وَأُمِّهِۦ وَأَبِيهِ
Da uwarsa da ubansa
Tarayya :
وَصَٰحِبَتِهِۦ وَبَنِيهِ
Da matarsa da ‘ya’yansa
لِكُلِّ ٱمۡرِيٕٖ مِّنۡهُمۡ يَوۡمَئِذٖ شَأۡنٞ يُغۡنِيهِ
Kowane mutum daga cikinsu a wannan ranar yana da lamarin da ya sha kansa
وُجُوهٞ يَوۡمَئِذٖ مُّسۡفِرَةٞ
Wasu fuskoki a wannan ranar masu haske ne
ضَاحِكَةٞ مُّسۡتَبۡشِرَةٞ
Masu dariya, masu farin ciki
وَوُجُوهٞ يَوۡمَئِذٍ عَلَيۡهَا غَبَرَةٞ
Wasu fuskokin kuma a ranar akwai qura a kansu
تَرۡهَقُهَا قَتَرَةٌ
Baqin ciki zai lulluve su
أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡكَفَرَةُ ٱلۡفَجَرَةُ
Waxannan su ne kafirai mavarnata
إِذَا ٱلشَّمۡسُ كُوِّرَتۡ
Idan rana aka naxe ta[1]
1- Watau aka haxa ta da wata wuri xaya, aka kuma tafiyar da haskenta.
وَإِذَا ٱلنُّجُومُ ٱنكَدَرَتۡ
Idan kuma taurari suka farfaxo
وَإِذَا ٱلۡجِبَالُ سُيِّرَتۡ
Idan kuma duwatsu aka tafiyar da su
وَإِذَا ٱلۡعِشَارُ عُطِّلَتۡ
Idan kuma raquma masu ciki aka bar su ba makiyayi
وَإِذَا ٱلۡوُحُوشُ حُشِرَتۡ
Idan kuma namun daji aka tattara su[1]
1- Watau aka tattara su wuri guda tare da ‘yan’adam.
وَإِذَا ٱلۡبِحَارُ سُجِّرَتۡ
Idan kuma koguna aka rura su (suka zama wuta)
وَإِذَا ٱلنُّفُوسُ زُوِّجَتۡ
Idan kuma rayuka aka haxa su (da jinsinsu)
وَإِذَا ٱلۡمَوۡءُۥدَةُ سُئِلَتۡ
Idan kuma yarinyar da aka binne da rai aka tambaye ta
بِأَيِّ ذَنۢبٖ قُتِلَتۡ
Da wane laifi ne aka kashe ta?
وَإِذَا ٱلصُّحُفُ نُشِرَتۡ
Idan kuma takardun (ayyuka) aka baza su[1]
1- Watau don kowa ya karanta takardarsa da kansa.
وَإِذَا ٱلسَّمَآءُ كُشِطَتۡ
Idan kuma sama aka xaye ta
وَإِذَا ٱلۡجَحِيمُ سُعِّرَتۡ
Idan kuma wutar Jahimu aka hura ta
وَإِذَا ٱلۡجَنَّةُ أُزۡلِفَتۡ
Idan kuma Aljanna aka kusanto da ita[1]
1- Watau aka matso da ita dab da masu taqawa.
عَلِمَتۡ نَفۡسٞ مَّآ أَحۡضَرَتۡ
To kowane rai ya san abin da ya halarto (da shi na ayyuka)
فَلَآ أُقۡسِمُ بِٱلۡخُنَّسِ
To ina rantsuwa da taurari masu vuya[1]
1- Watau suna vuya lokacin hudowar hasken asuba, kamar yadda gada take voyewa a cikin gidanta.
ٱلۡجَوَارِ ٱلۡكُنَّسِ
Masu gudu zuwa masaukansu
وَٱلَّيۡلِ إِذَا عَسۡعَسَ
Da kuma dare idan ya yi duhu
وَٱلصُّبۡحِ إِذَا تَنَفَّسَ
Da kuma asuba idan ta keto
إِنَّهُۥ لَقَوۡلُ رَسُولٖ كَرِيمٖ
Lalle shi (Alqur’ani) magana ce ta Manzo mai karamci[1]
1- Watau Mala’ika Jibrilu () wanda Allah ya amince masa ya isar wa da Manzon Allah () zancensa.
ذِي قُوَّةٍ عِندَ ذِي ٱلۡعَرۡشِ مَكِينٖ
Ma’abocin qarfi a wurin Mai Al’arshi, kuma mai babban matsayi
مُّطَاعٖ ثَمَّ أَمِينٖ
Wanda ake yi wa biyayya ne a can (sama), amintacce
وَمَا صَاحِبُكُم بِمَجۡنُونٖ
Mutumin naku kuma (watau Ma’aiki) ba mahaukaci ba ne