۞أَفَمَن يَعۡلَمُ أَنَّمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَ ٱلۡحَقُّ كَمَنۡ هُوَ أَعۡمَىٰٓۚ إِنَّمَا يَتَذَكَّرُ أُوْلُواْ ٱلۡأَلۡبَٰبِ
Yanzu wanda ya san cewa abin da aka saukar maka daga Ubangijinka gaskiya ne (zai zama) kamar wanda yake shi makaho ne? Lalle ma’abota hankali ne kaxai ke wa’azantuwa
ٱلَّذِينَ يُوفُونَ بِعَهۡدِ ٱللَّهِ وَلَا يَنقُضُونَ ٱلۡمِيثَٰقَ
(Su ne) waxanda suke cika alqawarin Allah kuma ba sa warware alqawarin
وَٱلَّذِينَ يَصِلُونَ مَآ أَمَرَ ٱللَّهُ بِهِۦٓ أَن يُوصَلَ وَيَخۡشَوۡنَ رَبَّهُمۡ وَيَخَافُونَ سُوٓءَ ٱلۡحِسَابِ
Waxanda kuma suke sadar da abin da Allah Ya yi umarni a sadar da shi (na zumunci), suke kuma tsoron Ubangijinsu, kuma suke tsoron mummunan hisabi
وَٱلَّذِينَ صَبَرُواْ ٱبۡتِغَآءَ وَجۡهِ رَبِّهِمۡ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَأَنفَقُواْ مِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ سِرّٗا وَعَلَانِيَةٗ وَيَدۡرَءُونَ بِٱلۡحَسَنَةِ ٱلسَّيِّئَةَ أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ عُقۡبَى ٱلدَّارِ
Waxanda kuma suka yi haquri don neman yardar Ubangijnsu, suka kuma tsai da salla, kuma suka ciyar daga abin da Muka arzuta su da shi a voye da sarari, suke kuma ingije mummunan aiki da kyakkyawa, waxannan suna da (kyakkyawar) makoma ta gidan (Aljanna)
جَنَّـٰتُ عَدۡنٖ يَدۡخُلُونَهَا وَمَن صَلَحَ مِنۡ ءَابَآئِهِمۡ وَأَزۡوَٰجِهِمۡ وَذُرِّيَّـٰتِهِمۡۖ وَٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ يَدۡخُلُونَ عَلَيۡهِم مِّن كُلِّ بَابٖ
Gidajen Aljanna na dawwama, za su shiga su da waxanda suka kyautata (aiki) daga iyayensu da matansu da kuma zuriyarsu; mala’iku kuma za su riqa shigowa wurinsu ta kowace qofa
سَلَٰمٌ عَلَيۡكُم بِمَا صَبَرۡتُمۡۚ فَنِعۡمَ عُقۡبَى ٱلدَّارِ
(Suna ce musu): “Aminci ya tabbata a gare ku saboda haqurin da kuka yi. To madalla da gida na qarshe (watau Aljanna)”
وَٱلَّذِينَ يَنقُضُونَ عَهۡدَ ٱللَّهِ مِنۢ بَعۡدِ مِيثَٰقِهِۦ وَيَقۡطَعُونَ مَآ أَمَرَ ٱللَّهُ بِهِۦٓ أَن يُوصَلَ وَيُفۡسِدُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمُ ٱللَّعۡنَةُ وَلَهُمۡ سُوٓءُ ٱلدَّارِ
Waxanda kuma suke warware alqawarin Allah bayan sun qulla shi, suke kuma yanke abin da Allah Ya yi umarni a sadar da shi, kuma suke varna a bayan qasa, waxannan la’ana ta tabbata a gare su kuma suna da (sakamakon) mummunan gida (shi ne Jahannama)
ٱللَّهُ يَبۡسُطُ ٱلرِّزۡقَ لِمَن يَشَآءُ وَيَقۡدِرُۚ وَفَرِحُواْ بِٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَمَا ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَا فِي ٱلۡأٓخِرَةِ إِلَّا مَتَٰعٞ
Allah ne Yake shimfixa arziki ga wanda Ya ga dama, Yake kuma quntatawa (ga wanda Ya ga dama. (Kafirai) kuma sun yi farin ciki da rayuwar duniya, rayuwar duniya kuwa ba komai ba ce illa xan jin daxi kaxan dangane da na lahira
وَيَقُولُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَوۡلَآ أُنزِلَ عَلَيۡهِ ءَايَةٞ مِّن رَّبِّهِۦۚ قُلۡ إِنَّ ٱللَّهَ يُضِلُّ مَن يَشَآءُ وَيَهۡدِيٓ إِلَيۡهِ مَنۡ أَنَابَ
Waxanda suka kafirta kuma suna cewa: “Me ya hana a saukar masa da aya daga Ubangijinsa?” Ka ce: “Lalle Allah Yana vatar da wanda Ya ga dama, Yana kuma shiryar da wanda ya koma gare Shi
ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَتَطۡمَئِنُّ قُلُوبُهُم بِذِكۡرِ ٱللَّهِۗ أَلَا بِذِكۡرِ ٱللَّهِ تَطۡمَئِنُّ ٱلۡقُلُوبُ
“(Su ne) waxanda suka yi imani, zukatansu kuma suna nutsuwa da ambaton Allah. Ku saurara, da ambaton Allah ne zukata suke nutsuwa
ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ طُوبَىٰ لَهُمۡ وَحُسۡنُ مَـَٔابٖ
“Waxanda suka yi imani suka kuma yi aiki nagari, to farin ciki ya tabbata a gare su da kuma kyakkyawar makoma.”
كَذَٰلِكَ أَرۡسَلۡنَٰكَ فِيٓ أُمَّةٖ قَدۡ خَلَتۡ مِن قَبۡلِهَآ أُمَمٞ لِّتَتۡلُوَاْ عَلَيۡهِمُ ٱلَّذِيٓ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ وَهُمۡ يَكۡفُرُونَ بِٱلرَّحۡمَٰنِۚ قُلۡ هُوَ رَبِّي لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ عَلَيۡهِ تَوَكَّلۡتُ وَإِلَيۡهِ مَتَابِ
Kamar haka Muka aiko ka cikin al’umma wadda tuni wasu al’ummun sun wuce kafinta, don ka karanta musu abin da Muka yi maka wahayinsa, alhali kuwa su suna kafirce wa Arrahamanu[1]. Ka ce: “Shi ne Ubangijina, babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi, gare Shi kawai na dogara, kuma gare Shi kawai tubata take.”
1- Kafiran Quraishawa suna qyamar su siffanta Allah da suna Arrahman, watau Mai rahma, kamar yadda ya zo a cikin Suratul Furqan aya ta 60.
وَلَوۡ أَنَّ قُرۡءَانٗا سُيِّرَتۡ بِهِ ٱلۡجِبَالُ أَوۡ قُطِّعَتۡ بِهِ ٱلۡأَرۡضُ أَوۡ كُلِّمَ بِهِ ٱلۡمَوۡتَىٰۗ بَل لِّلَّهِ ٱلۡأَمۡرُ جَمِيعًاۗ أَفَلَمۡ يَاْيۡـَٔسِ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَن لَّوۡ يَشَآءُ ٱللَّهُ لَهَدَى ٱلنَّاسَ جَمِيعٗاۗ وَلَا يَزَالُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ تُصِيبُهُم بِمَا صَنَعُواْ قَارِعَةٌ أَوۡ تَحُلُّ قَرِيبٗا مِّن دَارِهِمۡ حَتَّىٰ يَأۡتِيَ وَعۡدُ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُخۡلِفُ ٱلۡمِيعَادَ
Da a ce akwai wani abin karantawa da za a gusar da duwatsu da shi, ko kuma a keta qasa da shi, ko kuma a yi magana da matattu da shi, (to da wannan Alqur’anin ne). Bari dai, dukkanin al’amari gaba xaya na Allah ne. Shin waxanda suka yi imani ba su san da cewa da Allah Ya ga dama da Ya shiryi mutane gaba xaya ba? Kafirai kuwa azaba ba za ta daina samun su ba saboda abin da suka aikata, ko kuwa ta faxo kusa da gidajensu har sai alqawarin Allah ya zo. Lalle Allah ba Ya sava alqawari
وَلَقَدِ ٱسۡتُهۡزِئَ بِرُسُلٖ مِّن قَبۡلِكَ فَأَمۡلَيۡتُ لِلَّذِينَ كَفَرُواْ ثُمَّ أَخَذۡتُهُمۡۖ فَكَيۡفَ كَانَ عِقَابِ
Haqiqa an yi wa manzannin da suka gabace ka izgili, sai Na yi wa waxanda suka kafirta talala, sannan Na damqe su. To yaya uqubata ta kasance (a gare su)?
