نَحۡنُ جَعَلۡنَٰهَا تَذۡكِرَةٗ وَمَتَٰعٗا لِّلۡمُقۡوِينَ
Mu ne Muka sanya ta wa’azi da kuma abin amfani ga matafiya
فَسَبِّحۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلۡعَظِيمِ
Saboda haka sai ka tsarkake Sunan Ubangijinka Mai girma
۞فَلَآ أُقۡسِمُ بِمَوَٰقِعِ ٱلنُّجُومِ
To ina yin rantsuwa da mafaxar taurari
وَإِنَّهُۥ لَقَسَمٞ لَّوۡ تَعۡلَمُونَ عَظِيمٌ
Lalle ita kuwa rantsuwa ce mai girma, da kuna ganewa.[1]
1- Domin taurari da tafiyarsu a sararin sama abu ne mai cike da ayoyi da darussa masu ximbin yawa.
إِنَّهُۥ لَقُرۡءَانٞ كَرِيمٞ
Lalle shi Alqur’ani ne mai girma
فِي كِتَٰبٖ مَّكۡنُونٖ
A cikin littafi abin kiyayewa (daga wani sauyi).[1]
1- Shi ne Lauhul Mahfuz.
لَّا يَمَسُّهُۥٓ إِلَّا ٱلۡمُطَهَّرُونَ
Babu mai tava shi sai tsarkakakku
تَنزِيلٞ مِّن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Saukakke ne daga Ubangijin talikai
أَفَبِهَٰذَا ٱلۡحَدِيثِ أَنتُم مُّدۡهِنُونَ
Yanzu wannan zance kuke qaryatawa?
وَتَجۡعَلُونَ رِزۡقَكُمۡ أَنَّكُمۡ تُكَذِّبُونَ
Kuke kuma sanya (godiyar) arzikinku shi ne ku riqa qaryatawa?
فَلَوۡلَآ إِذَا بَلَغَتِ ٱلۡحُلۡقُومَ
Me ya hana idan (rai) ya isa maqogwaro
وَأَنتُمۡ حِينَئِذٖ تَنظُرُونَ
Ku kuma a lokacin kuna kallo
وَنَحۡنُ أَقۡرَبُ إِلَيۡهِ مِنكُمۡ وَلَٰكِن لَّا تُبۡصِرُونَ
Mu ne kuwa Muka fi ku kusanci da shi, sai dai kuma ba kwa gani
فَلَوۡلَآ إِن كُنتُمۡ غَيۡرَ مَدِينِينَ
Me ya hana idan da kun zamanto ba waxanda za a tasa ba ne
تَرۡجِعُونَهَآ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Ku dawo da shi (ran) mana idan kun kasance masu gaskiya
فَأَمَّآ إِن كَانَ مِنَ ٱلۡمُقَرَّبِينَ
Amma kuma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta
فَرَوۡحٞ وَرَيۡحَانٞ وَجَنَّتُ نَعِيمٖ
To (sakamakonsa) hutu ne da arziki mai daxi, da kuma Aljannar ni’ima
وَأَمَّآ إِن كَانَ مِنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلۡيَمِينِ
Idan kuma ya kasance daga ma’abota hannun dama ne
فَسَلَٰمٞ لَّكَ مِنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلۡيَمِينِ
To aminci ya tabbata a gare ka don zamanka na hannun dama
وَأَمَّآ إِن كَانَ مِنَ ٱلۡمُكَذِّبِينَ ٱلضَّآلِّينَ
Idan kuwa ya kasance daga masu qaryatawa ne vatattu
فَنُزُلٞ مِّنۡ حَمِيمٖ
To kavaki ne na tafasasshen ruwa (sakamakonsa)
وَتَصۡلِيَةُ جَحِيمٍ
Da kuma shiga wutar Jahannama
إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ حَقُّ ٱلۡيَقِينِ
Lalle wannan (bayani na cikin wannan Surar) shi ne haqiqanin gaskiya
فَسَبِّحۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلۡعَظِيمِ
To ka yi tasbihi da tsarkake sunan Ubangijinka mai girma
سَبَّحَ لِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ
Abin da yake cikin sammai da qasa ya yi tasbihi ga Allah; Shi ne kuma Mabuwayi, Mai hikima
لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ
Mulkin sammai da qasa nasa ne; Yana rayawa, Yana kuma kashewa; kuma Shi Mai iko ne a kan komai
هُوَ ٱلۡأَوَّلُ وَٱلۡأٓخِرُ وَٱلظَّـٰهِرُ وَٱلۡبَاطِنُۖ وَهُوَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٌ
Shi ne Na farko kuma Na qarshe, kuma Bayyananne kuma Voyayye[1]; Shi kuma Masanin komai ne
1- Na farko, watau babu wani abu gabaninsa. Na qarshe, watau babu wani abu bayansa. Bayyananne, watau babu wani abu sama da shi. Voyayye, watau babu wani abu da ya fi shi vuya.
هُوَ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٖ ثُمَّ ٱسۡتَوَىٰ عَلَى ٱلۡعَرۡشِۖ يَعۡلَمُ مَا يَلِجُ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَا يَخۡرُجُ مِنۡهَا وَمَا يَنزِلُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ وَمَا يَعۡرُجُ فِيهَاۖ وَهُوَ مَعَكُمۡ أَيۡنَ مَا كُنتُمۡۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ
Shi ne wanda Ya halicci sammai da qasa cikin kwana shida, sannan Ya daidaitu a kan Al’arshi. Yana sane da abin da yake shiga cikin qasa da abin da yake fitowa daga cikinta, da kuma abin da yake saukowa daga sama da abin da yake hawa cikinta; kuma Shi Yana tare da ku a duk inda kuka kasance[1]. Allah kuwa Mai ganin duk abin da kuke aikatawa ne
1- Watau da iliminsa. Babu wani abu da yake vuya a gare shi, yana kuma ganin duk abin da suke aikatawa.
لَّهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَإِلَى ٱللَّهِ تُرۡجَعُ ٱلۡأُمُورُ
Mulkin sammai da qasa nasa ne. Kuma ga Allah ake mayar da al’amura
يُولِجُ ٱلَّيۡلَ فِي ٱلنَّهَارِ وَيُولِجُ ٱلنَّهَارَ فِي ٱلَّيۡلِۚ وَهُوَ عَلِيمُۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ
Yana shigar da dare cikin rana, Yana kuma shigar da rana cikin dare. Kuma Shi Masanin abubuwan da suke cikin qiraza ne