Sura: Suratul Fatiha

Aya : 1

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin qai[1]


1- Bisimilla Alqur’ani ce, kuma aya ce a ‘Suratun Namli aya ta 30’; sannan ita aya ce a farkon ‘Suratul Fatiha’, sannan an saukar da ita a farkon kowace sura don bambance tsakanin qarshen sura da farkon wata sura. Amma ban da tsakanin ‘Suratul Anfal’ da ‘Taubah’.


Sura: Suratul Fatiha

Aya : 2

ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai



Sura: Suratul Fatiha

Aya : 3

ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

Mai rahama Mai jin qai[1]


1- Allah, suna ne na wanda ya cancanta a bauta masa shi kaxai. Ba a kiran wani da shi. Arrahman wanda yake nuna yalwatacciyar rahmar Allah wadda take shafar kowa da komai a nan duniya da kuma sunansa Arrahim, wanda yake nuna kevantacciyar rahamarsa a lahira ga muminai kawai masu tsoran sa.


Sura: Suratul Fatiha

Aya : 4

مَٰلِكِ يَوۡمِ ٱلدِّينِ

Mamallakin ranar sakamako



Sura: Suratul Fatiha

Aya : 5

إِيَّاكَ نَعۡبُدُ وَإِيَّاكَ نَسۡتَعِينُ

Kai kaxai muke bautata wa, kuma Kai kaxai muke neman taimakonka



Sura: Suratul Fatiha

Aya : 6

ٱهۡدِنَا ٱلصِّرَٰطَ ٱلۡمُسۡتَقِيمَ

Ka shiryar da mu tafarkin nan madaidaici



Sura: Suratul Fatiha

Aya : 7

صِرَٰطَ ٱلَّذِينَ أَنۡعَمۡتَ عَلَيۡهِمۡ غَيۡرِ ٱلۡمَغۡضُوبِ عَلَيۡهِمۡ وَلَا ٱلضَّآلِّينَ

Tafarkin waxanda Ka yi wa ni’ima[1], ba waxanda aka yi fushi da su ba[2], ba kuma vatattu ba[3]


1- Su ne waxanda aka ambata a aya ta 69 a Suratun Nisa’i.


2- Watau waxanda suka san gaskiya suka take, kamar Yahudawa.


3- Watau waxanda suke bautar Allah da jahilci, kamar Nasara.


Sura: Suratul Baqara

Aya : 1

الٓمٓ

ALIF LAM MIM[1]


1- Allah () ya buxe wannan Sura da harufan Alif da Lam da Mim. Hakanan akwai surorin da dama da Allah ya buxe su da irin waxannan datsattsun haruffa. Allah ne kaxai ya san haqiqanin abin da yake nufi da su. Wasu malamai na cewa, Allah yana nuna mu’ujizar Alqurani ne da irin waxannan haruffa.


Sura: Suratul Baqara

Aya : 2

ذَٰلِكَ ٱلۡكِتَٰبُ لَا رَيۡبَۛ فِيهِۛ هُدٗى لِّلۡمُتَّقِينَ

Wannan littafin babu wani kokwanto a cikinsa; shiriya ne ga masu taqawa[1]


1- Taqawa tana nufin aikata abin Allah ya wajabta da nisantar abin da ya haramta.


Sura: Suratul Baqara

Aya : 3

ٱلَّذِينَ يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡغَيۡبِ وَيُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَمِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ يُنفِقُونَ

Waxanda suke yin imani da gaibi kuma suke tsayar da salla kuma suke ciyarwa daga abin da Muka arzuta su da shi



Sura: Suratul Baqara

Aya : 4

وَٱلَّذِينَ يُؤۡمِنُونَ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ وَمَآ أُنزِلَ مِن قَبۡلِكَ وَبِٱلۡأٓخِرَةِ هُمۡ يُوقِنُونَ

Waxanda suke yin imani da abin da aka saukar maka da abin da aka saukar a gabaninka, kuma suke sakankancewa da ranar lahira



Sura: Suratul Baqara

Aya : 5

أُوْلَـٰٓئِكَ عَلَىٰ هُدٗى مِّن رَّبِّهِمۡۖ وَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ

Waxannan suna kan (babbar) shiriya daga Ubangijinsu, kuma waxannan su ne masu samun babban rabo



Sura: Suratul Baqara

Aya : 6

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ سَوَآءٌ عَلَيۡهِمۡ ءَأَنذَرۡتَهُمۡ أَمۡ لَمۡ تُنذِرۡهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ

Lalle waxanda suka kafirta, duk xaya ne a gare su, ka yi musu gargaxi ko ba ka yi musu ba, ba za su yi imani ba