أَفَمَنۡ هُوَ قَآئِمٌ عَلَىٰ كُلِّ نَفۡسِۭ بِمَا كَسَبَتۡۗ وَجَعَلُواْ لِلَّهِ شُرَكَآءَ قُلۡ سَمُّوهُمۡۚ أَمۡ تُنَبِّـُٔونَهُۥ بِمَا لَا يَعۡلَمُ فِي ٱلۡأَرۡضِ أَم بِظَٰهِرٖ مِّنَ ٱلۡقَوۡلِۗ بَلۡ زُيِّنَ لِلَّذِينَ كَفَرُواْ مَكۡرُهُمۡ وَصُدُّواْ عَنِ ٱلسَّبِيلِۗ وَمَن يُضۡلِلِ ٱللَّهُ فَمَا لَهُۥ مِنۡ هَادٖ
Yanzu wanda Yake tsaye a kan kula da kowane rai game da abin da ya aikata, (zai zama daidai da wanda ba haka ba?) Sun kuma sanya wa Allah abokan tarayya. Ka ce: (da su) “Ku faxa min sunayensu. Ko kuwa kuna ba Shi labarin abin da bai sani ba ne a bayan qasa, ko kuma dai kun riqe wata vatacciyar magana ce?” Bari dai; an dai qawata wa kafirai makircinsu ne kawai, aka kuma toshe musu hanyar (Allah). Wanda kuwa Allah Ya vatar to ba shi da wani mai shiryarwa
لَّهُمۡ عَذَابٞ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ وَلَعَذَابُ ٱلۡأٓخِرَةِ أَشَقُّۖ وَمَا لَهُم مِّنَ ٱللَّهِ مِن وَاقٖ
Suna da wata azaba a rayuwar duniya; kuma lalle azabar lahira ita ta fi tsanani; ba su kuwa da wani mai kare su daga (azabar) Allah
۞مَّثَلُ ٱلۡجَنَّةِ ٱلَّتِي وُعِدَ ٱلۡمُتَّقُونَۖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۖ أُكُلُهَا دَآئِمٞ وَظِلُّهَاۚ تِلۡكَ عُقۡبَى ٱلَّذِينَ ٱتَّقَواْۚ وَّعُقۡبَى ٱلۡكَٰفِرِينَ ٱلنَّارُ
Misalin Aljannar nan da aka yi wa masu taqawa alqawari da ita; qoramu ne suke gudana ta qarqashinta; abincinta kuma mai dawwama ne da kuma inuwarta. Wannan shi ne makomar waxanda suka kiyaye dokokin Allah; makomar kafirai kuma ita ce wuta
وَٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ يَفۡرَحُونَ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكَۖ وَمِنَ ٱلۡأَحۡزَابِ مَن يُنكِرُ بَعۡضَهُۥۚ قُلۡ إِنَّمَآ أُمِرۡتُ أَنۡ أَعۡبُدَ ٱللَّهَ وَلَآ أُشۡرِكَ بِهِۦٓۚ إِلَيۡهِ أَدۡعُواْ وَإِلَيۡهِ مَـَٔابِ
Waxanda kuwa Muka bai wa littafi (muminansu) suna farin ciki da abin da aka saukar maka; akwai kuma wasu daga qungiyoyi waxanda suke musun wani sashi nasa. Ka ce: “Ni dai an umarce ni ne kawai da in bauta wa Allah, kada kuma in tara wani abu da Shi. Kuma zuwa gare Shi kawai nake kira, wurinsa ne kawai kuma makomata.”
