Sura: Suratus Shura

Aya : 53

صِرَٰطِ ٱللَّهِ ٱلَّذِي لَهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ أَلَآ إِلَى ٱللَّهِ تَصِيرُ ٱلۡأُمُورُ

(Watau) tafarkin Allah wanda Yake da mulkin abin da yake cikin sammai da abin da yake qasa. Ku saurara, zuwa ga Allah ne kawai al’amura suke komawa



Sura: Suratuz Zukhruf 

Aya : 1

حمٓ

HA MIM[1]


1- Duba Suratul Baqara, aya ta 1, hashiya ta 8.


Sura: Suratuz Zukhruf 

Aya : 2

وَٱلۡكِتَٰبِ ٱلۡمُبِينِ

Na rantse da Littafi mabayyani (Alqur’ani)



Sura: Suratuz Zukhruf 

Aya : 3

إِنَّا جَعَلۡنَٰهُ قُرۡءَٰنًا عَرَبِيّٗا لَّعَلَّكُمۡ تَعۡقِلُونَ

Lalle Mu Mun sanya shi ya zamo abin karantawa cikin harshen Larabci domin ku hankalta



Sura: Suratuz Zukhruf 

Aya : 4

وَإِنَّهُۥ فِيٓ أُمِّ ٱلۡكِتَٰبِ لَدَيۡنَا لَعَلِيٌّ حَكِيمٌ

Lalle kuma shi (Alqur’ani) a cikin Littafi Lauhul-Mahafuzu a wurinmu tabbas maxaukaki ne, mai hikima



Sura: Suratuz Zukhruf 

Aya : 5

أَفَنَضۡرِبُ عَنكُمُ ٱلذِّكۡرَ صَفۡحًا أَن كُنتُمۡ قَوۡمٗا مُّسۡرِفِينَ

Yanzu Ma fasa saukar muku da Alqur’ani Mu watsar da ku, don kun kasance mutane masu yawan varna?



Sura: Suratuz Zukhruf 

Aya : 6

وَكَمۡ أَرۡسَلۡنَا مِن نَّبِيّٖ فِي ٱلۡأَوَّلِينَ

Annabi nawa Muka aika wa mutanen farko



Sura: Suratuz Zukhruf 

Aya : 7

وَمَا يَأۡتِيهِم مِّن نَّبِيٍّ إِلَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ

Ba kuma wani annabi da yakan zo musu sai sun kasance suna yi masa izgili



Sura: Suratuz Zukhruf 

Aya : 8

فَأَهۡلَكۡنَآ أَشَدَّ مِنۡهُم بَطۡشٗا وَمَضَىٰ مَثَلُ ٱلۡأَوَّلِينَ

Sai Muka hallakar da waxanda suka fi su tsananin qarfi[1], kuma bayanin yadda aka hallakar da mutanen farko ya riga ya shuxe


1- Watau kamar qabilun Adawa da Samudawa da mutanen Annabi Luxu ().


Sura: Suratuz Zukhruf 

Aya : 9

وَلَئِن سَأَلۡتَهُم مَّنۡ خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ لَيَقُولُنَّ خَلَقَهُنَّ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡعَلِيمُ

Lalle kuma idan ka tambaye su wane ne ya halicci sammai da qasa, to tabbas za su ce: “(Allah) ne Mabuwayi, Masani Ya halicce su.”



Sura: Suratuz Zukhruf 

Aya : 10

ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلۡأَرۡضَ مَهۡدٗا وَجَعَلَ لَكُمۡ فِيهَا سُبُلٗا لَّعَلَّكُمۡ تَهۡتَدُونَ

Wanda Ya sanya muku qasa ta zama shimfixa, Ya kuma sanya muku hanyoyi a cikinta don ku gane (inda za ku dosa)



Sura: Suratuz Zukhruf 

Aya : 11

وَٱلَّذِي نَزَّلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءَۢ بِقَدَرٖ فَأَنشَرۡنَا بِهِۦ بَلۡدَةٗ مَّيۡتٗاۚ كَذَٰلِكَ تُخۡرَجُونَ

Wanda kuma Ya saukar da ruwa daidai gwargwado daga sama sannan Muka raya mataccen gari da shi. Kamar haka ne za a fito da ku (daga qabarurruka)



Sura: Suratuz Zukhruf 

Aya : 12

وَٱلَّذِي خَلَقَ ٱلۡأَزۡوَٰجَ كُلَّهَا وَجَعَلَ لَكُم مِّنَ ٱلۡفُلۡكِ وَٱلۡأَنۡعَٰمِ مَا تَرۡكَبُونَ

Kuma wanda Ya halicci dukkan dangogin abubuwa bibbiyu, Ya kuma sanya muku daga jiragen ruwa da kuma dabbobin ni’ima, abubuwan da kuke hawa



Sura: Suratuz Zukhruf 

Aya : 13

لِتَسۡتَوُۥاْ عَلَىٰ ظُهُورِهِۦ ثُمَّ تَذۡكُرُواْ نِعۡمَةَ رَبِّكُمۡ إِذَا ٱسۡتَوَيۡتُمۡ عَلَيۡهِ وَتَقُولُواْ سُبۡحَٰنَ ٱلَّذِي سَخَّرَ لَنَا هَٰذَا وَمَا كُنَّا لَهُۥ مُقۡرِنِينَ

Don ku daidaita a kan bayansu, sannan ku tuna ni’imar Ubangijinku lokacin da kuka daidaita a kansu kuma ku ce: “Tsarki ya tabbata ga wanda Ya hore mana wannan, ba mu zamanto masu ikon sarrafa shi ba



Sura: Suratuz Zukhruf 

Aya : 14

وَإِنَّآ إِلَىٰ رَبِّنَا لَمُنقَلِبُونَ

“Kuma lalle zuwa ga Ubangijinmu tabbas za mu koma.”



