Sura: Suratu Luqman

Aya : 7

وَإِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِ ءَايَٰتُنَا وَلَّىٰ مُسۡتَكۡبِرٗا كَأَن لَّمۡ يَسۡمَعۡهَا كَأَنَّ فِيٓ أُذُنَيۡهِ وَقۡرٗاۖ فَبَشِّرۡهُ بِعَذَابٍ أَلِيمٍ

Idan kuma ana karanta masa ayoyinmu sai ya juya yana mai girman kai kamar bai ji su ba, kamar a ce akwai wani nauyi a cikin kunnuwansa; to ka yi masa albishir da azaba mai raxaxi



Sura: Suratu Luqman

Aya : 8

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ لَهُمۡ جَنَّـٰتُ ٱلنَّعِيمِ

Lalle waxanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari suna da (sakamakon) gidajen Aljanna na ni’ima



Sura: Suratu Luqman

Aya : 9

خَٰلِدِينَ فِيهَاۖ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٗاۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

Suna madawwama a cikinsu; alqawarin Allah kuwa gaskiya ne. Kuma Shi Mabuwayi ne, Mai hikima



Sura: Suratu Luqman

Aya : 10

خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ بِغَيۡرِ عَمَدٖ تَرَوۡنَهَاۖ وَأَلۡقَىٰ فِي ٱلۡأَرۡضِ رَوَٰسِيَ أَن تَمِيدَ بِكُمۡ وَبَثَّ فِيهَا مِن كُلِّ دَآبَّةٖۚ وَأَنزَلۡنَا مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَنۢبَتۡنَا فِيهَا مِن كُلِّ زَوۡجٖ كَرِيمٍ

Ya halicci sammai ba tare da wani ginshiqi da kuke ganin sa ba, Ya kuma kafa manya-manyan duwatsu a cikin qasa don kada ta riqa tangal-tangal da ku, Ya kuma yaxa kowace irin dabba a cikinta. Kuma Mun saukar da ruwa daga sama sai Muka tsirar da kowane irin dangin tsiro mai qayatarwa



Sura: Suratu Luqman

Aya : 11

هَٰذَا خَلۡقُ ٱللَّهِ فَأَرُونِي مَاذَا خَلَقَ ٱلَّذِينَ مِن دُونِهِۦۚ بَلِ ٱلظَّـٰلِمُونَ فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ

Wannan (ita ce) halittar Allah, sai ku nuna min abin da waxanda ba Shi ba suka halitta. A’a, su dai azzalumai suna cikin vata ne mabayyani



Sura: Suratu Luqman

Aya : 12

وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا لُقۡمَٰنَ ٱلۡحِكۡمَةَ أَنِ ٱشۡكُرۡ لِلَّهِۚ وَمَن يَشۡكُرۡ فَإِنَّمَا يَشۡكُرُ لِنَفۡسِهِۦۖ وَمَن كَفَرَ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَنِيٌّ حَمِيدٞ

Haqiqa kuma Mun bai wa Luqumanu[1] hikima cewa: “Ka yi godiya ga Allah. Kuma duk wanda yake godewa to yana godewa ne don kansa, wanda kuwa ya kafirta to lalle Allah Mawadaci ne, Sha-yabo.”


1- Wani salihin bawa ne da Allah ya hore masa hikima da ilimi. Wasu masana tarihi sun ce yarayu ne a zamanin Annabi Dawud ().


Sura: Suratu Luqman

Aya : 13

وَإِذۡ قَالَ لُقۡمَٰنُ لِٱبۡنِهِۦ وَهُوَ يَعِظُهُۥ يَٰبُنَيَّ لَا تُشۡرِكۡ بِٱللَّهِۖ إِنَّ ٱلشِّرۡكَ لَظُلۡمٌ عَظِيمٞ

Kuma (ka tuna) lokacin da Luqumanu ya ce da xansa a yayin da yake yi masa wa’azi: “Ya kai xanxana, kada ka yi shirka da Allah; lalle ita shirka zalunci ne mai girma



Sura: Suratu Luqman

Aya : 14

وَوَصَّيۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ بِوَٰلِدَيۡهِ حَمَلَتۡهُ أُمُّهُۥ وَهۡنًا عَلَىٰ وَهۡنٖ وَفِصَٰلُهُۥ فِي عَامَيۡنِ أَنِ ٱشۡكُرۡ لِي وَلِوَٰلِدَيۡكَ إِلَيَّ ٱلۡمَصِيرُ

Kuma Mun yi wa mutum wasiyya game da iyayensa, mahaifiyarsa ta xauke shi a cikinta rauni a kan rauni, yaye shi kuwa a cikin shekara biyu ne, saboda haka ka gode min da kuma iyayenka, makoma gare Ni take