وَكَذَٰلِكَ أَنزَلۡنَٰهُ حُكۡمًا عَرَبِيّٗاۚ وَلَئِنِ ٱتَّبَعۡتَ أَهۡوَآءَهُم بَعۡدَ مَا جَآءَكَ مِنَ ٱلۡعِلۡمِ مَا لَكَ مِنَ ٱللَّهِ مِن وَلِيّٖ وَلَا وَاقٖ
Kamar haka Muka saukar da shi (Alqur’ani), ya zama hukunci, da harshen Larabci. Lalle kuma idan ka bi son ransu bayan abin da ya zo maka na ilimi, to ba ka da wani majivinci ko mai kariya daga (azabar) Allah
وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا رُسُلٗا مِّن قَبۡلِكَ وَجَعَلۡنَا لَهُمۡ أَزۡوَٰجٗا وَذُرِّيَّةٗۚ وَمَا كَانَ لِرَسُولٍ أَن يَأۡتِيَ بِـَٔايَةٍ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۗ لِكُلِّ أَجَلٖ كِتَابٞ
Haqiqa kuma Mun aiko manzanni a gabaninka, Muka kuma ba su matan aure da zurriya. Bai kuma kamata ba ga wani annabi ya zo da wata aya (da za a neme shi da ya kawo ta) sai da izinin Allah. Kuma kowane lokaci yana nan a rubuce
يَمۡحُواْ ٱللَّهُ مَا يَشَآءُ وَيُثۡبِتُۖ وَعِندَهُۥٓ أُمُّ ٱلۡكِتَٰبِ
Allah Yana shafe abin da ya ga dama, Yana kuma tabbatar (da abin da ya ga dama); kuma a wurinsa asalin littafi yake[1]
1- Watau Lauhul Mahfuzu, littafin da Allah ya rubuta komai a cikinsa.
وَإِن مَّا نُرِيَنَّكَ بَعۡضَ ٱلَّذِي نَعِدُهُمۡ أَوۡ نَتَوَفَّيَنَّكَ فَإِنَّمَا عَلَيۡكَ ٱلۡبَلَٰغُ وَعَلَيۡنَا ٱلۡحِسَابُ
Ko dai Mu nuna maka irin sashin abin da Muke yi musu gargaxi da aukuwarsa, ko kuma Mu karvi ranka (kafin lokacin), abin da yake kanka kawai shi ne isar da aike, Mu kuma hisabi yana a kanmu
أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّا نَأۡتِي ٱلۡأَرۡضَ نَنقُصُهَا مِنۡ أَطۡرَافِهَاۚ وَٱللَّهُ يَحۡكُمُ لَا مُعَقِّبَ لِحُكۡمِهِۦۚ وَهُوَ سَرِيعُ ٱلۡحِسَابِ
Yanzu ba sa ganin cewa Muna zaike wa qasa Muna ta cinye iyakokinta[1]? Allah ne Mai yin hukunci, babu kuma mai yin gyara ga hukuncinsa. Shi ne kuma Mai saurin yin hisabi
1- Watau Musulmi suna ta samun nasara a kansu, suna ta cinye garuruwansu da yaqi.