Sura: Suratuz Zukhruf 

Aya : 15

وَجَعَلُواْ لَهُۥ مِنۡ عِبَادِهِۦ جُزۡءًاۚ إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ لَكَفُورٞ مُّبِينٌ

Kuma suka mai da wasu daga cikin bayinsa wani vangare nasa (wato `ya`yansa). Lalle mutum mai yawan butulci ne mai bayyana (butulcinsa)



Sura: Suratuz Zukhruf 

Aya : 16

أَمِ ٱتَّخَذَ مِمَّا يَخۡلُقُ بَنَاتٖ وَأَصۡفَىٰكُم بِٱلۡبَنِينَ

Yanzu Ya xauki `ya`ya mata daga abubuwan da Yake halitta, ku kuma Ya zava muku `ya`ya maza?



Sura: Suratuz Zukhruf 

Aya : 17

وَإِذَا بُشِّرَ أَحَدُهُم بِمَا ضَرَبَ لِلرَّحۡمَٰنِ مَثَلٗا ظَلَّ وَجۡهُهُۥ مُسۡوَدّٗا وَهُوَ كَظِيمٌ

Idan kuma aka yi wa xayansu albishir da abin da ya buga misali cewa na (Allah) Arrahmanu ne, sai fuskarsa ta yini a murtuke yana cike da baqin ciki



Sura: Suratuz Zukhruf 

Aya : 18

أَوَمَن يُنَشَّؤُاْ فِي ٱلۡحِلۡيَةِ وَهُوَ فِي ٱلۡخِصَامِ غَيۡرُ مُبِينٖ

Yanzu (sa danganta wa Allah) wanda da ake renon sa cikin kwalliya, alhali kuma idan an zo wajen husuma ba zai iya bayyana kansa (wajan ba da hujja) ba?



Sura: Suratuz Zukhruf 

Aya : 19

وَجَعَلُواْ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةَ ٱلَّذِينَ هُمۡ عِبَٰدُ ٱلرَّحۡمَٰنِ إِنَٰثًاۚ أَشَهِدُواْ خَلۡقَهُمۡۚ سَتُكۡتَبُ شَهَٰدَتُهُمۡ وَيُسۡـَٔلُونَ

Suka kuma mai da mala’iku waxanda suke bayin (Allah) Arrahmanu ne `ya`ya mata. Shin sun halarci sanda aka halicce su ne? To za a rubuta shaidarsu, za kuma a tambaye su (a lahira)



Sura: Suratuz Zukhruf 

Aya : 20

وَقَالُواْ لَوۡ شَآءَ ٱلرَّحۡمَٰنُ مَا عَبَدۡنَٰهُمۗ مَّا لَهُم بِذَٰلِكَ مِنۡ عِلۡمٍۖ إِنۡ هُمۡ إِلَّا يَخۡرُصُونَ

Suka kuma ce: “Da (Allah) Arrahmanu Ya ga dama, da ba mu bauta musu ba (wato mala’ikun).” Ba su da wani takamaiman ilimi a kan hakan; ba abin da suke yi sai shaci-faxi



Sura: Suratuz Zukhruf 

Aya : 21

أَمۡ ءَاتَيۡنَٰهُمۡ كِتَٰبٗا مِّن قَبۡلِهِۦ فَهُم بِهِۦ مُسۡتَمۡسِكُونَ

Ko kuma Mun ba su wani littafi ne gabaninsa (Alqur’ani), saboda haka suke riqe da shi qam-qam?



Sura: Suratuz Zukhruf 

Aya : 22

بَلۡ قَالُوٓاْ إِنَّا وَجَدۡنَآ ءَابَآءَنَا عَلَىٰٓ أُمَّةٖ وَإِنَّا عَلَىٰٓ ءَاثَٰرِهِم مُّهۡتَدُونَ

A’a, cewa dai suka yi: “Lalle mu mun sami iyayenmu a kan wani addini ne, mu kuma lalle sawunsu muke bi.”



Sura: Suratuz Zukhruf 

Aya : 23

وَكَذَٰلِكَ مَآ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ فِي قَرۡيَةٖ مِّن نَّذِيرٍ إِلَّا قَالَ مُتۡرَفُوهَآ إِنَّا وَجَدۡنَآ ءَابَآءَنَا عَلَىٰٓ أُمَّةٖ وَإِنَّا عَلَىٰٓ ءَاثَٰرِهِم مُّقۡتَدُونَ

Kuma kamar haka ne, ba Mu tava aiko wani mai gargaxi ba a wata alqarya a gabaninka sai ‘yan ta-moren cikinsu sun ce: “Lalle mu mun sami iyayenmu a kan wani addini, kuma lalle mu hanyarsu muke kwaikwayo.”