Sura: Suratu Luqman

Aya : 15

وَإِن جَٰهَدَاكَ عَلَىٰٓ أَن تُشۡرِكَ بِي مَا لَيۡسَ لَكَ بِهِۦ عِلۡمٞ فَلَا تُطِعۡهُمَاۖ وَصَاحِبۡهُمَا فِي ٱلدُّنۡيَا مَعۡرُوفٗاۖ وَٱتَّبِعۡ سَبِيلَ مَنۡ أَنَابَ إِلَيَّۚ ثُمَّ إِلَيَّ مَرۡجِعُكُمۡ فَأُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

Idan kuma suka matsa maka kan ka yi tarayya da Ni game da abin da ba ka da wani sani a kansa, to kada ka bi su; kuma ka yi zaman duniya da su ta kyakkyawar hanya; ka kuma bi hanyar wanda ya mayar da al’amarinsa gare Ni. Sannan kuma zuwa gare Ni ne kawai makomarku, sai in ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa



Sura: Suratu Luqman

Aya : 16

يَٰبُنَيَّ إِنَّهَآ إِن تَكُ مِثۡقَالَ حَبَّةٖ مِّنۡ خَرۡدَلٖ فَتَكُن فِي صَخۡرَةٍ أَوۡ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ أَوۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ يَأۡتِ بِهَا ٱللَّهُۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَطِيفٌ خَبِيرٞ

(Luqumanu ya ci gaba da cewa): “Ya kai xanxana, lalle ita (kyakkyawa ko mummuna) in ta kasance daidai da qwayar komayya, sannan kuma ta zamanto cikin qaton dutse ko kuma cikin sammai ko cikin qasa, to Allah zai zo da ita. Lalle Allah Mai tausasawa ne, Masanin (komai)



Sura: Suratu Luqman

Aya : 17

يَٰبُنَيَّ أَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ وَأۡمُرۡ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَٱنۡهَ عَنِ ٱلۡمُنكَرِ وَٱصۡبِرۡ عَلَىٰ مَآ أَصَابَكَۖ إِنَّ ذَٰلِكَ مِنۡ عَزۡمِ ٱلۡأُمُورِ

“Ya kai xanxana, ka tsayar da salla kuma ka yi umarni da aikata alheri, ka kuma hana aikata mummunan aiki, kuma ka yi haquri bisa duk abin da ya same ka; lalle wannan yana daga manyan al’amura



Sura: Suratu Luqman

Aya : 18

وَلَا تُصَعِّرۡ خَدَّكَ لِلنَّاسِ وَلَا تَمۡشِ فِي ٱلۡأَرۡضِ مَرَحًاۖ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ كُلَّ مُخۡتَالٖ فَخُورٖ

“Kada kuma ka riqa xauke wa mutane fuskarka[1], kuma kada ka yi tafiya a ban qasa kana mai taqama. Lalle Allah ba Ya son duk wani mai taqama, mai fariya


1- Watau yana umartar sa da ya zama mai sakin fuska da haba-haba da jama’a.


Sura: Suratu Luqman

Aya : 19

وَٱقۡصِدۡ فِي مَشۡيِكَ وَٱغۡضُضۡ مِن صَوۡتِكَۚ إِنَّ أَنكَرَ ٱلۡأَصۡوَٰتِ لَصَوۡتُ ٱلۡحَمِيرِ

“Kuma ka tsakaita tafiyarka, kuma ka yi qasa-qasa da muryarka. Lalle mafi munin muryoyi ita ce muryar jakai.”



Sura: Suratu Luqman

Aya : 20

أَلَمۡ تَرَوۡاْ أَنَّ ٱللَّهَ سَخَّرَ لَكُم مَّا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَأَسۡبَغَ عَلَيۡكُمۡ نِعَمَهُۥ ظَٰهِرَةٗ وَبَاطِنَةٗۗ وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يُجَٰدِلُ فِي ٱللَّهِ بِغَيۡرِ عِلۡمٖ وَلَا هُدٗى وَلَا كِتَٰبٖ مُّنِيرٖ

Yanzu ba kwa gani cewa Allah Ya hore muku abin da yake cikin sammai da kuma abin da yake cikin qasa, Ya kuma cika muku ni’imominsa na sarari da na voye? Daga mutane kuma akwai waxanda suke jayayya game da Allah ba tare da wani ilimi ko wata shiriya ba, ba kuma tare da wani littafi mai haskakawa ba



Sura: Suratu Luqman

Aya : 21

وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ٱتَّبِعُواْ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ قَالُواْ بَلۡ نَتَّبِعُ مَا وَجَدۡنَا عَلَيۡهِ ءَابَآءَنَآۚ أَوَلَوۡ كَانَ ٱلشَّيۡطَٰنُ يَدۡعُوهُمۡ إِلَىٰ عَذَابِ ٱلسَّعِيرِ

Idan kuma aka ce da su: “Ku bi abin da Allah Ya saukar”, sai su ce: “A’a, mu muna bin abin da muka sami iyayenmu ne a kansa.” Yanzu (sa yi haka) ko da Shaixan ya zamanto yana kiran su zuwa ga azaba ta (wuta) mai ruruwa?