Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 13

ثُلَّةٞ مِّنَ ٱلۡأَوَّلِينَ

Su jama’a ne (masu yawa) daga (al’ummun) farko



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 14

وَقَلِيلٞ مِّنَ ٱلۡأٓخِرِينَ

Kuma kaxan ne daga (al’ummun) qarshe



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 15

عَلَىٰ سُرُرٖ مَّوۡضُونَةٖ

Suna kan gadaje masu adon zinari



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 16

مُّتَّكِـِٔينَ عَلَيۡهَا مُتَقَٰبِلِينَ

Suna kishingixe a kansu suna fuskantar juna



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 17

يَطُوفُ عَلَيۡهِمۡ وِلۡدَٰنٞ مُّخَلَّدُونَ

Yara samari dawwamammu (masu hidima) za su riqa zagaya su



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 18

بِأَكۡوَابٖ وَأَبَارِيقَ وَكَأۡسٖ مِّن مَّعِينٖ

Da kofuna (marasa mariqai) da butoci masu hannaye da kuma qoquna na giya



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 19

لَّا يُصَدَّعُونَ عَنۡهَا وَلَا يُنزِفُونَ

Ba sa ciwon kai saboda ita, kuma ba sa buguwa



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 20

وَفَٰكِهَةٖ مِّمَّا يَتَخَيَّرُونَ

Da kuma ababan marmari na abin da suke so su zava



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 21

وَلَحۡمِ طَيۡرٖ مِّمَّا يَشۡتَهُونَ

Da kuma naman tsuntsaye na abin da suke sha’awa



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 22

وَحُورٌ عِينٞ

Da kuma matan Hurul-Ini



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 23

كَأَمۡثَٰلِ ٱللُّؤۡلُوِٕ ٱلۡمَكۡنُونِ

Kamar misalin lu’ulu’u da yake cikin kwasfa



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 24

جَزَآءَۢ بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Sakamako ne na abin da suka kasance suna aikatawa



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 25

لَا يَسۡمَعُونَ فِيهَا لَغۡوٗا وَلَا تَأۡثِيمًا

Ba sa kuma jin wani zancen banza da mai sa zunubi a cikinta



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 26

إِلَّا قِيلٗا سَلَٰمٗا سَلَٰمٗا

Sai dai faxar salamun-salamun[1]


1- Watau sallamar mala’iku a gare su da wadda za su riqa yi wa junansu.


Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 27

وَأَصۡحَٰبُ ٱلۡيَمِينِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلۡيَمِينِ

Ma’abota hannun dama kuwa, mamakin darajar ma’abota hannun dama!



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 28

فِي سِدۡرٖ مَّخۡضُودٖ

Suna cikin ‘ya’yan itacen magarya marasa qaya



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 29

وَطَلۡحٖ مَّنضُودٖ

Da kuma ayaba mai ‘ya’ya dava-dava



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 30

وَظِلّٖ مَّمۡدُودٖ

Da inuwa madawwamiya



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 31

وَمَآءٖ مَّسۡكُوبٖ

Da kuma ruwa mai kwarara



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 32

وَفَٰكِهَةٖ كَثِيرَةٖ

Da ababen marmari masu yawa



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 33

لَّا مَقۡطُوعَةٖ وَلَا مَمۡنُوعَةٖ

Ba masu yankewa ba kuma ba ababen hanawa ba



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 34

وَفُرُشٖ مَّرۡفُوعَةٍ

Da shimfixu masu daraja



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 35

إِنَّآ أَنشَأۡنَٰهُنَّ إِنشَآءٗ

Lalle Mu ne Muka qage su (‘yan matan Aljanna) sabuwar qagowa



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 36

فَجَعَلۡنَٰهُنَّ أَبۡكَارًا

Sannan Muka sanya su budurwai



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 37

عُرُبًا أَتۡرَابٗا

Masu begen mazajensu, tsarekun juna



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 38

لِّأَصۡحَٰبِ ٱلۡيَمِينِ

Don ma’abota hannun dama



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 39

ثُلَّةٞ مِّنَ ٱلۡأَوَّلِينَ

Su jama’a ne (masu yawa) daga (al’ummun) farko



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 40

وَثُلَّةٞ مِّنَ ٱلۡأٓخِرِينَ

Kuma jama’a ne (masu yawa) daga (al’ummar) qarshe



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 41

وَأَصۡحَٰبُ ٱلشِّمَالِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلشِّمَالِ

Ma’abota hannun hagu kuma, mamakin qasqancin ma’abota hannun hagu!



Sura: Suratul Waqi’a

Aya : 42

فِي سَمُومٖ وَحَمِيمٖ

Suna cikin iska mai tsananin zafi da kuma tafasasshen ruwa