Sura: Suratul Baqara

Aya : 7

خَتَمَ ٱللَّهُ عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ وَعَلَىٰ سَمۡعِهِمۡۖ وَعَلَىٰٓ أَبۡصَٰرِهِمۡ غِشَٰوَةٞۖ وَلَهُمۡ عَذَابٌ عَظِيمٞ

Allah Ya toshe zukatansu da jinsu, kuma akwai wani lulluvi a kan idanunsu, kuma suna da azaba mai girma



Sura: Suratul Baqara

Aya : 8

وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَقُولُ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ وَبِٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَمَا هُم بِمُؤۡمِنِينَ

A cikin mutane kuma akwai waxanda suke cewa: “Mun yi imani da Allah kuma mun yi imani da ranar lahira,” alhalin su ba muminai ne ba



Sura: Suratul Baqara

Aya : 9

يُخَٰدِعُونَ ٱللَّهَ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَمَا يَخۡدَعُونَ إِلَّآ أَنفُسَهُمۡ وَمَا يَشۡعُرُونَ

Suna ganin suna yaudarar Allah ne da waxanda suka yi imani, amma kuwa ba kowa suke yaudara ba sai kawunansu, kuma su ba sa jin hakan



Sura: Suratul Baqara

Aya : 10

فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٞ فَزَادَهُمُ ٱللَّهُ مَرَضٗاۖ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمُۢ بِمَا كَانُواْ يَكۡذِبُونَ

Akwai wata cuta (ta munafunci) a cikin zukatansu, sai Allah Ya qara musu wata cutar, kuma suna da wata azaba mai raxaxi saboda qaryar da suke yi



Sura: Suratul Baqara

Aya : 11

وَإِذَا قِيلَ لَهُمۡ لَا تُفۡسِدُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ قَالُوٓاْ إِنَّمَا نَحۡنُ مُصۡلِحُونَ

Idan kuma aka ce musu: “Kada ku yi varna a bayan qasa”, sai su ce: “Mu fa masu gyara ne kawai.”



Sura: Suratul Baqara

Aya : 12

أَلَآ إِنَّهُمۡ هُمُ ٱلۡمُفۡسِدُونَ وَلَٰكِن لَّا يَشۡعُرُونَ

Saurara, lalle su su ne mavarnata, amma ba sa jin hakan



Sura: Suratul Baqara

Aya : 13

وَإِذَا قِيلَ لَهُمۡ ءَامِنُواْ كَمَآ ءَامَنَ ٱلنَّاسُ قَالُوٓاْ أَنُؤۡمِنُ كَمَآ ءَامَنَ ٱلسُّفَهَآءُۗ أَلَآ إِنَّهُمۡ هُمُ ٱلسُّفَهَآءُ وَلَٰكِن لَّا يَعۡلَمُونَ

Idan kuma aka ce da su: “Ku yi imani kamar yadda mutane suka yi imani”, sai su ce: “Shin za mu yi imani ne kamar yadda wawaye suka yi imani?” Saurara, lalle su ne wawayen, sai dai ba sa sanin (hakan)



Sura: Suratul Baqara

Aya : 14

وَإِذَا لَقُواْ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ قَالُوٓاْ ءَامَنَّا وَإِذَا خَلَوۡاْ إِلَىٰ شَيَٰطِينِهِمۡ قَالُوٓاْ إِنَّا مَعَكُمۡ إِنَّمَا نَحۡنُ مُسۡتَهۡزِءُونَ

Idan kuma suka haxu da waxanda suka yi imani sai su ce: “Mun yi imani.” To amma idan suka kevanta da shaixanunsu (iyayen gidansu)[1] sai su ce: “Mu fa lalle muna nan tare da ku, mu kawai izgili ne muke yi.”


1- Shexanunsu, su ne manyan kafirai da Yahudawa.


Sura: Suratul Baqara

Aya : 15

ٱللَّهُ يَسۡتَهۡزِئُ بِهِمۡ وَيَمُدُّهُمۡ فِي طُغۡيَٰنِهِمۡ يَعۡمَهُونَ

Allah Yana yi musu izgili, kuma Yana yi musu talala cikin shisshiginsu suna masu ximuwa



Sura: Suratul Baqara

Aya : 16

أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ ٱشۡتَرَوُاْ ٱلضَّلَٰلَةَ بِٱلۡهُدَىٰ فَمَا رَبِحَت تِّجَٰرَتُهُمۡ وَمَا كَانُواْ مُهۡتَدِينَ

