Sura: Suratul Isra’i

Aya : 99

۞أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّ ٱللَّهَ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ قَادِرٌ عَلَىٰٓ أَن يَخۡلُقَ مِثۡلَهُمۡ وَجَعَلَ لَهُمۡ أَجَلٗا لَّا رَيۡبَ فِيهِ فَأَبَى ٱلظَّـٰلِمُونَ إِلَّا كُفُورٗا

Yanzu ba sa gani cewa Allah wanda Ya halicci sammai da qasa Mai iko ne a kan Ya halicci irinsu? Ya kuma sanya musu wani lokaci wanda ba kokwanto a cikinsa, sai azzalumai suka qi (yin imani) sai kafircewa



Sura: Suratul Isra’i

Aya : 100

قُل لَّوۡ أَنتُمۡ تَمۡلِكُونَ خَزَآئِنَ رَحۡمَةِ رَبِّيٓ إِذٗا لَّأَمۡسَكۡتُمۡ خَشۡيَةَ ٱلۡإِنفَاقِۚ وَكَانَ ٱلۡإِنسَٰنُ قَتُورٗا

Ka ce da su: “Idan da ku ne kuka mallaki taskokin rahamar Ubangijina to lalle da kun riqe su qam-qam don tsoron ciyarwa. Mutum kuwa ya tabbata mai tsananin rowa ne



Sura: Suratul Isra’i

Aya : 101

وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَىٰ تِسۡعَ ءَايَٰتِۭ بَيِّنَٰتٖۖ فَسۡـَٔلۡ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ إِذۡ جَآءَهُمۡ فَقَالَ لَهُۥ فِرۡعَوۡنُ إِنِّي لَأَظُنُّكَ يَٰمُوسَىٰ مَسۡحُورٗا

Kuma haqiqa Mun bai wa Musa ayoyi tara bayyanannu; to ka tambayi Banu Isra’ila lokacin da ya zo musu, sai Fir’auna ya ce da shi: “Lalle ni fa ina tsammanin kai Musa sihirtacce ne!”



Sura: Suratul Isra’i

Aya : 102

قَالَ لَقَدۡ عَلِمۡتَ مَآ أَنزَلَ هَـٰٓؤُلَآءِ إِلَّا رَبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ بَصَآئِرَ وَإِنِّي لَأَظُنُّكَ يَٰفِرۡعَوۡنُ مَثۡبُورٗا

(Musa) ya ce: “Haqiqa ka sani ba wanda ya saukar da waxannan (ayoyin) sai Ubangijin sammai da qasa don su zama hujjoji, kuma lalle ina tsammanin kai Fir’auna halakakke ne.”



Sura: Suratul Isra’i

Aya : 103

فَأَرَادَ أَن يَسۡتَفِزَّهُم مِّنَ ٱلۡأَرۡضِ فَأَغۡرَقۡنَٰهُ وَمَن مَّعَهُۥ جَمِيعٗا

Sai ya yi nufin ya girgiza su a qasar (ta Masar don ya fitar da su daga ciki), to sai Muka nutsar da shi da duk wanda yake tare da shi gaba xaya



Sura: Suratul Isra’i

Aya : 104

وَقُلۡنَا مِنۢ بَعۡدِهِۦ لِبَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ ٱسۡكُنُواْ ٱلۡأَرۡضَ فَإِذَا جَآءَ وَعۡدُ ٱلۡأٓخِرَةِ جِئۡنَا بِكُمۡ لَفِيفٗا

Muka kuma ce da Banu Isra’ila: “Ku zauna a qasar (ta Falasxinu), to idan lokacin alqiyama ya zo za Mu tattaro ku gaba xaya



Sura: Suratul Isra’i

Aya : 105

وَبِٱلۡحَقِّ أَنزَلۡنَٰهُ وَبِٱلۡحَقِّ نَزَلَۗ وَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ إِلَّا مُبَشِّرٗا وَنَذِيرٗا

Kuma da gaskiya Muka saukar da shi (Alqur’ani), kuma da gaskiya ya sauko. Ba Mu kuma aiko ka ba sai mai yin albishir, mai kuma gargaxi



