلَطَ بِهِۦ نَبَاتُ ٱلۡأَرۡضِ مِمَّا يَأۡكُلُ ٱلنَّاسُ وَٱلۡأَنۡعَٰمُ حَتَّىٰٓ إِذَآ أَخَذَتِ ٱلۡأَرۡضُ زُخۡرُفَهَا وَٱزَّيَّنَتۡ وَظَنَّ أَهۡلُهَآ أَنَّهُمۡ قَٰدِرُونَ عَلَيۡهَآ أَتَىٰهَآ أَمۡرُنَا لَيۡلًا أَوۡ نَهَارٗا فَجَعَلۡنَٰهَا حَصِيدٗا كَأَن لَّمۡ تَغۡنَ بِٱلۡأَمۡسِۚ كَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يَتَفَكَّرُونَ

Misalin rayuwar duniya kawai kamar ruwa ne da Muka saukar da shi daga sama, to sai shukokin da suke kan qasa suka cuxanya da shi daga abin da mutane da dabbobi suke ci; har lokacin da qasa ta qawata (da shi) ta kuma yi ado; masu ita kuma suka sakankance cewa su masu ikon cin amfaninta ne, sai qaddararmu ta zo mata cikin dare ko rana, sai Muka mayar da ita girbabbiya kamar daxai ba ta rayu ba a jiya. Kamar haka Muke bayyana ayoyi ga mutanen da suke tunani



Sura: Suratu Yunus

Aya : 25

وَٱللَّهُ يَدۡعُوٓاْ إِلَىٰ دَارِ ٱلسَّلَٰمِ وَيَهۡدِي مَن يَشَآءُ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

Allah kuwa Yana kira ne zuwa gidan aminci (wato Aljanna), Yana kuma shiryar da wanda Ya ga dama zuwa tafarki madaidaici