۞قَالَ أَلَمۡ أَقُل لَّكَ إِنَّكَ لَن تَسۡتَطِيعَ مَعِيَ صَبۡرٗا
Ya ce: “Shin ban faxa maka cewa lalle kai ba za ka iya haquri da ni ba?”
قَالَ إِن سَأَلۡتُكَ عَن شَيۡءِۭ بَعۡدَهَا فَلَا تُصَٰحِبۡنِيۖ قَدۡ بَلَغۡتَ مِن لَّدُنِّي عُذۡرٗا
(Musa) ya ce: “Idan na sake tambayar ka wani abu bayansa, to kada ka tafi tare da ni; haqiqa ka sami (cikakken) hanzari a kaina.”
فَٱنطَلَقَا حَتَّىٰٓ إِذَآ أَتَيَآ أَهۡلَ قَرۡيَةٍ ٱسۡتَطۡعَمَآ أَهۡلَهَا فَأَبَوۡاْ أَن يُضَيِّفُوهُمَا فَوَجَدَا فِيهَا جِدَارٗا يُرِيدُ أَن يَنقَضَّ فَأَقَامَهُۥۖ قَالَ لَوۡ شِئۡتَ لَتَّخَذۡتَ عَلَيۡهِ أَجۡرٗا
Sai suka ci gaba da tafiya har suka iso ga mutanen wata alqarya, sai suka nemi mutanen alqaryar su ciyar da su, to sai suka qi su karvi baquntarsu, sai suka samu wani garu a alqaryar yana haramar rugujewa sai (Khadiru) ya tashe shi, sai (Musa) ya ce: “Da ka ga dama ai da sai ka karvi lada a kansa.” (Watau aikin tayarwar)
قَالَ هَٰذَا فِرَاقُ بَيۡنِي وَبَيۡنِكَۚ سَأُنَبِّئُكَ بِتَأۡوِيلِ مَا لَمۡ تَسۡتَطِع عَّلَيۡهِ صَبۡرًا
Ya ce: “Wannan ita ce rabuwata da kai. Zan ba ka labarin abin da ka kasa haquri a kansa.”
أَمَّا ٱلسَّفِينَةُ فَكَانَتۡ لِمَسَٰكِينَ يَعۡمَلُونَ فِي ٱلۡبَحۡرِ فَأَرَدتُّ أَنۡ أَعِيبَهَا وَكَانَ وَرَآءَهُم مَّلِكٞ يَأۡخُذُ كُلَّ سَفِينَةٍ غَصۡبٗا
“To game da shi jirgin ruwan nan ya kasance na wasu miskinai ne da suke aiki a cikin kogi, to sai na yi nufin in lalata shi domin kuwa a gabansu akwai wani sarki da yake qwace kowane jirgin ruwa (lafiyayye)
وَأَمَّا ٱلۡغُلَٰمُ فَكَانَ أَبَوَاهُ مُؤۡمِنَيۡنِ فَخَشِينَآ أَن يُرۡهِقَهُمَا طُغۡيَٰنٗا وَكُفۡرٗا
“To amma kuma game da shi yaron nan, iyayensa sun kasance muminai ne, sai muka ji tsoron kada ya afkar da su cikin shisshigi da kafirci
فَأَرَدۡنَآ أَن يُبۡدِلَهُمَا رَبُّهُمَا خَيۡرٗا مِّنۡهُ زَكَوٰةٗ وَأَقۡرَبَ رُحۡمٗا
“Sai muka yi nufin Ubangijinsu Ya musanya musu (wani xa) wanda ya fi tsarkaka ya kuma fi shi tausayi
وَأَمَّا ٱلۡجِدَارُ فَكَانَ لِغُلَٰمَيۡنِ يَتِيمَيۡنِ فِي ٱلۡمَدِينَةِ وَكَانَ تَحۡتَهُۥ كَنزٞ لَّهُمَا وَكَانَ أَبُوهُمَا صَٰلِحٗا فَأَرَادَ رَبُّكَ أَن يَبۡلُغَآ أَشُدَّهُمَا وَيَسۡتَخۡرِجَا كَنزَهُمَا رَحۡمَةٗ مِّن رَّبِّكَۚ وَمَا فَعَلۡتُهُۥ عَنۡ أَمۡرِيۚ ذَٰلِكَ تَأۡوِيلُ مَا لَمۡ تَسۡطِع عَّلَيۡهِ صَبۡرٗا
“To game da shi garun nan kuwa ya kasance na wasu yara ne marayu a cikin wannan birnin, a qarqashinsa kuwa da akwai wata taska tasu, mahaifinsu kuma ya kasance mutumin kirki ne, to sai Ubangijinka Ya nufi su girma su cika hankalinsu su, kuma fito da taskarsu, don rahama daga Ubangijinka. Ban aikata haka ba ne da raxin kaina. Wannan shi ne fassarar abin da ka kasa haquri a kansa.”