Sura: Suratul Isra’i

Aya : 106

وَقُرۡءَانٗا فَرَقۡنَٰهُ لِتَقۡرَأَهُۥ عَلَى ٱلنَّاسِ عَلَىٰ مُكۡثٖ وَنَزَّلۡنَٰهُ تَنزِيلٗا

Kuma Mun saukar da Qur’ani, Mun bayyana shi don ka karanta wa mutane shi a sannu a hankali, Mun kuma saukar da shi daki-daki



Sura: Suratul Isra’i

Aya : 107

قُلۡ ءَامِنُواْ بِهِۦٓ أَوۡ لَا تُؤۡمِنُوٓاْۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ مِن قَبۡلِهِۦٓ إِذَا يُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ يَخِرُّونَۤ لِلۡأَذۡقَانِۤ سُجَّدٗاۤ

Ka ce da su: “Ko ku yi imani da shi ko kada ku yi imani da shi (duk xaya ne).” Lalle waxanda aka bai wa ilimi gabaninsa (Yahudu da Nasara)[1] idan ana karanta musu shi suna faxuwa da fuskokinsu suna masu sujjada


1- Watau mutanen kirki daga cikinsu.


Sura: Suratul Isra’i

Aya : 108

وَيَقُولُونَ سُبۡحَٰنَ رَبِّنَآ إِن كَانَ وَعۡدُ رَبِّنَا لَمَفۡعُولٗا

Suna kuma cewa: “Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu, lalle alqawarin Ubangijinmu tabbas ya zamanto abin aikatawa ne.”



Sura: Suratul Isra’i

Aya : 109

وَيَخِرُّونَ لِلۡأَذۡقَانِ يَبۡكُونَ وَيَزِيدُهُمۡ خُشُوعٗا۩

Suna kuma faxuwa da fuskokinsu suna kuka, Yana kuma qara musu qasqantar da kai



Sura: Suratul Isra’i

Aya : 110

قُلِ ٱدۡعُواْ ٱللَّهَ أَوِ ٱدۡعُواْ ٱلرَّحۡمَٰنَۖ أَيّٗا مَّا تَدۡعُواْ فَلَهُ ٱلۡأَسۡمَآءُ ٱلۡحُسۡنَىٰۚ وَلَا تَجۡهَرۡ بِصَلَاتِكَ وَلَا تُخَافِتۡ بِهَا وَٱبۡتَغِ بَيۡنَ ذَٰلِكَ سَبِيلٗا

Ka ce: “Ku kira (sunan) Allah ko ku kira (sunan) Arrahaman; kowanne kuka kira to shi Yana da sunaye ne mafiya kyau.” Kada kuma ka xaga muryarka da (karatun) sallarka, kada kuma ka yi shi a voye, ka nemi tsaka-tsakin wannan



Sura: Suratul Isra’i

Aya : 111

وَقُلِ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِي لَمۡ يَتَّخِذۡ وَلَدٗا وَلَمۡ يَكُن لَّهُۥ شَرِيكٞ فِي ٱلۡمُلۡكِ وَلَمۡ يَكُن لَّهُۥ وَلِيّٞ مِّنَ ٱلذُّلِّۖ وَكَبِّرۡهُ تَكۡبِيرَۢا

Kuma ka ce, “Yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda bai riqi xa ba, kuma ba Shi da wani abokin tarayya a cikin mulki, kuma ba Shi da wani mataimaki don kare masa qasqanci.” Kuma ka girmama shi girmamawa ta sosai



Sura: Suratul Kahf 

Aya : 1

ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ عَلَىٰ عَبۡدِهِ ٱلۡكِتَٰبَ وَلَمۡ يَجۡعَل لَّهُۥ عِوَجَاۜ

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah wanda Ya saukar wa da Bawansa Littafi, bai kuma sanya masa wata karkata ba



Sura: Suratul Kahf 

Aya : 2

قَيِّمٗا لِّيُنذِرَ بَأۡسٗا شَدِيدٗا مِّن لَّدُنۡهُ وَيُبَشِّرَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ٱلَّذِينَ يَعۡمَلُونَ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ أَنَّ لَهُمۡ أَجۡرًا حَسَنٗا

Daidaitacce ne, don ya yi gargaxi game da azaba mai tsanani daga gare Shi (wato Allah), ya kuma yi wa muminai waxanda suke aiki nagari albishir cewa suna da lada kyakkyawa



