وَمَا لَا تُبۡصِرُونَ
Da kuma abin da ba kwa gani
Tarayya :
إِنَّهُۥ لَقَوۡلُ رَسُولٖ كَرِيمٖ
Lalle shi (Alqur’ani) tabbas zance ne na wani manzo mai girma
وَمَا هُوَ بِقَوۡلِ شَاعِرٖۚ قَلِيلٗا مَّا تُؤۡمِنُونَ
Shi kuwa ba zancen mawaqi ba ne. Kaxan ne qwarai kuke yin imani
وَلَا بِقَوۡلِ كَاهِنٖۚ قَلِيلٗا مَّا تَذَكَّرُونَ
Ba kuma zance ne na boka ba. Kaxan ne qwarai kuke wa’azantuwa
تَنزِيلٞ مِّن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Shi saukakke ne daga Ubangijin halittu
وَلَوۡ تَقَوَّلَ عَلَيۡنَا بَعۡضَ ٱلۡأَقَاوِيلِ
Kuma da ya qaga Mana wasu maganganu
لَأَخَذۡنَا مِنۡهُ بِٱلۡيَمِينِ
Tabbas da Mun kama shi da qarfi
ثُمَّ لَقَطَعۡنَا مِنۡهُ ٱلۡوَتِينَ
Sannan da Mun yanke masa jijiyar zuciyarsa
فَمَا مِنكُم مِّنۡ أَحَدٍ عَنۡهُ حَٰجِزِينَ
Sannan kuma ba wani xaya daga cikinku da zai kare shi
وَإِنَّهُۥ لَتَذۡكِرَةٞ لِّلۡمُتَّقِينَ
Lalle shi (Alqur’ani) wa’azi ne ga masu kiyaye dokokin Allah
وَإِنَّا لَنَعۡلَمُ أَنَّ مِنكُم مُّكَذِّبِينَ
Lalle kuma Mu Muna sane da cewa a cikinku akwai masu qaryatawa
وَإِنَّهُۥ لَحَسۡرَةٌ عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ
Kuma lalle shi tabbas nadama ce ga kafirai
وَإِنَّهُۥ لَحَقُّ ٱلۡيَقِينِ
Kuma lalle shi tabbas gaskiya ce ta sakankancewa
فَسَبِّحۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلۡعَظِيمِ
Saboda haka ka yi tasbihi da sunan Ubangijinka Mai girma
سَأَلَ سَآئِلُۢ بِعَذَابٖ وَاقِعٖ
Mai tambaya ya yi tambaya game da wata azaba mai aukuwa[1]
1- Watau wadda Annabi () yake musu kashedi da ita idan sun qi imani. Duba Suratul Anfal, aya ta 32. Mai tambayar kuwa shi ne Nadhru xan Haris.
لِّلۡكَٰفِرِينَ لَيۡسَ لَهُۥ دَافِعٞ
Ga kafirai (wadda) ba ta da wani mai kaxe ta
مِّنَ ٱللَّهِ ذِي ٱلۡمَعَارِجِ
Daga Allah Mai matattakalai
تَعۡرُجُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ وَٱلرُّوحُ إِلَيۡهِ فِي يَوۡمٖ كَانَ مِقۡدَارُهُۥ خَمۡسِينَ أَلۡفَ سَنَةٖ
Mala’iku tare da Jibrilu suna hawa zuwa gare Shi a cikin wata rana (wadda) gwargwadonta yake daidai da shekara dubu hamsin
فَٱصۡبِرۡ صَبۡرٗا جَمِيلًا
Sai ka yi haquri kyakkyawan haquri
إِنَّهُمۡ يَرَوۡنَهُۥ بَعِيدٗا
Lalle su suna ganin ta mai nisa ce
وَنَرَىٰهُ قَرِيبٗا
Mu kuma Muna ganin ta kusa-kusa
يَوۡمَ تَكُونُ ٱلسَّمَآءُ كَٱلۡمُهۡلِ
A ranar da sama za ta kasance kamar narkakkiyar dalma
وَتَكُونُ ٱلۡجِبَالُ كَٱلۡعِهۡنِ
Duwatsu kuma su zama kamar kaxaxxiyar auduga (ta gashin tumaki)
وَلَا يَسۡـَٔلُ حَمِيمٌ حَمِيمٗا
Kuma aboki ba ya tambayar aboki
يُبَصَّرُونَهُمۡۚ يَوَدُّ ٱلۡمُجۡرِمُ لَوۡ يَفۡتَدِي مِنۡ عَذَابِ يَوۡمِئِذِۭ بِبَنِيهِ
(Alhali kuma) ana nuna musu junansu. Mai laifi ya riqa burin ina ma zai fanshi kansa daga azabar wannan rana da ‘ya’yansa
وَصَٰحِبَتِهِۦ وَأَخِيهِ
Da matarsa da xan’uwansa
وَفَصِيلَتِهِ ٱلَّتِي تُـٔۡوِيهِ
Da danginsa waxanda suke kare shi
وَمَن فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗا ثُمَّ يُنجِيهِ
Da ma duk wanda yake a bayan qasa baki xaya, sannan (fansar) ta tserar da shi
كَلَّآۖ إِنَّهَا لَظَىٰ
Faufau! Lalle ita (wutar) Laza ce
نَزَّاعَةٗ لِّلشَّوَىٰ
Mai xaxxaye fatar kai