وَأَنَّ إِلَىٰ رَبِّكَ ٱلۡمُنتَهَىٰ
“Lalle kuma zuwa ga Ubangijinka ne makoma
Tarayya :
وَأَنَّهُۥ هُوَ أَضۡحَكَ وَأَبۡكَىٰ
“Kuma lalle Shi ne Ya sa a yi dariya, kuma Ya sa a yi kuka
وَأَنَّهُۥ هُوَ أَمَاتَ وَأَحۡيَا
“Kuma lalle Shi ne Ya kashe kuma Ya raya
وَأَنَّهُۥ خَلَقَ ٱلزَّوۡجَيۡنِ ٱلذَّكَرَ وَٱلۡأُنثَىٰ
“Kuma lalle Shi ne Ya halicci dangi biyu namiji da mace
مِن نُّطۡفَةٍ إِذَا تُمۡنَىٰ
“Daga maniyyi yayin da ake zuba shi
وَأَنَّ عَلَيۡهِ ٱلنَّشۡأَةَ ٱلۡأُخۡرَىٰ
“Kuma lalle Ya xora wa kansa sake tashin matattu
وَأَنَّهُۥ هُوَ أَغۡنَىٰ وَأَقۡنَىٰ
“Lalle kuma Shi ne Ya wadata, Ya kuma yalwata
وَأَنَّهُۥ هُوَ رَبُّ ٱلشِّعۡرَىٰ
“Kuma lalle Shi ne Ubangijin tauraron nan Shi’ira
وَأَنَّهُۥٓ أَهۡلَكَ عَادًا ٱلۡأُولَىٰ
“Lalle kuma Ya hallakar da Adawa na farko
وَثَمُودَاْ فَمَآ أَبۡقَىٰ
“Da kuma Samudawa, don haka bai bar saura ba
وَقَوۡمَ نُوحٖ مِّن قَبۡلُۖ إِنَّهُمۡ كَانُواْ هُمۡ أَظۡلَمَ وَأَطۡغَىٰ
“Da mutanen Nuhu tun kafin su; lalle su sun kasance su ne mafiya zalunci kuma mafiya xagawa
وَٱلۡمُؤۡتَفِكَةَ أَهۡوَىٰ
“Da waxanda aka kife (mutanen Luxu, Allah) ya qasqanta su
فَغَشَّىٰهَا مَا غَشَّىٰ
“Sannan abin da ya lulluve su (na azaba) ya lulluve su.”
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكَ تَتَمَارَىٰ
To (kai xan’adam) da waxanne ni’imomin Ubangijinka kake jayayya?
هَٰذَا نَذِيرٞ مِّنَ ٱلنُّذُرِ ٱلۡأُولَىٰٓ
Wannan mai gargaxi ne daga irin masu gargaxin farko
أَزِفَتِ ٱلۡأٓزِفَةُ
Mai kusantowa ta kusanto (watau alqiyama)
لَيۡسَ لَهَا مِن دُونِ ٱللَّهِ كَاشِفَةٌ
Ba wani mai bayyana lokacinta in ban da Allah
أَفَمِنۡ هَٰذَا ٱلۡحَدِيثِ تَعۡجَبُونَ
Yanzu game da wannan zancen ne[1] kuke mamaki?
1- Watau Alqur’ani mai girma.
وَتَضۡحَكُونَ وَلَا تَبۡكُونَ
Kuke kuma dariya ba kwa yin kuka?
وَأَنتُمۡ سَٰمِدُونَ
Alhali kuna cikin gafala?
فَٱسۡجُدُواْۤ لِلَّهِۤ وَٱعۡبُدُواْ۩
To ku yi sujjada ga Allah ku kuma bauta (masa)
ٱقۡتَرَبَتِ ٱلسَّاعَةُ وَٱنشَقَّ ٱلۡقَمَرُ
Alqiyama ta kusanto, wata kuma ya tsage[1]
1- Watau a zamanin Manzon Allah () wanda mushirikan Quraishawa suka gani da idonsu, bayan sun nemi ya nuna musu mu’ujiza.
وَإِن يَرَوۡاْ ءَايَةٗ يُعۡرِضُواْ وَيَقُولُواْ سِحۡرٞ مُّسۡتَمِرّٞ
Idan kuma suka ga wata aya sai su kau da kai kuma su ce: “Wannan sihiri ne qaqqarfa.”
وَكَذَّبُواْ وَٱتَّبَعُوٓاْ أَهۡوَآءَهُمۡۚ وَكُلُّ أَمۡرٖ مُّسۡتَقِرّٞ
Suka kuma qaryata, suka bi soye-soyen zukatansu. Kowane al’amari kuwa (na alheri ko na sharri) mai tabbata ne
وَلَقَدۡ جَآءَهُم مِّنَ ٱلۡأَنۢبَآءِ مَا فِيهِ مُزۡدَجَرٌ
Haqiqa kuma wasu labarai waxanda tsawatarwa take cikinsu sun zo musu
حِكۡمَةُۢ بَٰلِغَةٞۖ فَمَا تُغۡنِ ٱلنُّذُرُ
Hikima ce mai kaiwa matuqa, sai dai kuma gargaxin ba ya amfanarwa
فَتَوَلَّ عَنۡهُمۡۘ يَوۡمَ يَدۡعُ ٱلدَّاعِ إِلَىٰ شَيۡءٖ نُّكُرٍ
Saboda haka ka rabu da su. A ranar da mai kira[1] zai yi kira zuwa ga wani abu na qi a rai[2]
1- Shi ne Mala’ika Israfilu () mai busa a qaho.2- Watau lokacin fitowa daga qaburbura.
خُشَّعًا أَبۡصَٰرُهُمۡ يَخۡرُجُونَ مِنَ ٱلۡأَجۡدَاثِ كَأَنَّهُمۡ جَرَادٞ مُّنتَشِرٞ
Idanuwansu suna a qasqance suna fitowa daga qaburbura, kai ka ce su farin xango ne masu bazuwa
مُّهۡطِعِينَ إِلَى ٱلدَّاعِۖ يَقُولُ ٱلۡكَٰفِرُونَ هَٰذَا يَوۡمٌ عَسِرٞ
Suna gaggawa zuwa ga mai kiran; kafirai za su riqa cewa: “Wannan rana ce mai tsanani.”
۞كَذَّبَتۡ قَبۡلَهُمۡ قَوۡمُ نُوحٖ فَكَذَّبُواْ عَبۡدَنَا وَقَالُواْ مَجۡنُونٞ وَٱزۡدُجِرَ
Mutanen Nuhu sun qaryata kafin su (Quraishawa), sai suka qaryata Bawanmu suka kuma ce, mahaukaci ne, aka kuma kyare (shi)