Waxannan su ne suka musanya shiriya da vata, don haka kasuwancinsu bai yi riba ba, kuma ba su zamo shiryayyu ba



Sura: Suratul Baqara

Aya : 17

مَثَلُهُمۡ كَمَثَلِ ٱلَّذِي ٱسۡتَوۡقَدَ نَارٗا فَلَمَّآ أَضَآءَتۡ مَا حَوۡلَهُۥ ذَهَبَ ٱللَّهُ بِنُورِهِمۡ وَتَرَكَهُمۡ فِي ظُلُمَٰتٖ لَّا يُبۡصِرُونَ

Misalinsu kamar misalin wanda ya wahala har ya kunna wuta ne, yayin da ta haskaka abin da yake daura da shi, sai Allah Ya tafiyar da haskensu Ya bar su cikin duffai ba sa gani



Sura: Suratul Baqara

Aya : 18

صُمُّۢ بُكۡمٌ عُمۡيٞ فَهُمۡ لَا يَرۡجِعُونَ

( Su ) kurame ne, bebaye ne, makafi ne, don haka ba za su tava dawowa (kan gaskiya) ba



Sura: Suratul Baqara

Aya : 19

أَوۡ كَصَيِّبٖ مِّنَ ٱلسَّمَآءِ فِيهِ ظُلُمَٰتٞ وَرَعۡدٞ وَبَرۡقٞ يَجۡعَلُونَ أَصَٰبِعَهُمۡ فِيٓ ءَاذَانِهِم مِّنَ ٱلصَّوَٰعِقِ حَذَرَ ٱلۡمَوۡتِۚ وَٱللَّهُ مُحِيطُۢ بِٱلۡكَٰفِرِينَ

Ko kuma (misalinsu) kamar wani mamakon ruwan sama ne, wanda yake xauke da duffai da tsawa da walqiya, har ta kai suna sanya ‘yan yatsunsu cikin kunnuwansu don tsananin tsawarwaki saboda tsoron mutuwa. Allah Kuma Yana kewaye da kafirai (da iliminsa)



Sura: Suratul Baqara

Aya : 20

يَكَادُ ٱلۡبَرۡقُ يَخۡطَفُ أَبۡصَٰرَهُمۡۖ كُلَّمَآ أَضَآءَ لَهُم مَّشَوۡاْ فِيهِ وَإِذَآ أَظۡلَمَ عَلَيۡهِمۡ قَامُواْۚ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ لَذَهَبَ بِسَمۡعِهِمۡ وَأَبۡصَٰرِهِمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Walqiyar ta kusa ta fauce idanuwansu. Duk sa›adda ta haska musu sai su ci gaba da tafiya cikin (haskenta); idan kuma ta rufe su da duhu sai su tsaya cak. Da kuwa Allah Ya ga dama da sai Ya tafiyar da jinsu da ganinsu. Lalle Allah Mai iko ne a kan komai



Sura: Suratul Baqara

Aya : 21

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱعۡبُدُواْ رَبَّكُمُ ٱلَّذِي خَلَقَكُمۡ وَٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَتَّقُونَ

Ya ku mutane, ku bauta wa Ubangijinku Wanda Ya halicce ku, da waxanda suka gabace ku, don ku samu taqawa



Sura: Suratul Baqara

Aya : 22

ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلۡأَرۡضَ فِرَٰشٗا وَٱلسَّمَآءَ بِنَآءٗ وَأَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَخۡرَجَ بِهِۦ مِنَ ٱلثَّمَرَٰتِ رِزۡقٗا لَّكُمۡۖ فَلَا تَجۡعَلُواْ لِلَّهِ أَندَادٗا وَأَنتُمۡ تَعۡلَمُونَ

Shi ne Wanda Ya sanya muku qasa ta zama shimfixa kuma Ya sanya muku sama ta zama gini kuma Ya saukar da ruwa daga sama Ya fitar muku da arziqi na ‘ya’yan itatuwa, don haka kada ku sanya wa Allah kishiyoyi alhalin kuna sane



Sura: Suratul Baqara

Aya : 23

وَإِن كُنتُمۡ فِي رَيۡبٖ مِّمَّا نَزَّلۡنَا عَلَىٰ عَبۡدِنَا فَأۡتُواْ بِسُورَةٖ مِّن مِّثۡلِهِۦ وَٱدۡعُواْ شُهَدَآءَكُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

Kuma idan kun kasance cikin kokwanto game da abin da Muka saukar wa bawanmu, to ku zo da kwatankwacin sura xaya kamarsa, kuma ku kirawo masu taimakonku ba Allah ba in kun kasance masu gaskiya