وَيَسۡـَٔلُونَكَ عَن ذِي ٱلۡقَرۡنَيۡنِۖ قُلۡ سَأَتۡلُواْ عَلَيۡكُم مِّنۡهُ ذِكۡرًا
Suna kuma tambayar ka game da Zulqarnaini[1]; ka ce (da su): “Ba da daxewa ba zan ba ku labari a kansa.”
1- Daga nan har zuwa aya ta 98 Allah ya ba da labarin Zulqarnaini ne. Shi kuma wani sarki ne mumini da Allah ya ba shi qarfin Mulki har ya ci garuruwa masu yawa da yaqi.
إِنَّا مَكَّنَّا لَهُۥ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَءَاتَيۡنَٰهُ مِن كُلِّ شَيۡءٖ سَبَبٗا
Lalle Mu Muka kafa shi a bayan qasa, Muka kuma ba shi hanyar cimma duk wani muradinsa
فَأَتۡبَعَ سَبَبًا
Sai ya bi hanya
حَتَّىٰٓ إِذَا بَلَغَ مَغۡرِبَ ٱلشَّمۡسِ وَجَدَهَا تَغۡرُبُ فِي عَيۡنٍ حَمِئَةٖ وَوَجَدَ عِندَهَا قَوۡمٗاۖ قُلۡنَا يَٰذَا ٱلۡقَرۡنَيۡنِ إِمَّآ أَن تُعَذِّبَ وَإِمَّآ أَن تَتَّخِذَ فِيهِمۡ حُسۡنٗا
Har sai da ya isa mafaxar rana, sai ya same ta tana faxuwa ne cikin wani marmaro haxe da baqin tavo mai wari, ya kuma sami wasu mutane a wurinta, Muka ce: “Ya Zulqarnaini, ko dai ka azabtar (da su), ko kuma ka kyautata musu.”
قَالَ أَمَّا مَن ظَلَمَ فَسَوۡفَ نُعَذِّبُهُۥ ثُمَّ يُرَدُّ إِلَىٰ رَبِّهِۦ فَيُعَذِّبُهُۥ عَذَابٗا نُّكۡرٗا
(Zulqarnaini) ya ce: “Amma wanda ya yi zalunci to za mu azabtar da shi, sannan a mayar da shi zuwa ga Ubangijinsa (shi ma) Ya yi masa mummunar azaba
وَأَمَّا مَنۡ ءَامَنَ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا فَلَهُۥ جَزَآءً ٱلۡحُسۡنَىٰۖ وَسَنَقُولُ لَهُۥ مِنۡ أَمۡرِنَا يُسۡرٗا
“Amma kuma wanda ya yi imani ya kuma yi aiki nagari, to yana da mafi kyan sakamako, kuma za mu faxa masa tattausar (magana) game da al’amarinmu.”
ثُمَّ أَتۡبَعَ سَبَبًا
Sannan ya kama hanya
حَتَّىٰٓ إِذَا بَلَغَ مَطۡلِعَ ٱلشَّمۡسِ وَجَدَهَا تَطۡلُعُ عَلَىٰ قَوۡمٖ لَّمۡ نَجۡعَل لَّهُم مِّن دُونِهَا سِتۡرٗا
Har dai lokacin da ya isa mahudar rana, ya same ta tana vullowa ne a kan wasu mutane da ba Mu sanya musu wata kariya ba daga gare ta[1]
1- Watau ba su da gidaje, kuma a inda suke babu bishiyoyi babu duwatsu da za su fake a inuwoyinsu, kuma qasar ba ta xaukan gine-gine.
كَذَٰلِكَۖ وَقَدۡ أَحَطۡنَا بِمَا لَدَيۡهِ خُبۡرٗا
Kamar haka (ya yi hukunci watau irin yadda ya yi a mafaxar rana), haqiqa kuma Mun kewaye da sanin (duk) abin da ke tare da shi (Zulqarnaini)
ثُمَّ أَتۡبَعَ سَبَبًا
Sannan ya kama hanya
حَتَّىٰٓ إِذَا بَلَغَ بَيۡنَ ٱلسَّدَّيۡنِ وَجَدَ مِن دُونِهِمَا قَوۡمٗا لَّا يَكَادُونَ يَفۡقَهُونَ قَوۡلٗا
Har ya iso (wani gari) tsakanin duwatsu biyu, ya kuma sami wasu mutane a gabansu (watau duwatsun) waxanda ba sa fahimtar wata magana
قَالُواْ يَٰذَا ٱلۡقَرۡنَيۡنِ إِنَّ يَأۡجُوجَ وَمَأۡجُوجَ مُفۡسِدُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَهَلۡ نَجۡعَلُ لَكَ خَرۡجًا عَلَىٰٓ أَن تَجۡعَلَ بَيۡنَنَا وَبَيۡنَهُمۡ سَدّٗا
Suka ce: “Ya Zulqarnaini, lalle Yajuju da Majuju (mutane ne) masu varna a bayan qasa, to ko za mu iya biyan ka wata jinga don ka sanya wani shamaki tsakaninmu da su?”