وَقَدۡ مَكَرَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ فَلِلَّهِ ٱلۡمَكۡرُ جَمِيعٗاۖ يَعۡلَمُ مَا تَكۡسِبُ كُلُّ نَفۡسٖۗ وَسَيَعۡلَمُ ٱلۡكُفَّـٰرُ لِمَنۡ عُقۡبَى ٱلدَّارِ
Haqiqa kuma waxanda suke gabaninsu sun qulla makirci, (sakamakon) qulle-qulle dukkaninsa ga Allah yake; Yana sane da abin da kowane rai yake aikatawa. Ba da daxewa ba kuma kafirai za su san wane ne mai kyakkyawan gidan (qarshe)
وَيَقُولُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَسۡتَ مُرۡسَلٗاۚ قُلۡ كَفَىٰ بِٱللَّهِ شَهِيدَۢا بَيۡنِي وَبَيۡنَكُمۡ وَمَنۡ عِندَهُۥ عِلۡمُ ٱلۡكِتَٰبِ
Kafirai kuma suna cewa: “Kai ba manzo ba ne.” Ka ce (da su): “Allah Ya isa shaida tsakanina da ku, da kuma wanda yake da ilimin Littafi[1].”
1- Watau malaman Ahlulkitabi waxanda suka musulunta suka shaida da manzancinsa, suka yi imani da shi.
الٓرۚ كِتَٰبٌ أَنزَلۡنَٰهُ إِلَيۡكَ لِتُخۡرِجَ ٱلنَّاسَ مِنَ ٱلظُّلُمَٰتِ إِلَى ٱلنُّورِ بِإِذۡنِ رَبِّهِمۡ إِلَىٰ صِرَٰطِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَمِيدِ
ALIF LAM RA[1]. Littafi ne da Muka saukar maka da shi, don ka fitar da mutane daga duffai zuwa ga haske, da izinin Ubangijinsu zuwa ga tafarkin (Allah) Mabuwayi, Abin godiya
1- Duba Suratul Baqara aya ta 1, hashiya ta 8.
ٱللَّهِ ٱلَّذِي لَهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ وَوَيۡلٞ لِّلۡكَٰفِرِينَ مِنۡ عَذَابٖ شَدِيدٍ
(Watau) Allah, Wanda abin da yake cikin sammai da na cikin qasa duka nasa ne. Bone na wata azaba mai tsanani kuma ya tabbatta ga kafirai
ٱلَّذِينَ يَسۡتَحِبُّونَ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا عَلَى ٱلۡأٓخِرَةِ وَيَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ وَيَبۡغُونَهَا عِوَجًاۚ أُوْلَـٰٓئِكَ فِي ضَلَٰلِۭ بَعِيدٖ
Waxanda suke fifita son rayuwar duniya a kan lahira, suke kuma hanawa (a bi) hanyar Allah, kuma suke neman ta zama karkatacciya. To waxannan suna cikin vata mai nisa
وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن رَّسُولٍ إِلَّا بِلِسَانِ قَوۡمِهِۦ لِيُبَيِّنَ لَهُمۡۖ فَيُضِلُّ ٱللَّهُ مَن يَشَآءُ وَيَهۡدِي مَن يَشَآءُۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ
Ba Mu tava aiko wani manzo ba kuwa sai da harshen mutanensa don ya yi musu bayani; sannan Allah Yana vatar da wanda ya ga dama, ya kuma shiryar da wanda ya ga dama. Shi ne kuwa Mabuwayi, Mai hikima
وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا مُوسَىٰ بِـَٔايَٰتِنَآ أَنۡ أَخۡرِجۡ قَوۡمَكَ مِنَ ٱلظُّلُمَٰتِ إِلَى ٱلنُّورِ وَذَكِّرۡهُم بِأَيَّىٰمِ ٱللَّهِۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّكُلِّ صَبَّارٖ شَكُورٖ
Haqiqa kuma Mun aiko Musa da ayoyinmu cewa: “Ka fitar da mutananka daga duffai zuwa ga haske, kuma ka tunatar da su ni’imomin Allah (da ya yi musu).” Lalle game da wannan da akwai ayoyi ga duk wani mai yawan haquri, mai yawan godiya