Sura: Suratul Kahf 

Aya : 3

مَّـٰكِثِينَ فِيهِ أَبَدٗا

Madawwama a cikinsa har abada



Sura: Suratul Kahf 

Aya : 4

وَيُنذِرَ ٱلَّذِينَ قَالُواْ ٱتَّخَذَ ٱللَّهُ وَلَدٗا

Ya kuma gargaxi waxanda suka ce Allah Yana da xa



Sura: Suratul Kahf 

Aya : 5

مَّا لَهُم بِهِۦ مِنۡ عِلۡمٖ وَلَا لِأٓبَآئِهِمۡۚ كَبُرَتۡ كَلِمَةٗ تَخۡرُجُ مِنۡ أَفۡوَٰهِهِمۡۚ إِن يَقُولُونَ إِلَّا كَذِبٗا

Ba su da wani ilimi game da shi (wannan zance) kuma iyayensu ma ba su da (ilimi game da shi). Kalmar da take fitowa daga bakunansu ta yi girma. Ba abin da suke faxa sai qarya



Sura: Suratul Kahf 

Aya : 6

فَلَعَلَّكَ بَٰخِعٞ نَّفۡسَكَ عَلَىٰٓ ءَاثَٰرِهِمۡ إِن لَّمۡ يُؤۡمِنُواْ بِهَٰذَا ٱلۡحَدِيثِ أَسَفًا

To ko mai yiwuwa ne za ka kashe kanka da baqin ciki, in ba su yi imani da wannan zancen ba (watau Alqur’ani)



Sura: Suratul Kahf 

Aya : 7

إِنَّا جَعَلۡنَا مَا عَلَى ٱلۡأَرۡضِ زِينَةٗ لَّهَا لِنَبۡلُوَهُمۡ أَيُّهُمۡ أَحۡسَنُ عَمَلٗا

Lalle Mu Mun sanya abin da yake bayan qasa ya zama ado a gare ta, don (kuma) Mu jarraba su, wane ne daga cikinsu ya fi kyakkyawan aiki?



Sura: Suratul Kahf 

Aya : 8

وَإِنَّا لَجَٰعِلُونَ مَا عَلَيۡهَا صَعِيدٗا جُرُزًا

Lalle kuma Mu za Mu mai da abin da yake kanta (ya zama) turvaya qeqasasshiya



Sura: Suratul Kahf 

Aya : 9

أَمۡ حَسِبۡتَ أَنَّ أَصۡحَٰبَ ٱلۡكَهۡفِ وَٱلرَّقِيمِ كَانُواْ مِنۡ ءَايَٰتِنَا عَجَبًا

Shin ka yi tsammanin cewa lalle Mutanen Kogo da Raqimu[1] sun kasance daga ayoyinmu masu ban mamaki?


1- An yi savani wajen fassara ma’anar arraqimu. Wasu sun ce sunan dutsen da suka kasance a cikinsa ne; wasu kuma sun ce sunan allon da aka rubuta sunayensu a ciki; wasu kuma sun ce mutanen nan uku ne da suka shiga kogo dutse ya rufe da su.


Sura: Suratul Kahf 

Aya : 10

إِذۡ أَوَى ٱلۡفِتۡيَةُ إِلَى ٱلۡكَهۡفِ فَقَالُواْ رَبَّنَآ ءَاتِنَا مِن لَّدُنكَ رَحۡمَةٗ وَهَيِّئۡ لَنَا مِنۡ أَمۡرِنَا رَشَدٗا

Lokacin da samarin nan suka fake a Kogon, sai suka ce: “Ya Ubangijinmu, Ka ba mu rahama daga gare Ka, Ka kuma tanadar mana shiriya cikin lamarinmu



Sura: Suratul Kahf 

Aya : 11

فَضَرَبۡنَا عَلَىٰٓ ءَاذَانِهِمۡ فِي ٱلۡكَهۡفِ سِنِينَ عَدَدٗا

Sai Muka sanya (shamaki) a kan kunnuwansu (suka yi barci) shekaru masu yawa a cikin Kogon



Sura: Suratul Kahf 

Aya : 12

ثُمَّ بَعَثۡنَٰهُمۡ لِنَعۡلَمَ أَيُّ ٱلۡحِزۡبَيۡنِ أَحۡصَىٰ لِمَا لَبِثُوٓاْ أَمَدٗا

Sannan Muka tashe su don Mu san wane ne daga qungiyoyin nan biyu (masu savani game da lamarin samarin) ya fi kiyayewa da tsawon zamaninsu?