قَالَ مَا مَكَّنِّي فِيهِ رَبِّي خَيۡرٞ فَأَعِينُونِي بِقُوَّةٍ أَجۡعَلۡ بَيۡنَكُمۡ وَبَيۡنَهُمۡ رَدۡمًا
Ya ce, “Abin da Ubangijina Ya ba ni ya fi (abin da za ku ba ni), sai dai ku taimake ni da qarfi (don) in sanya shamaki tsakaninku da su
ءَاتُونِي زُبَرَ ٱلۡحَدِيدِۖ حَتَّىٰٓ إِذَا سَاوَىٰ بَيۡنَ ٱلصَّدَفَيۡنِ قَالَ ٱنفُخُواْۖ حَتَّىٰٓ إِذَا جَعَلَهُۥ نَارٗا قَالَ ءَاتُونِيٓ أُفۡرِغۡ عَلَيۡهِ قِطۡرٗا
“Ku kawo mini guntattakin qarafa”; har dai lokacin da ya daidaita (ginin da) duwatsun nan biyu, sai ya ce: “Ku hura wuta da zugazuginku”; har dai yayin da ya mai da shi wuta, sai ya ce: “Ku kawo min narkakkiyar dalma in zuba a kansu.”
فَمَا ٱسۡطَٰعُوٓاْ أَن يَظۡهَرُوهُ وَمَا ٱسۡتَطَٰعُواْ لَهُۥ نَقۡبٗا
Saboda haka ba su samu ikon su haura shi ba, ba su kuma sami ikon huda shi ba
قَالَ هَٰذَا رَحۡمَةٞ مِّن رَّبِّيۖ فَإِذَا جَآءَ وَعۡدُ رَبِّي جَعَلَهُۥ دَكَّآءَۖ وَكَانَ وَعۡدُ رَبِّي حَقّٗا
Ya ce, “Wannan rahama ce daga Ubangijina; sai dai idan alqawarin Ubangijina ya zo, (watau tashin alqiyama) to zai mai da shi daga-daga; alqawarin Ubangijina kuwa ya tabbata gaskiya ne.”
۞وَتَرَكۡنَا بَعۡضَهُمۡ يَوۡمَئِذٖ يَمُوجُ فِي بَعۡضٖۖ وَنُفِخَ فِي ٱلصُّورِ فَجَمَعۡنَٰهُمۡ جَمۡعٗا
Kuma Muka bar sashinsu (mutane) a wannan rana yana cakuxa da wani sashi[1]; aka kuma busa qaho, sannan Muka tattara su gaba xaya
1- Wannan zai iya xaukar ma’anar cewa, ranar da Yajuju da Majuju za su fito da yawa suna gauraya da mutane suna masu varna. A wata ma’anar kuma ana nufin ranar alqiyama da mutane da aljannu za su gauraya da juna wuri xaya.
وَعَرَضۡنَا جَهَنَّمَ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡكَٰفِرِينَ عَرۡضًا
Muka kuma bijiro da (wutar) Jahannama a wannan ranar ga kafirai (su gan ta) quru-quru
ٱلَّذِينَ كَانَتۡ أَعۡيُنُهُمۡ فِي غِطَآءٍ عَن ذِكۡرِي وَكَانُواْ لَا يَسۡتَطِيعُونَ سَمۡعًا
(Su ne) waxanda idanuwansu suka makance daga ambatona, suka kuma kasance ba sa iya jin (gaskiya)
أَفَحَسِبَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَن يَتَّخِذُواْ عِبَادِي مِن دُونِيٓ أَوۡلِيَآءَۚ إِنَّآ أَعۡتَدۡنَا جَهَنَّمَ لِلۡكَٰفِرِينَ نُزُلٗا
Yanzu waxanda suka kafirta suna tsammanin su riqi wasu bayina ababen bauta ba Ni ba? Lalle Mun tanadi Jahannama ta zama masauki ga kafirai
قُلۡ هَلۡ نُنَبِّئُكُم بِٱلۡأَخۡسَرِينَ أَعۡمَٰلًا
Ka ce (da su): “Ba na ba ku labarin waxanda suka fi asarar ayyukansu ba?
ٱلَّذِينَ ضَلَّ سَعۡيُهُمۡ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَهُمۡ يَحۡسَبُونَ أَنَّهُمۡ يُحۡسِنُونَ صُنۡعًا
“(Su ne) waxanda aikinsu ya vace a rayuwarsu ta duniya alhali kuwa su suna tsammanin suna kyautata aiki ne.”