إِنَّهُمۡ كَانُوٓاْ إِذَا قِيلَ لَهُمۡ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا ٱللَّهُ يَسۡتَكۡبِرُونَ
Lalle sun kasance idan aka ce da su: “Babu abin bauta wa da gaskiya sai Allah,” sai su riqa yin girman kai
Tarayya :
وَيَقُولُونَ أَئِنَّا لَتَارِكُوٓاْ ءَالِهَتِنَا لِشَاعِرٖ مَّجۡنُونِۭ
Su kuma riqa cewa: “Yanzu ma bar allolinmu don wani mawaqi mai tavin hankali?”
بَلۡ جَآءَ بِٱلۡحَقِّ وَصَدَّقَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Ba haka ba ne, ya dai zo ne da gaskiya, ya kuma gaskata manzanni
إِنَّكُمۡ لَذَآئِقُواْ ٱلۡعَذَابِ ٱلۡأَلِيمِ
Lalle ku tabbas za ku xanxani azaba mai tsanani
وَمَا تُجۡزَوۡنَ إِلَّا مَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Ba kuwa za a saka muku ba sai da irin abin da kuka kasance kuna aikatawa
إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلۡمُخۡلَصِينَ
Sai dai bayin Allah waxanda aka tsarkake
أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ رِزۡقٞ مَّعۡلُومٞ
Waxannan suna da arziki sananne
فَوَٰكِهُ وَهُم مُّكۡرَمُونَ
(Shi ne) kayan marmari; su kuma ababen karramawa ne
فِي جَنَّـٰتِ ٱلنَّعِيمِ
A cikin gidajen Aljanna na ni’ima
عَلَىٰ سُرُرٖ مُّتَقَٰبِلِينَ
A kan gadaje suna fuskantar juna
يُطَافُ عَلَيۡهِم بِكَأۡسٖ مِّن مَّعِينِۭ
Ana zagaya su da kofuna na giya
بَيۡضَآءَ لَذَّةٖ لِّلشَّـٰرِبِينَ
Fara fat, ga kuma daxi ga masu sha
لَا فِيهَا غَوۡلٞ وَلَا هُمۡ عَنۡهَا يُنزَفُونَ
Babu sa ciwon kai a gare ta, kuma ba za a bugar da su da ita ba
وَعِندَهُمۡ قَٰصِرَٰتُ ٱلطَّرۡفِ عِينٞ
A wurinsu kuma akwai mataye masu taqaita kallonsu ga mazajensu, masu qwala-qwalan ido
كَأَنَّهُنَّ بَيۡضٞ مَّكۡنُونٞ
Kai ka ce su wani qwai ne a cikin kwasfa
فَأَقۡبَلَ بَعۡضُهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖ يَتَسَآءَلُونَ
Sannan sashinsu ya fuskanci shashi suna tambayar juna
قَالَ قَآئِلٞ مِّنۡهُمۡ إِنِّي كَانَ لِي قَرِينٞ
Wani daga cikinsu ya ce: “Lalle a da can ina da wani aboki
يَقُولُ أَءِنَّكَ لَمِنَ ٱلۡمُصَدِّقِينَ
“Da yake cewa: ‘Yanzu kai kana cikin masu ba da gaskiya?
أَءِذَا مِتۡنَا وَكُنَّا تُرَابٗا وَعِظَٰمًا أَءِنَّا لَمَدِينُونَ
“Yanzu idan muka mutu muka zama qasa da qasusuwa shin ko za a iya yi mana wani sakamako?’”
قَالَ هَلۡ أَنتُم مُّطَّلِعُونَ
Ya ce: “Shin ko za ku leqa ne?”
فَٱطَّلَعَ فَرَءَاهُ فِي سَوَآءِ ٱلۡجَحِيمِ
Sai shi ya leqa, sai kuwa ya gan shi a tsakiyar wuta
قَالَ تَٱللَّهِ إِن كِدتَّ لَتُرۡدِينِ
Ya ce: “Wallahi ka kusa ka hallakar da ni
وَلَوۡلَا نِعۡمَةُ رَبِّي لَكُنتُ مِنَ ٱلۡمُحۡضَرِينَ
“Ba don rahamar Ubangijina ba, da lalle ni ma na zama cikin ‘yan wuta.”
أَفَمَا نَحۡنُ بِمَيِّتِينَ
(Sai ‘yan Aljanna su ce da juna): “Ashe yanzu ba za mu sake mutuwa ba?
إِلَّا مَوۡتَتَنَا ٱلۡأُولَىٰ وَمَا نَحۡنُ بِمُعَذَّبِينَ
“Sai fa mutuwarmu ta farko, ba kuma za a azabtar da mu ba?”
إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ
Lalle wannan shi ne babban rabo
لِمِثۡلِ هَٰذَا فَلۡيَعۡمَلِ ٱلۡعَٰمِلُونَ
Don samun irin wannan lalle masu (kyakkyawan) aiki su yi aiki
أَذَٰلِكَ خَيۡرٞ نُّزُلًا أَمۡ شَجَرَةُ ٱلزَّقُّومِ
Shin wannan liyafa ita ce ta fi alheri ko kuwa bishiyar Zaqqum?
إِنَّا جَعَلۡنَٰهَا فِتۡنَةٗ لِّلظَّـٰلِمِينَ
Lalle Mu Mun sanya ta don ta zama fitina ga azzalumai
إِنَّهَا شَجَرَةٞ تَخۡرُجُ فِيٓ أَصۡلِ ٱلۡجَحِيمِ
Lalle ita wata bishiya ce da take fitowa a tsakiyar wutar Jahima