Sura: Suratul Kahf 

Aya : 13

نَّحۡنُ نَقُصُّ عَلَيۡكَ نَبَأَهُم بِٱلۡحَقِّۚ إِنَّهُمۡ فِتۡيَةٌ ءَامَنُواْ بِرَبِّهِمۡ وَزِدۡنَٰهُمۡ هُدٗى

Mu ne za Mu ba ka labarinsu da gaskiya. Lalle su samari ne da suka yi imani da Ubangijinsu, Muka kuwa qara musu shiriya



Sura: Suratul Kahf 

Aya : 14

وَرَبَطۡنَا عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ إِذۡ قَامُواْ فَقَالُواْ رَبُّنَا رَبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ لَن نَّدۡعُوَاْ مِن دُونِهِۦٓ إِلَٰهٗاۖ لَّقَدۡ قُلۡنَآ إِذٗا شَطَطًا

Muka kuma xaure zukatansu lokacin da suka tsaya suka ce: “Ubangijinmu Shi ne Ubangijin sammai da qasa; ba za mu bauta wa wani abin bauta ba in ban da Shi; idan muka yi haka kuwa to haqiqa mun faxi qarya



Sura: Suratul Kahf 

Aya : 15

هَـٰٓؤُلَآءِ قَوۡمُنَا ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِهِۦٓ ءَالِهَةٗۖ لَّوۡلَا يَأۡتُونَ عَلَيۡهِم بِسُلۡطَٰنِۭ بَيِّنٖۖ فَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبٗا

“Waxannan mutanenmu ne da suka riqi wasu alloli ba Shi ba; me ya hana ba su zo musu da wata hujja mabayyaniya (kan haka) ba? To ba wanda ya fi zalunci fiye da wanda ya yi wa Allah qarya



Sura: Suratul Kahf 

Aya : 16

وَإِذِ ٱعۡتَزَلۡتُمُوهُمۡ وَمَا يَعۡبُدُونَ إِلَّا ٱللَّهَ فَأۡوُۥٓاْ إِلَى ٱلۡكَهۡفِ يَنشُرۡ لَكُمۡ رَبُّكُم مِّن رَّحۡمَتِهِۦ وَيُهَيِّئۡ لَكُم مِّنۡ أَمۡرِكُم مِّرۡفَقٗا

“Tun da kun qaurace musu tare da abin da suke bauta wa sai Allah, to sai ku tare a kogon, Ubangijinku zai yalwata muku rahamarsa ya kuma shirya muku hanyar rayuwa mai sauqi ga al’amuranku.”



Sura: Suratul Kahf 

Aya : 17

۞وَتَرَى ٱلشَّمۡسَ إِذَا طَلَعَت تَّزَٰوَرُ عَن كَهۡفِهِمۡ ذَاتَ ٱلۡيَمِينِ وَإِذَا غَرَبَت تَّقۡرِضُهُمۡ ذَاتَ ٱلشِّمَالِ وَهُمۡ فِي فَجۡوَةٖ مِّنۡهُۚ ذَٰلِكَ مِنۡ ءَايَٰتِ ٱللَّهِۗ مَن يَهۡدِ ٱللَّهُ فَهُوَ ٱلۡمُهۡتَدِۖ وَمَن يُضۡلِلۡ فَلَن تَجِدَ لَهُۥ وَلِيّٗا مُّرۡشِدٗا

(Sai) kuma ka ga rana idan za ta vullo tana kauce wa kogonsu ta vangaren dama, idan kuma za ta faxi sai ta riqa kauce musu ta vangaren hagu, su kuwa suna tsakiyarsa. Wannan yana daga ayoyin Allah. Wanda Allah Ya shiryar to shi ne shiryayye, wanda kuwa Ya vatar to ba za ka sami wani majivinci da zai shirye shi ba